Mene ne hukuncin yin sallar Juma'a ranar Idi?

Asalin hoton, BBC/GRAB
Sallar Idin babbar salla ta bana ta dace da ranar Juma'a ta 10 ga watan Zhul Hajji, wani abu da ke janyo kace-nace dangane da yin ɗaya a bar ɗaya ko kuma haɗa su duka biyun.
BBC ta tattauna da wasu malaman addinin Musulunci guda biyu, Sheikh Ahmad Gumi da Sheikh Halliru Maraya a kwanakin baya domin jin fatawoyin malamai a kan haka.
Kuma malaman sun ce addinin Musulunci tuni ya yi tanadi game da haɗa waɗannan ibadun biyu.
Fatawar Sheikh Gumi

Asalin hoton, BBC/GRAB
Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, malamin addinin Musulunci ya ce idan Idi ya dace da ranar Juma'a to Musulmi na da Idi guda biyu.
"Idan an samu Idi ya zo ya dace da ranar Juma'a to Musulmi na da taro guda biyu. Taron idi da ake yi duk shekara-shekara sannan kuma akwai haɗuwa ta ranar Juma'a.
Kowacce ibada ce daban ba tare da an haɗa ta da wata ba. Sai dai waɗanda Juma'a ba ta wajaba a kansu ba waɗanda suke mutanen ƙauye, mutanen nesa kamar mutanen al'awaali ko kuwa al'aliyaa waɗanda ke barin ƙauyukansu su zo Madina sallar Idi to waɗannan an ba su rangwame cewar ba sai sun koma Madina sallar Juma'a ba.
Ba a ɗuke musu sallar Azahar ba kamar yadda muka ji wasu na faɗa cewa wanda ya zo sallar Idi ka da ya je sallar Juma'a. Wannan fahimtar kuskure ne. Sai dai kuma idan akwai larura kamar tafiya ko rashin lafiya." In ji Sheikh Ahmad Gumi.
Fatawar Sheikh halliru Maraya

Asalin hoton, BBC/Grab
Sheikh Halliru maraya wanda malamin addinin Musulunci ne a Kaduna ya ce al'amarin ba na rikicewa ba ne.
"Irin wannan abu ya taɓa faruwa lokacin manzon Allah kuma abin da annabi ya yi shi ne ya je Idin kuma ya je masallaci gya gabatar da sallar Juma'a. A lokaicn da aka yi salalr Idi sai ya ce yau ne sallar Idi kuma mun yi Idi kuma game da sallar Juma'a duk wanda yake so zai iya sallar Juma'a amma mu dai za mu yi sallar Juma'a ɗin"
"Saboda haka babban abin da ya dace shi ne mutane su dage su yi sallar Idin sannan kuma su yi sallar Juma'a. Wannan shi ne abin da ya kamata."
"Akwai magana kuma mai raunin gaske da ke cewa idan mutum ya yi sallar Idi to wai da Juma'a da Azahar ɗin duk sun faɗi. Amma wannan malamai kaɗn ne suka yadda da ita saboda tana da matuƙar rauni."











