Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muƙarraban gwamnatin Najeriya biyar da aka zarga da takardun bogi
A Najeriya ana ci gaba da mahawara dangane da binciken da jaridar Premium Times ta yi inda ta gano ministan kimiyya da fasaha na ƙasar, Mista Uche Nnaji da mallakar "takardun boge".
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun wani muƙarrabin gwamnati mai ci da mallakar takardun na bogi ba, inda daga bisani suke sauka daga muƙaman nasu sakamakon matsin lamba.
BBC ta yi nazari kan wasu manyan muƙarraban gwamnati guda biyar da aka zarga da mallakar takardun bogi da kuma ya kai ga barin su kujerun nasu.
Uche Nnaji
Mista Uche Nnaji shi ne ministan kimiyya da fasaha na gwamnatin Shugaban Bola Ahmed Tinubu.
A ranar 16 ga watan Agustan 2023 ne shugaba Bola Tinubu ya naɗa mista Uche Nnaji a matsayin minista.
An haifi Uche Nnaji Nwakaibie a garin Akpugo da ke ƙaramar hukumar Nkanu West a jihar Enugu.
Binciken da jaridar ta Premium times ta wallafa ya ce an gano cewa ministan ya miƙa takardun bogin ga majalisar dattawan ƙasar domin tattance shi, bayan shugaban Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunansa cikin waɗanda yake so ya bai wa muƙamin minista a shekarar 2023.
Jaridar ta yi ikirarin cewa takardun shaidar kammala karatun digiri da na bautar ƙasa na Mr Nnaji duka na boge ne.
Inda ta ƙara da cewa masu suka sun ce ministan bai kammala karatun digirin ba, haka kuma takardar shaidar bautar ƙasar da ya miƙa wa ofishin sakataran gwamnatin tarayya da hukumar tattara bayanan sirri ta DSS da kuma majalisar dattawan na bogi ne.
Kuma binciken da ta yi ya tabbatar mata da cewa takardun na boge ne.
A cewar jaridar a ranar Lahadi ministan ya amince cewa jami'ar Nsukka da ke Najeriyar ba ta taɓa ba shi shaidar kammala karatu na digiri ba.
Batun zargin takardun bogin na cikin manyan batutuwan da suka fi jan hankali a kafafen sada zumunta na Najeriya a ranar Litinin.
Kemi Adeosun
An sami Kemi Adeosun wadda ita ce ministar kuɗi ta Najeriya lokacin Muhammadu Buhari daga watan Nuwamban 2015 zuwa Satumban 2018.
Ministar ta kuɗi ta ajiye muƙaminta ne bayan matsain lamba kan gwamnatin Buhari da ta cire ta bisa zargin mallakar takardar kammala hidimar ƙasa ta bogi.
Jaridar Premium Times ta ce ta bankado yadda Kemi Adeosun ta ki halartar aikin hidimar kasa bayan kammala karatunta a Birtaniya 1989, amma daga bisani ta mallaki takardar "jabu" da ke nuna cewa an dauke mata yin hidimar.
Dan jaridar Premium Times Abdul'aziz Abdul'aziz ne ya bankado labarin, inda ya bi kwakwaf domin gano inganci ko sahihancin takardun da ministar ta gabatar da ke nuna cewa an dauke mata halartar aikin hidimar kasar.
Bayan binciken ne kuma, wanda ya dauki lokaci ana gudanarwa, jaridar ta ce ta gano cewa shaidar da Misis Adeosun ta gabatar ta boge ce.
Bayan kammala karatunta a shekarar 1989, tana da shekara 22 da haihuwa a Polytechnic of East London.
Ya kamata a ce Misis Adeosun ta zo Najeriya domin yin aikin hidimar kasa, amma sai ta ki yin hakan, inda ta fara aiki a Birtaniya.
Ta koma Najeriya a shekarar 2002, amma duk da haka ba ta je ta halacci NYSC ba, sai kawai ta ci gaba da aiki a wani kamfani mai zaman kansa mai suna, Chapel Hill Denham, kamar yadda Premium Times ta bayyana.
