Chelsea da Arsenal na harin Murillo, Manchester United na son tsawaita kwantragin Casemiro

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Mai horar da ƴan wasan Chelsea Enzo Maresca na son ɗauko ɗan wasan Nottingham Forest Murill, don ƙara ƙarfin tsaron bayan ƙungiyar, sai dai ɗan ƙasar Brazil ɗin na janhankalin Arsenal da Barcelona. (Caught Offside)

Manchester United na son Casemiro da ya ci gaba da zama a ƙungiyar, ta hanyar sabuntakwantaraginsa, sai dai suna son ya amince da ragin albashin da za su yi masa a matsayin sharaɗin sabunta masa kwantaragin. (Fabrizio Romano)

Manchester United ka iya amincewa da miƙawa Antoine Semenyo buƙatarsa na son riga mai lamba 24, a wani yunƙuri na jan a'ayinsa na dawowa ƙungiyar daga Bournemouth ya koma taka leda a Old Trafford a Janeru. (Manchester Evening News)

Liverpool ta yi wa Ibrahim Konate tayin sabunta masa kwantaraginsa, sai dai ɗan ƙasar Faransan bai kai ga cewa komai ba , duk kuwa da harinsa da Real Madarid ke yi masa. (Caught Offside)

A ƙarshen kakar nan ne kwantaragin Ɗan wasan Bayer Munich Dayot Upamecano, za ta ƙare, yayin da Real Madrid da Inter Milan, da Liverpool, ɗan waan ya musanta hasashen da ake na cewar zai iya komawa Cheksea a Watan Janeru. (Metro)

ɗan wasan Italy Federico Chiesa na duba ƙungiyar da ya kamata ya koma idan ya bar Liverpool a watan Janeru, yayin da Inter Milan, da Napoli, da AS Roma da Ac Milan ke kokawar daukarsa. (Fichajes - in Spanish)

Liverpool ta gaza ɗaukar kyftin ɗin Crystal Palace Marc Guehi mai shekaru 25, inda ya jefa shakku a zuciyar ɗan wasan bayan Ingila, inda yanzu ya ke son tsayawa zuwa ƙarshen kakar wasanni, don sanin makomar sa. (Alan Nixon on Patreon)

Ɗan wasan Newcastle William Osula mai shekaru 22, na son komawa Eintracht Frankfurt a Janeru , bayan kamala gasa Premier League, inda ƙungiyar ta yi nasarara bayar da shi a matsayin ɗan wasan aro ga kungiyar ta Jamus. (Fussball Transfers - in German)

Ɗan wasan Chelsea da Portugal Pedro Neto mai shekaru 25, zai iya komawa Barcelona da taka leda sakmakon yadda Daraktan wasannin Deco ya kaance abin koyinsa. (Fichajes - in Spanish)

Fabian Schar zai iya barin Newcastle idan kwantaraginsa ta ƙare a kakar wasa mai zuwa, sakamakon sha'awar komawa taka leda a ƙungiyoyin Jamus da ya ke da shi.(Football Insider)

Liverpool na shirin siyen dan Portugal da ke taka leda a Paris St-Germain Joao Neveskan fam miliyan 140. (Fichajes - in Spanish)

Brentford za ta bar mai tsaron ragartaMatthew Cox barin ƙungiyar, a matsayin aro a kakar siyen ƴan wasa a watan Janeru mai zuwa. (Football Insider)