Vinicius zai bar Real Madrid,Liverpool na zawarcin Semenyo

Asalin hoton, Reuters
Dan wasan Brazil Vinicius Junior, mai shekara 25, ya fada wa Real Madrid cewa ba shi da aniyar sabunta kwantaraginsa da zai kare a bazarar 2027 saboda alakarsa da kocin kungiyar, Xabi Alonso ta yi tsami.(Athletic )
Liverpool da Manchester United da wasu kungiyoyin Firimiya na bibiyar halin da Vinicius ke ciki a Real Madrid. (Mirror)
Liverpool na zawarcin dan wasan Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 25, kuma tana sane da fam miliyan 65 da za a biya domin sakinsa. (Florian Plettenberg)
Manchester United da Chelsea sun nuna sha'awar daukar dan wasan RB Leipzig da Jamus Assan Ouedraogo, mai shekara 19. (Sky Sports Germany )
Marseille na son su tattauna da Brighton don daukar dan wasan Denmark Matt O'Riley, mai shekara 25, a matsayin dan wasan dindin a watan Janairu. (Sky Sports),
AC Milan na zawarcin dan wasan Crystal Palace da Faransa Jean-Philippe Mateta, mai shekara 28. (Teamtalk),
Ana sa ran kungiyoyin gasar Firimiya za su yi kokarin sayen dan wasan Atletico Madrid da Ingila Conor Gallagher a watan Janairu, muddin kulob din na Sifaniya ya amince ya sayar da tsohon dan wasan na Chelsea mai shekara 25 ko ya ba da shi aro (Sky Sports),
Paris St-Germain ta bi sahun Real Madrid wajen neman dan wasan Bayern Munich da Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 27, (Sky Sports Germany ), external














