Man Utd na ƙyalla ido kan Tel da Nkunku, AC Milan da Aston Villa na rububin Joao Felix

Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na son ɗaukan ɗanwasan gaba na Bayern Munich da Faransa Mathys Tel, 19. Ko kuma ɗanwasan Chelsea da Faransa Christopher Nkunku, 27 a ranar cikar wa'adin kasuwar musayar ƴanwasa. (ESPN).

Tel na son koma wa Manchester United amma ana kan tattaunawa da Bayern, inda kuma ƙungiyar ta Bundesliga ta zaƙu a saka batun wajibcin sayensa ko kuma sauya ƙungiya na dindindin. (Sky Germany).

Arsenal na dako a bayan fage bayan da aka yi fatali da tayin da United ta yi sau biyu kan Tel a ranar Lahadi. (Mail).

Tottenham ta cimma matsaya da Chelsea kan aron ɗanwasan bayanta Axel Disasi, 26 amma ɗanwasan ɗan asalin Faransa yana son zuwa Aston Villa. (Fabrizio Romano).

Za a gwada lafiyar ɗanwasan Chelsea da Ingila Ben Chilwell, 28, a ƙungiyar ƙwlalon ƙafa ta Crystal Palace gabanin ya koma ƙungiyar kan aro a ranar ƙarshe ta kasuwar musayar ƴanwasa. (Telegraph - subscription required).

Newcastle za ta bai wa ɗanwasan Ingila Lloyd Kelly, 26 damar koma wa Juventus a wata yarjejeniya da za ta zama ta dindindin kan kuɗi fam miliyan 20 a bazara. (Mail).

Joao Felix yana sa ran ficewa daga Chelsea a ranar ƙarshe ta kasuwar musayar ƴanwasa inda AC Milan da Aston Villa duka suka bayyana sha'awarsu ta sayen ɗanwasan mai shekara 25 ɗan asalin Portugal. (Sky Germany).

Manchester United na rige-rigen ɗaukan ɗanwasan Ipswich da Ingila Liam Delap, 21, wanda Tottenham ke zawarcin sa. (Express).

Ajax ba za ta ƙyale ɗanwasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson, 34, ya koma Monaco ba a wannan kasuwar musayar ƴanwasan. (Mail).

Sunderland ta yi fatali da tayin fam miliyan takwas da Brighton ta yi kan matashin ɗanwasa Tommy Watson mai shekara 18. (Guardian).

Everton na ƙoƙarin ɗaukan ɗanwasan Rennes da Faransa Adrien Truffert, 23. (Mail).

Kocin Crystal Palace Oliver Glasner na son sayen ɗanwasan AC Milan da Serbia Strahinja Pavlovic, 23 kan fam miliyan 25. (Sun).

Ɗanwasan Arsenal da Italiya Jorginho, 33 na dab da ƙulla yarjejeniya da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Flamengo a Brazil don ya koma taka masu leda a bazara. (Sky Italy, via Sky Sports).

Ƙoƙarin Napoli na ɗauko ɗanwasan Al-Ahli da Faransa Allan Saint-Maximin, 27, da yanzu yake zaman aro a Fenerbahce - na cikin haɗari. (Corriere dello Sport in Italian).

Spurs na duba yiwuwar ɗaukan ɗanwasan Lorient Eli Junior Kroupi, 18, wanda Chelsea da West Ham su ma suke zawarcinsa. (Football Insider).