Matakan gwamnatin Tinubu shida da suka tayar da ƙura a Najeriya a 2024

Lokacin karatu: Minti 7

Tun bayan kama mulki a shekara ta 2023, shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ɓullo da wasu manufofi waɗanda suka tayar da ƙura a Najeriya.

Baya ga manyan ƙudurorin da shugaban ya gabatar a 2023, kamar cire tallafin man fetur da barin naira ta tantance darajarta a kasuwa – waɗanda suka yi matuƙar sauya rayuwar al'ummar ƙasar – a cikin shekara ta biyu ta mulkinsa ma ya ci gaba da gabatar da wasu ƙudurorin.

Wasu daga cikin irin waɗannan matakai sun sa an yi baran-baran, ba tsakanin al'ummar ƙasa da gwamnati kawai ba, har ma a tsakanin ƴaƴan jam'iyya mai mulki.

Gwamnatin Tinubu na cewa tana gabatar da ƙudurorin ne domin inganta yanayin ƙasar, wadda ita ce mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, kuma ɗaya daga cikin mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a nahiyar.

Ga shida daga cikin irin waɗannan matakai na gwamnati da suka fi ɗaukan hankali a Najeriya:

Yarjejeniyar Samoa

Duk da cewa a watan Nuwamban 2023 ne Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar ta Samoa ƙarƙashin ƙungiyar 'Organisation of African, Caribbean and Pacific States' (OACPS), labarin ya ɓulla ga jama'a ne a shekarar 2024.

Tun bayan ɓullar labarin sanya hann kan yarjejeniyar, ƴan Najeriya suka ɓarke da zazzafar muhawara keta ce-ce-ku-ce game da yarjejeniyar musamman kan wasu batutuwan da ta ƙunsa.

Babban abin da ya janyo cece-ku-ce kan batun sanya hannu kan yarjejeniyar shi ne batun ƴancin ɗan'adam.

Sashe na 11 na dokar wanda ya shafi rungumar kowa domin zama al'umma ɗaya ya ce "Ƙasashen OACP za su ɗauki matakan ganowa da magance matsalar tsangwama bisa kowane irin dalili, kamar bambancin launin fata, da jinsi, da harshe, da addini, da ra'ayin siyasa, da haihuwa, da nakasa, da shekarun haihuwa da kuma jinsin mutum."

Wannan sashe ne ya haifar da tayar da haƙarƙari, inda wasu ƙungiyoyi suka yi tir da dokar duk kuwa da cewa gwamnatin Najeriya ta yi bayani kan cewa babu batun auren jinsi a dokar.

Sai dai binciken BBC ya nuna cewa babu wani wuri a cikin yarjejeniyar da ya fito ƙarara ya bayyana cewa dole ne ƙasar da ta sanya hannu kan yarjejeniyar ta halasta auren jinsi ɗaya.

Albashi mafi ƙanƙanta

A ranar Alhamis, 19 ga watan Yunin 2024 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar suka sanar da matsaya kan naira 70,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan ƙasar.

Hakan na nufin an nunka tsohon albashi mafi ƙanƙanta na 30,000 fiye da sau biyu.

Ƙarin albashin mafi ƙanƙanta ya zo ne bayan kai ruwa rana da aka yi tsakanin ɓangaren gwamnati da na ƴan ƙadago game da buƙatar ƙarin albashin domin yin daidai da halin da ƙasar ke ciki.

Sai dai sabon albashin mafi ƙanƙanta ya gaza wanda ƙungiyoyin ƙwadagon suka gabatar na naira 250,000.

A lokacin da yake jawabi ga manema labaru, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC, Joe Ajaero ya ce "a halin da ake cikin yanzu an tsaya ne kan naira 70,000, amma wani abin jin daɗi shi ne ba za mu tsaya har sai nan da shekara biyar kafin a sake duba albashin mafi ƙanƙanta ba.

Taƙaddamar Dangote da NNPC

A ƙarshen shekarar 2023 ne matatar Dangote ta tabbatar da cewa ta fara karɓar ɗanyen man fetur wanda za ta fara tacewa domin samar da man fetur da sauran abubuwan amfani.

Matatar wadda aka kashe dala biliyan 20 wajen gina ta, ita ce mafi girma a Afirka, wadda za ta iya tace gangar man fetur 650,000 a rana, kuma an yi fatan cewa za ta kawo ƙarshen matsalolin da Najeriya da daɗe tana fuskanta a ɓangaren man fetur.

Sai dai ya zuwa farkon 2024, matatar ta Dangote ta riƙa samun saɓani da kamfanin mai na Najeriya NNPCL, inda kamfanin ya fara cewa sinadarin sulfur da ke cikin man matatar ya zarta adadin da ake buƙata.

Haka nan kuma shugaban hukumar kula da harkar man fetur ta Najeriya (NMDPRA) Farouk Ahmed, ya faɗa wa taron manema labarai cewa "man fetur ɗin matatar Dangote bai kai ingancin wanda ake shigowa da shi ba".

Haka nan NNPCL ya zargi Dangote da ƙoƙarin "yin babakere a harkar man fetur".

Saɓanin ya yi zafin da har Aliko Dangote ya bayyana cewa a shirye yake ya sayar wa NNPCL da matatar ta biliyoyin daloli.

