Dalilan da ke janyo rashin tsayayyiyar wutar lantarki a Najeriya

..

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist

Wata matsala da ƴan Najeriya ke fama da ita tsawon shekaru ita ce rashin tsayayyiyar wutar lantarki abin da ke shafar harkokin yau da kullum da kuma na kasuwanci.

Sai dai matsalar ta yi muni a baya-bayan nan inda ake samun yawan ɗaukewar lantarki a faɗin ƙasar ko ma rashin wutar na tsawon kwanaki a wasu jihohin duk da kasancewar ƙasar babbar mai samar da iskar gas da man fetur ce.

Lamarin kuma ya zo a daidai lokacin da ake fuskantar yanayi na tsananin zafi sannan kuma al'ummar musulmi a ƙasar ke azumin watan Ramadan - wani lokaci da mutane ke buƙatar wuta sosai domin samun kayan sanyaya maƙoshinsu a lokacin bude baki.

Rashin wutar kan janyo lalacewar abinci cikin sauri musamman wanda aka ajiye a firinji, sai kuma yadda matsalar ta janyo durƙushewar harkokin kasuwanci.

Hukumomi dai sun sha cewa suna aiki domin magance matsalar da suke alaƙantawa ga matsalar ƙarancin iskar gas da ke samar da kashi 80 cikin 100 na wutar da kuma ayyukan masu satar kayan wuta a cibiyoyin wuta da ke faɗin ƙasar.

A watan Nuwamban 2022, Najeriya ta iya cimma yawan karfin lantarki megawatts 4,594.6.

Matsalar ta sa mutane da dama nemarwa kansu mafita ta hanyar komawa amfani da wutar sola mai amfani da hasken rana wasu kuma suna amfani da injin janareto.

Ƴan Najeriya da dama sun bayyana rashin jin daɗinsu ga yadda matsalar wutar ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

Lamarin da ya sa wasu ƴan Najeriyar zuwa shafukansu na sada zumunta domin bayyana yadda matsalar ta kai masu maƙura inda suke caccakar hukumomi tare da neman su yi bayanin abin da ke sa ake yawan ɗauke wuta a ƙasar.

Stein wani ma'abocin shafin X da aka fi sani da Twitter a baya, inda ya wallafa cewa babu wani abu da ke tafiya daidai a Najeriya har da wutar lantarki da sadarwar intanet.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Ita ma Boss Lady a shafinta na X ta bayyana cewa "duk lokacin da Ramadan ya zagayo, sai an samu ƙarancin wutar lantarki a Najeriya."

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Kaɗan daga cikin irin ƙorafe-ƙorafen da ƴan Najeriya ke yi game da matsalar rashin wutar.

Wannan ne kuma ya sa za mu duba abin da ke janyo matsalar wutar da kuma hanyoyin da ya kamata hukumomi su bi domin daidaita al'amura tare da magance matsalar da kuma yawan wutar da ake buƙata Najeriya ta fita daga ƙangin na rashin wutar.

Najeriya ta gaza samar da isasshiyar wuta

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Injiniya Yabagi Sani, masani kan harkar makamashi ya ce matsalar rashin wuta a Najeriya ta zama abin damuwa.

Ya ce gwamnati ta saka isasshen kuɗin da ya kamata wajen inganta ɓangaren wutar lantarki.

"Halin da aka shiga da aka cire tallafin mai, gwamnati ba za ta iya fitowa ta ce an cire tallafin da ake bayar wa a ɓangaren wutar lantarki ba."

"Ke nan gwamnati ta kasa domin ba ta da kuɗin kuma rashin kuɗin ya sa abin da ke buƙata domin yin gyara a ɓangarorin samar da wutar lantarkin." in ji shi.

Masanin ya ce har yanzu Najeriya ba ta samar da rabin ƙarfin wutar da ya kamata ta rika samarwa ba, kasancewar a yanzu tana iya samar da megawatt dubu 13 kawai.

"Abin da muke buƙata da zai samar da isasshiyar wuta a Najeriya ya kai megawatt dubu 25." kamar yadda ya ce.

Injiniya Yabagi ya kuma yi magana kan abubuwan da ke kawo tangarɗa a yunƙurin inganta wutar lantarki a ƙasar.

Ya lissafo dalilai biyu da ke janyo wannan matsala - ayyukan ƴanbindiga da ke kai hare-hare kan cibiyoyin lantarki.

Sai kuma matsalar cin hanci da rashawa inda ake samun kuɗaɗen da ake warewa don inganta wuta ke zurarewa ta wannan hanya.

Yadda za a shawo kan matsalar

Injiniya Yabagi Sani ya bayyana cewa akwai hanyoyi da dama da gwamnati ya kamata ta bi domin samar da wutar lantarki mara ɗaukewa.

Ya lissafo hanyoyin kamar haka:

  • Zuba isasshen kuɗi domin yin gyaran da ake buƙata a ɓangaren lantarki
  • Ƙara yawan iskar gas da ya kamata a yi amfani da ita don samar da wuta
  • Ƙara kaimi wajen ƙara yawan megawatts ɗin da ake samarwa
  • Maganin matsalar cin hanci da rashawa da ta yi katutu

A cewarsa, matuƙar gwamnati ta warware waɗan nan matsalolin, to talaka a Najeriya zai samu sauƙin rashin wuta.

Abin da gwamnati take...

A baya-bayan nan gwamnatin Najeriya ta sa hannu kan wata yarjejeniyar gina cibiyar samar da wutar lantarki mai amfani da ruwa da hasken rana da za ta samar da wuta mai ƙarfin megawatt 20.

Shirin samar da lantarki mai ƙarfin megawatt 300 wani ɓangare ne na ƙudurin Najeriya na komawa ga amfani da makamashi mara gurɓata muhalli.

Za a gina cibiyar a Shiroro da ke jihar Neja a tsakiyar Najeriya kuma zai zama shirin haɗin gwiwa tsakanin kamfanin NSP mai zaman kansa da hukumar NSIA mai bibiyar harkokin gwamnatin a Najeriya.

"Wannan wani shiri ne na farko na samar da lantarki mai amfani da hasken rana da ruwa," in ji mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Ya ƙara da cewa shirin zai taimaka wa Najeriya ta faɗaɗa hanyoyin da take amfani da makamashi.