Ƴan kasuwar Arewa na neman diyyar sama da Triliyan ɗaya kan ɗauke wutar lantarki

Asalin hoton, Google
Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan sana'o'in daga arewacin Najeriya ke ci gaba da lissafa irin griman asarar milyoyin nerorin da suka tafka sakamakon katsewar lantarki na kusan makwanni biyu da aka samu a wasu jihohin yankin, wasu yan kasuwa a yankin sun ce sun fara tattaro kawunansu da ɗai-ɗaikun jama'a don neman diyyar abun da suka yi asarar daga ɓanagaren gwamnatin tarayya.
Gidauniyar Jino mai rajin kare hakki da fafutukar tabbatar da adalci da shugabanci na gari a Najeriya, ta ce ta fara tattara waɗan nan bayanai na yawan asarar da aka tafka a jihohin da ke yankin 19, don ganin ganin an biya su diyyar wajen rage wa mutane raɗaɗin asarar da suka tafka, ganin yadda wasunsu sun durkushe har abada idan ba a kai masu dauki ba, saboda karyewar da jarinsu ya yi baki ɗaya.
Shugaban gidauniyar, Imrana Jino ya shaida wa BBC cewar, bai kamata a tsaya kan matakin dawo da wutar lantarkin kaɗai ba, kamata ya yi a haɗa da batun biyan diyyar, ko bai wa mutane wani tallafi ko ihisani don ganin sun sake farfaɗo da tattalin arzikinsu, da jarinsu.
Har Ila yau Imrana Jino ya ce ‘duk wanda ya ke magana kan wannan dauke wutar ana magana ne kan dawo da wutar, ba a magana kan irin ɓarnar da hakan ya haifar wa ga jihohin, da abun da ya kamata a yi bayan ɓarnar ko wannan asarar da aka samu ba, shi ya sa muke kiran duk wadan yake da kamfani, ko ɗan kasuwa, kai hatta kayan cefane, ko kayan lantarki da daukewar wutar ta shafa, da su futo su yi bayani, don ganin an biya su diyya' in ji shi.
"Rashin wannan wutar ya gurgunta harkokin lafiya, tare kananan sana'oi da mata ke yi da suke amfani da lantarki waje siyar da kayan sanyi, ɓanagren noma ma an sami wannan matsala, musamman masu kiwon kifi, da masu siyar da kajin da ake ajiye su a dakin sanyi, wanda da dama daga cikinsu idan har ba a ba su tallafi ba, to ba lallai su sake dawowa su ci gaba da kasuwancinsu ba" in ji Imrana Jino.
Shugaban Gidauniyar ta Jino ya ce kawo yanzu ƙiyasin asarar da aka tafka ya kai Naira Triliyan ɗaya da miliyan ɗari biyar, a ɗaukacin fadin jihohin arewacin ƙasar da katsewar lantarkin ta shafa.
Sannan ya ce suna tattara bayanai, tare da tuntubar lauyoyi, da abokan su ƴan kasuwa, don ganin ta inda aka fara neman diyyar.
Gidauniyar Jino ta ce za ta yi dukkan mai wiwuwa daomin ganin wannan fata na ta na ganin an biya diyya ya tabbata.
Katsewar lantarki a yankin na arewa na zuwa ne ƴan kwanaki bayan ɗaukacin ƙasar ta yi fama da katsewar wutar har sau uku a cikin kwana biyu sakamakon lalacewar babban layin wutar na ƙasa wato national grid.
Fatan ƴan arewacin Najeriyar dai a yanzu bai wuce ganin gwamnonin yankin sun ƙaddamar da abubuwan da suka cimma a lokacin taron nasu na Kaduna, kasancewar an yin ruwa ƙasa na tsotsewa - babban fatan dai shi ne wannan katsewar wutar lantarki ta zama wani darasi na tunkarar ƙalaubalen da yankin ke fuskanta.











