Man Utd za ta sallami Fernandes, Barcelona na son ɗaukar Harry Kane da Julian Alvarez

.

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Mai horar da ƴan wasan Manchester United Ruben Amorim, ya ce ya na shirye-shiryen ƙyale kyftin ɗin ƙungiyar Bruno Fernandes, a kakar wasa mai zuwa, don samun damar ɗaukar Adam Wharton, da Elliot Anderson, daga Crystal Palace da Nottingham Forest, da ɗan wasan Kamaru Carlos Baleba daga Brighton. (Teamtalk)

Manchester United za ta barCasemiro, da Jadon Sancho, su tafi a kakar siyen ƴan wasa, don samun rarar fam miliyan 31. (Sun)

Barcelona na harin ɗan wasan Bayern Munich Harry Kane, da ɗan wasan Argentina Julian Alvarez a kakar siyen yan wasan da ake daba da buɗewa. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Real Madrid na son ɗaukar ɗan wasan Stuttgart Angelo Stiller, mai shekaru 24, da ke son komawa Bernabeu. (Fichajes - in Spanish)

Bayern Munich na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Vasco da Gama Rayan da takwaransa Souza, da ke kwaɗayin taka leda a Santos. (Bild - in German)

Manchester City na bibiyar ɗan wasan Feyenoord Givairo Read, mai shekaru 19, a yunƙurinta na samun ɗan wasan da zai tsare mata baya ta gefe. Tuni Bayern Munich tagana da ɗan wasan. (Fabrizio Romano)

Tottenham na shirye shiryen siyen ɗan wasan gaban Villarreal Georges Mikautadzekan Fam miliyan 44. (Fichajes - in Spanish)

Everton na harin ɗan wasan Celtic da Japan Daizen Maeda, mai shekaru 28, a watan Janeru. (Football Insider)

Atletico Madrid ba zata siyarwa da Chelsea da Bayern Munich Pablo Barrios, ba sai dai in za su siye shi kan Fam miliyan 88. (Fichajes - in Spanish)

wakilan Arsenal sun gana da Jorge Mendes don cinikin siyen ɗan wasan Juventus Kenan Yildiz, mai shekaru 0. (Caught Offside)

Anan sa ran cewar Everton na shirye shiryen ɗaukar dan wasan Bologna ta Argentine Santiago Castro, mai shekaru 21. (Teamtalk)

Ɗan wasan baya na Brighton Olivier Boscagli, mai shekaru 28, na iya komawa Fenerbahce don ci gaba da taka leda, a mastayin aro a watan Janeru bayan kokawar samun damar buga wasanni tun bayan komawarsa ƙungiyar a kakar wasannin. (Fichajes - in Spanish)