Ko albashin naira N70,000 zai wadaci ma'aikacin Najeriya?

Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni ne shugaban Najeriya Bola Tinubu da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar suka sanar da matsaya kan naira 70,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan ƙasar.

Hakan na nufin an nunka tsohon albashi mafi ƙanƙanta na 30,000 fiye da sau biyu.

Ƙarin albashin mafi ƙanƙanta ya zo ne bayan kai ruwa rana da aka yi tsakanin ɓangaren gwamnati da na ƴan ƙadago game da buƙatar ƙarin albashin domin yin daidai da halin da ƙasar ke ciki.

Najeriya na fuskantar tashin farashin kayan masarufi da sufuri, yayin da rajarar kuɗin ƙasar ke ci gaba da zubewa.

Cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar ya yi a ranar da ya karɓi mulki cikin watan Maris na shekara ta 2013, ya sanya farashin kayan masarufi ya nunnunka, lamarin da ya jefa al'ummar ƙasar cikin mummunan hali.

A watan Yuni, alƙaluma daga Hukumar ƙididdiga ta Najeriya sun nuna cewa hauhawar farashi ta kai 34.2%, mafi yawa a cikin kusan shekara talatin.

Ko wannan ƙarin albashi zai iya cike giɓin da tashin farashin a ƙasar ya haifar ga ma'aikata?

BBC ta ji ra'ayin wasu ma'aikata da kuma masana tattalin arziƙi kan hakan...

Maganar isa ko rashin isan sabon albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan Najeriya ya danganta ne da inda ma'aikaci ke rayuwa da girman iyalinsa.

A bisa al'ada, rayuwa a cikin birane ta fi tsada yayin da rayuwa a yankunan karkara ta fi sauƙi.

Wani ma'aikacin gwamnati da BBC ta tattauna da shi a cikin garin Abuja ya ce: "Yanzu kamar waɗanda suke aiki a Abuja amma suna zama a Suleja a gaskiya salarin (albashin) ya kasa".

Ya ƙara da cewa haka nan batun iyali, idan mutum na da yara da yawa zai iya yiwuwa albashin ya gaza biya masa buƙatunsa.

Ya ce "ka ga ni a matsayin yawan yaran da nake da su, a gare ni babu matsala, zan iya rayuwa da 70,000."

Sai dai Mustapha Muhammad, wani ma'aikaci a jihar Kano da ke Najeriya ya ce: "Wannan (sabon albashi mafi ƙanƙanta) babu abin da zai yi".

A cewar sa "Farashin buhun shinkafa ya zarce sabon albashin, mu ɗauka cewa za ka sayi rabin buhun shinkafa ne a wata, abin da zai rage a hannunka bai wuce 30,000 ba.

Da me za ka yi amfani wajen sayen sauran kayan abinci kamar sukari da manja, kuma da me za ka biya kuɗin zirga-zirga?"

Abubakar Isiyaku, wani ma'aikaci kuma manomi da ke jihar Kaduna ya ce ƙarin albashin ba zai ishi matsakaicin ma'aikaci rayuwa ba.

A cewar sa "idan aka duba halin da ake ciki na tsadar abinci, buhun shinkafa ƴar gida ya kai sama da naira 65,000, buhun masara kuma ya kai sama da 80,000, ga matsalar sufuri sanadiyyar janye tallafin man fetur, ga tsadar kuɗin lantarki, ga biya wa yara kuɗin makaranta da sauran wahalhalu."

Ya ƙara da cewa kuɗin ba za su ishi ma'aikaci sauke nauyin da ke kansa sannan ya gudanar da aiki yadda ya kamata ba.

Ra'ayin masana

A tattaunawarsa da kafar talabijin ta Channels, wani masani kan harkar kuɗi kuma shugaban ƙungiyar BudgIT, mai sanya ido kan kasafin kuɗi a Najeriya, Seun Onigbinde ya yi amannar cewa sabon albashi mafi ƙanƙanta na naira 70,000 ba zai kashe ƙishin ma'aikatan Najeriya ba idan aka yi la'akari da tashin farashin da ke addabar ƙasar.

Ya ce "Ba zai isa ba, a ra'ayina. Amma babbar nasara ce da aka cimma hakan.

Ya bayyana cewa yana ganin sabon albashin ba zai rage raɗaɗin matsin tattalin arziƙin da al'umma ke ciki ba yadda ya kamata.

A cewarsa: "Bai kai yadda na yi tsammani ba. Na so a ce an kai tsakanin naira 100,000 zuwa 120,000 kasancewar abubuwa sun yi muni sosai idan aka duba yadda farashi ke tashi.

Amma gwamnati za mu tsaya mu ga abin da zai faru, kasancewar gwamnati ta ce za a iya sake tattaunawa kan batun albashin a cikin shekara uku."

A nasa ɓangaren, Dakta Ahmed Adamu na Jami'ar Nile da ke Abuja "wannan sabon albashin ba zai yi tasiri ba face rage darajar naira.

"Rayuwar da ma'aikata ke yi a lokacin da suke karɓar naira 30,000 ita ce rayuwar da za su ci gaba da yi a yanzu saboda tashin farashin kayan masarufi."

Ya ce hakan zai faru ne saboda ƴan kasuwa za su ƙara farashin kaya sanadiyyar ƙarin albashi da aka yi wa ma'aikata.

Ya ƙara da cewa: "wannan mataki babban tasirin da zai yi shi ne rage darajar naira."

A cewarsa Najeriya na kashe maƙudan kuɗaɗe a kan biyan albashi, idan aka ɗaga mafi ƙanƙantar albashi a ƙasar nauyi zai ƙara yawa a kan gwamnati, wanda hakan zai hana gwamnati yin ayyukan ci gaba.

Sannan ya kuma ce: "Idan ka ƙara yawan kuɗin da mutane ke samu ba tare da an ƙara gudumawar da suke bai wa tattalin arziƙi ba, abin da zai biyo baya shi ne tashin farashi.

'Ƙarin albashi ba shi ne mafita ba'

A cewar Dakta Adamu ya kamata Najeriya ta sake duba dokokinta da suka shafi ma'aikatan gwamnati don yin gyara a ɓangarorin da suka dace.

Daga cikin sauyin da ya ce ya kamata a kawo su ne a bar ma'aikatan gwamnati su shiga harkar sana'o'i, a maimakon halin da ake ciki wanda aka haramta wa ma'aikatan gwamnati yin wata sana'a baya ga noma da harkokin gona.

Ya ce kamata ya yi a rage yawan sa'o'in aikin ma'aikata, sai a ba su damar yin sana'a matuƙar dai sana'ar ba za ta shafi yadda suke gudanar da ayyukansu na gwamnati ba.

Ya kuma ce a maimakon yi musu ƙarin albashi, sai a haɗa kudin a ba ma'aikatan a matsayin bashi mai sauƙi wanda zai taimaka musu wajen fara sana'a.

Ya ce: "Ta hakan ne ma'aikata za su taimaka wajen inganta tattalin arziƙin ƙasa da kuma samar da ayyukan yi ga wasu."