Yadda rashin lantarki ya durƙusar da ƴan kasuwa a arewacin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya an shiga kwana na tara da yankin arewacin ƙasar ke fama da matsalar rashin wuta.
Jihohi da dama ne ke fama da matsalar, wadda ta shafi ma’aikatun gwamnati da masana’antu da kuma kasuwancin ɗaiɗaikun mutane.
Kwana taran da aka yi babu wuta a wadannan jihohi, a wurin wasu yankunan shi ne karon farko da suka ga haka a tarihi.
Wasu na cewa duk da dai kashi 80 na yankin arewacin Najeriya baya iya samun wutar awa 10 ciklin 24, amma yanzu da babu wutar baki daya sun gano cewa da babu gwara ba dadi.
Sana'o'i da dama sun dogara kan wutar lantarki domin tafiyar da su, duk kuwa da kankantarta.
Wasu masu sana'ar da ke da ruwa da lantarki, sun ce sun yanke kauna da sana'ar har sai abin da hali ya yi.
Malam Abubakar Auwal me sayar da nama kwanar dillalai a jihar Kano na daga cikinsu ya kuma ce rashinn lantarki ya jefa shi cikin halin matsi da yake ji kamar ya bar gari kafin zuwa lokacin da za a samu wutar.
"Ire-iren mu muna da yawa, waɗanda sun cinye jarinsu har sun shiga cikin dukiyar al'umma ana ta rigima da su, wanda da ba haka muke ba, muna sana'ar mu ne cikin kwanciyar hankali."
Malam Abubakar ya ce rashin lantarki ya sanya naman shi yana lalacewa har yana rasa yadda zai da shi, "Idan an saya na yanka ana dawo mani da shi saboda ya fara bugawa sakamakon wannan rashin wutar."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masrura Idris Abubkar daga jihar Platuea mai sana'ar girke-girke ce da take koyar da kuma girki ta ce ta yi asara da dama saboda wannan lokacin ne da suke ciniki saboda ana yawan bukukuwa.
"Muna sayen abubuwa da yawa mu saka a fridge saboda duk lokacin da kwastoma ya zo ya kasance muna da komai a ƙasa, kamar irinsu nama da kifi da kayan miya, ba mu taɓa tunanin za a samu wannan matsalar rashin wuta ta tsawon lokaci ba, haka muna ji muna gani kayanmu duk suka lalace."
Wata matashiyar dake sana'ar kayan gyaran jiki da na mata a jihar Katsina itama abin ya shafeta, ina ta ce sun kashe kudi masu yawa sun hada kaya gashi babu wuta kuma man fetur ay yi tsadar da ba za su iya saye ba.
"Dole da hannuna nake neman mutane ina basu kyauta saboda kada a yi asarar su gaba ɗaya, yanzu dole mu haƙura da sana'ar saboda asara ce za ai ta yi."
Masu sana'a da dama a arewacin Najeriya da ke da alaka da wutar lantarki na fuskantar hali gaba kura baya siyaki kamar dai wannan matashiya, ba za su iya ci gaba da sayan man fetur ba saboda tsadarsa, sannan kuma tsammanin wutar lantarkin ya zama kamar jiran gawon shanu a wurinsu.
Kamfanin raba wutar lantarki na Najeriya ya ce yana iya ƙoƙarinsa domin gyara matsalar lantarkin a yankin.
Kungiyar tuntubar juna ta dattawan arewacin Najeriya, ACF ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ɓangaren wutar lantarki a daidai lokacin da yankin arewacin ƙasar ke ci gaba da kasancewa cikin duhu sakamakon rashin wuta.
Ƙungiyar gwamnomin arewacin Najeriyar ita ma ta yi kira ga gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kawo ƙarshen matsalar.











