Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin ƙabilanci ya ɓarke a jihar Adamawa
Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da ɓarkewar rikicin ƙabilanci a wani kauye na jihar.
Rikicin ya barke ne tsakanin Hausawa mazauna garin Tinno da kabilar Chobo da ke karamar hukumar Lamorde.
Ana fargabar cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a cikin rikicin.
Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa wani karamin saɓani aka samu bayan wani matashi ya kaɗe wani ɗan ƙabilar Chobo.
Daga bisani `yan uwansa suka far ma mai babur ɗin, inda shi ma wasu suka yi kokarin kare shi, kuma wasa-wasa rikici ya girma.
Wani mazaunin garin, Sulaiman Bello mazaunin, ya shaida wa "Muna cikin mawuyacin hali saboda yanzu an yi mana ƙawanya ko ta ina kana jin ƙarar bindigogi kawai."
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Sulaiman Yahaya Nugroje, ya tabbatar wa BBC da aukuwar rikicin, ko da yake ya ce yanzu ne suke tattara bayanan kan ainihin abi da ya faru.
Jihar ta Adamawa dai ta sha fama da rikicin kabilanci a baya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.