A martanin da ya mayar, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya ce:

"NNPCL na iya sayen matatar don tafiyar da ita yadda yake so. Sun bayyana ni a matsayin mai babakere a harkar kasuwanci. Wannan ba gaskiya ba ne kuma bai dace ba, amma babu laifi. Idan za su saya, aƙalla za su yi maganin wanda suka kira mai babakere."

Ƴancin ƙananan hukumomi

An shafe shekaru, ƙananan hukumomi na ƙarƙashin ikon gwamnonin jihohi ta fuskantar tafiyar da kuɗinsu - ta hanyar wani asusu da ake kira na haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi - da kuma wurin zaɓen sabbin shugabanni.

Sai dai a wani hukunci da ta yanke a farkon watan Yuli, Kotun Ƙolin Najeriya ta ce iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnoni ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Alƙalin da ya jagoranci hukuncin Emmanuel Agim ya ce ƙananan hukumomi 774 na Najeriya su ne ke da haƙƙin tafiyar da kuɗaɗensu da suke samu daga kason tarayya.

Kotun Ƙolin ta ƙara fayyace ƙarfin ƙananan hukumomi inda a hukuncin ta ce tana cikin matakan gwamnati – tarayya da jiha da kuma ƙaramar hukuma.

Kotun ta kuma ce gwamnatin jiha ba ta da ikon naɗawa da kuma tuɓe shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi, dole sai ta hanyar zabe.

Ana ganin cewa wannan mataki ya sanya jihohi da dama sun garzaya domin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi.

Sai dai ya zuwa ƙarshen shekarar ta 2024 an ci gaba da kokawa kan cewa har yanzu akwai jihohi da dama da ba su fara amfani da hukuncin kotun ba.

Ƙudurin haraji

A farkon watan Oktoban 2024 ne Bola Tinubu ya aika da wasu ƙudurorin huɗu gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman amincewarta.

Jim kadan bayan haka ne kuma gwamnoni – na APC da na adawa - da ma wasu 'yan ƙasa da dama suka fara nuna adawa.

Yayin wani taro da ƙungiyar gwamnonin arewacin ƙasar ta yi a Kaduna a ƙarshen watan Oktoba, sun ce sabon ƙudirin ya saɓa wa muradun jihohinsu, kuma suka yi kira ga 'yan majalisar yankin su yi watsi da shi a zauren majalisar dokokin ƙasar.

"Abin da ya sa ba mu yarda ba shi ne, ana karɓar harajin VAT ne a hedikwatar kamfanonin maimakon inda sauran rassan kamfanonin ke gudanar da ayyukansu ko sayar da kayayyakinsu,'' in ji shugaban ƙungiyar Gwamnan Gombe Muhammad Inuwa Yahaya – wanda ɗan APC ne.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum na daga cikin waɗanda suka fito ƙarara suka yi adawa da dokar.

A watan hira da BBC, ya ce "Mun yi tir da wannan dokar da aka kai majalisa saboda zai kawo wa Arewa koma-baya...idan wannan ƙudirin ya wuce (nasara) ko albashi ba za mu iya biya ba."

Haka nan an tafka zazzafar muhawara kan dokar a majalisar dattijan ƙasar ta Najeriya.

Sai dai babbar muryar da aka fi ji wajen adawa da wannan ƙudiri ita ce ta Sanata Ali Ndume mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu a majalisar dattawa.

Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda gogaggen sanatan na jam'iyyar APC ya dinga musayar kalamai da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin (wanda ya jagoranci zaman a ranar) kan ƙudirin.

Sabon jirgin shugaban ƙasa

A cikin watan Agusta ne aka tsinkayi wani jirgi ƙirar Airbus A330 a filin jirgin sama na Abuja, wanda aka bayyana cewa shi ne sabon jirgin da shugaban ƙasar zai riƙa amfani da shi.

Kuma ba tare da ɓata lokaci ba, Bola Tinubu ya hau jirgin zuwa ƙasar Faransa, a wata ziyara da ya kai.

Cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X, ya tabbatar da balaguron amma bai faɗi dalilin zuwan Tinubu Faransa ba.

"Sabon jirgin da aka sayo ƙasa da farashin kasuwa, zai taimaka wa Najeriya rage kashe kuɗin tattali da na mai, wanda ya kai miliyoyin dala duk shekara," a cewar sanarwar.

Jirgin mai shekara 15 da ƙerawa wanda kuma aka ƙiyasta farashinsa kan dala miliyan 600, an ce yana da faffaɗan wurin zama na alfarma kuma yanzu yana ɗauke ne da lamba 5N-NGA, inda ya maye gurbin Boeing BBJ 737-700 mai shekara 19 da ƙerawa.

Wasu jami'an gwamnatin ƙasar sun faɗa a baya cewa akan kashe kuɗaɗe masu yawa na kula da jiragen shugaban ƙasar ne saboda tsufansu.

Wasu masu sharhi na siffanta sayen jirgin a lokacin da ya dace a ce ƙasar ta matse bakin aljihu a matsayin rashin tausayi ga miliyoyin 'yan ƙasa da ba su iya samun abincin da za su ci.