Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta ragargaji Man City a Premier League
Arsenal ta casa Manchester City da ci 5-1 a wasan mako na 24 a Premier League da suka kara ranar Lahadi a Emirates.
Minti biyu da take leda Gunners ta zura ƙwallo a raga ta hannun Martin Odegaard, haka suka je hutu Arsenal na cin 1-0.
Bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne City ta farke ta hannun Erling Haaland, sai dai kasa da minti biyu tsakani Gunners ta farke ta hannun Thomas Party.
Daga nan Myles Lewis-Skelly ya ƙara na uku a ragar City - mai shekara 18 da kwana 129 ya zama matashin da ya ci mai riƙe da kofi a Premier League a tarihi.
Mai riƙe da bajintar shi ne Wayne Rooney mai shekara 17 da kwana 150 daga Everton da ya zura ƙwallo a ragar Arsenal cikin Maris ɗin 2003.
Arsenal ta zura ƙwallo na huɗu ta hannun Kai Havertz, daga nan Ethan Nwaneri ya ci na biyar - hakan ya sa ta samu maki ukun da take buƙata.
Wannan shi ne karo na huɗu da aka zura ƙwallo huɗu ko fiye da haka a Manchester City a kakar nan - karon farko a tarihin Pep Guardiola a aikin horar da tamaula.
Arsenal ta yi wasa na 14 ba tare da rashin nasara ba a karon farko karkashin Mikel Arteta, kwazo mafi ƙyau tun bayan da ya fara horar da Gunners.
Sai dai ƙungiyar ta taɓa yin wannan bajintar karkashin Unai Emery daga Agusta zuwa Disambar 2018, lokacin da ya horar da Arsenal.
Da wannan sakamakon, Arsenal ta ci gaba da zama ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki shida tsakani da Liverpool mai ƙwantan wasa da Everton.
Ita kuma City mai maki 41 tana ta huɗun teburi da maki iri ɗaya da na Newcastle United ta biyar ɗin teburi.
Arsenal za ta je gidan Newcastle ranar Laraba, domin buga wasa na biyu a Carabao Cup, inda aka ci Gunners 2-0 a zagayen farko cikin Janairu.
Daga nan Leicester City za ta karɓi bakuncin Gunners a karawar mako na 25 a Premier League ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu.
Ita kuwa City za ta je Leyton Orient a wasan FA Cup ranar Asabar 8 ga watan nan, sannan Real Madrid ta karɓi bakuncin City a wasan farko zagayen cike gurbi a Champions League ranar Talata 11 ga watan Fabrairu.