Kwatsam a shekarar 2009 sai ta yanke shawarar karbar takardar shaidar boge wacce ta nuna cewa an amince ka da ta halacci aikin hidimar kasar, a cewar Premium Times.
Tsarin hukumar NYSC ya nuna cewa ba a bai wa duk mutumin da ya kammala makaranta yana/tana kasa da shekara 30 (kamar Misis Adeosun) damar kin halattar hidimar kasa.
Wasu jami'ai a hukumar da ba su amince a bayyana sunansu ba, sun shaida wa jaridar cewa shaidar da ta bayar ta boge ce, domin daraktan da ya sanya wa takardar hannu ya mutu watanni takwas kafin a bayar da takardar ta ta.
Imam Salisu Buhari 1999-2000
Tsohon shugaban majalisar wakilai ta Najeriya, Imam Salisu Buhari ya fuskanci irin wannan zargi na bogi, inda aka zarge shi da mallakar takardun bogi da suka jiɓanci shekarunsa da kuma na karatunsa.
Ya yi iƙrarin cewa shekarunsa 36 ya zuwa 1999, alhali kuma shekarunsa 29 ne sakamakon haihuwarsa da aka yi a 1970.
Kudin tsarin mulkin Najeriya dai ya keɓe shekaru 30 ga duk mai son zama ɗan majalisa.
Bugu da ƙari, tsohon shugaban majalsiar ta wakilai ya yi iƙrarin halartar jami'ar Toronta da ke Canada inda ya kammala da digiri a fannin gudanar da kasuwanci, sai dai kuma jami'ar ta musanta cewa ya taɓa zama ɗalibinta.
Har wayau, Salisu Buhari ya kuma ƙirƙiri takardun bogi domin samun gurbi a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda jami'ar ta kore shi ba tare da samun damar yi wa ƙasa hidima ba.
Imam Salihu Buhari ya sauka daga muƙaminsa a shekarar 2000 bayan amincewa da ya yi da zarge-zargen, inda cikin hawaye ya nemi afuwar ƴan Najeriya.
Ku san za a iya cewa Imam Salisu Buhari shi ne mutum na farko da aka fara ganowa da mallakar takardun bogi tun bayan komawar Najeriya kan turbar dimokraɗiyya a 1999.
Evan (s) Enwerem
Sanata Evan(s) Enwerem shi ne shugaban Mjalaisar Dattawan Najeriya na farko bayan da ƙasar ta koma turbar dimokraɗiyya.
Sai dai sakamkon badaƙalar mallakar takardun bogi, sanata Enwerem bai daɗe ba inda ya yi jagorancin majalisar tsakanin ranar 3 ga watan Yuni 1999 zuwa ranar 18 ga watan Nuwamban 1999, sai dai kuma ya ci gaba da kasancewa a matsayin sanata har zuwa 2003.
Abokan aikinsa sanatoci ne suka zargi sanata Evans da amfani da sunan bogi da takardun karatunsa.
Zargin kan sunansa shi ne ko Evan ko kuma Evans ne sunansa na haƙiƙa. Sanata Chuba Okadibo wanda ya jagoranci binciken shi ne mutumin da ya gaji sanatan.
Sanata Evan (s) Enwerem ya rasu a 2007.
Christian Aba
A watan Maris ɗin shekarar 2017 ne kotun ƙoli ta kori ɗan majalisar wakilai daga jihar Benue, Christian Abah inda ta nemi hukumar zaɓe ta maye gurbinsa da Hasan Saleh wanda shi ne me biye da shi a yawan ƙuri'a.
An zargi ɗan majalisar, mai wakiltar mazaɓar Ado/Okpokuw/Oggbadigbo da laifin mallakar takardun karatu na bogi waɗanda ya miƙa wa hukumar zaɓe ta INEC.
Kotun ƙolin ta tabbatar da cewa ɗanmajalisar ya mallaki takardun bogi na ƙaramar difloma da ya ce kwalejin fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Mubin jihar Adamawa ta ba shi a 1985.