Nigeria: Buhari ya nemi a kawo karshen rikicin Plateau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi sojojin kasar akan su tashi tsaye wajan daukar matakan dakile tashen tashe- hankula da suka dawo a jihar Flato.

Shugaba Buhari ya nuna alhini da kuma takaici kan asarar rayuka na baya-baya nan na mutum 20 a jihar ta Filato, a abin da ya kira harin ramuwar gayya ta Fulani makiyaya.

A kalla mutum 35 aka kashe yayin da aka jikkata wasu da dama a hare-haren da aka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Bassa a jihar Filato.

Wasu 'yan bindiga ne dai suka kai hare-haren a ranakun Lahadi da kuma Litinin, inda suka lalata gidaje da dama.

Rahotanni sun ce hukumomi sun sanya dokar takaita zirga-zirga a yankin inda aka tura karin jami'an tsaro.

Hukumomin Flato sun ce nan ba da jimawa ba gwamnan jihar zai yi wa al'ummar jihar bayani.

Mutane da dama ne suka mutu a 'yan shekarun baya a tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini a jihar.

Sai dai a 'yan watannin baya, an samu kwanciyar hankali a jihar bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da bangarorin da ke rikici da juna.