Abu biyar da suka kamata ku sani game da aikin Hajji

Asalin hoton, Getty Images
Hajji na ɗaya daga cikin ginshiƙan Musulunci guda biyar, inda a shekarun nan kimanin mutum miliyan biyu ke taruwa a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya domin aiwatar da shi.
Aikin wajibi ne a kan duk wani Musulmi baligi wanda ke da hali da lafiya, aƙalla sau ɗaya a rayuwa.
Hajji na ɗaya daga cikin ayyukan ibada da suka fi tara al'umma a wuri ɗaya daga sassa daban-daban na duniya.
Ga wasu bayanai da suka kamata ku sani game da aikin
Ka'aba - wadda annabi Ibrahim ya assasa
Kasancewar aikin Hajji ɗaya ne daga cikin ginshiƙan addinin Musulunci wanda Musulmai ke aikatawa a kowace shekara, wani zai yi tunanin cewa aikin ya fara ne daga lokacin annabi Muhammad (SAW).

Asalin hoton, EPA
Sai dai aikin ya samo asali ne tun lokacin annabi Ibrahim, wanda shi ne ya gina ɗakin na Ka'aba, kamar yadda addinin Musulunci ya bayyana.
Annabi Ibrahim shi ne ake kira Abraham a addinin kirista da na Juda, kuma ginshiki ne a waɗannan addinai.
Babu nuna wariyar jinsi

Asalin hoton, Yassine Gaidi/Anadolu Agency
Akasin yadda ake samu a wasu masallatai ko wuraren ibada na Musulunci, inda akan ware wuraren ibada na mata daban da na maza, a lokacin aikin Hajji maza da mata na gudanar da aiki iri ɗaya ne kuma a wuri ɗaya.
Daidaito ba tare da la'akari da muƙami ba
Masu aikin Hajji na sanya kaya iri ɗaya daidai da tanadin addinin Musulunci, wanda hakan ke nuni da cewa kowa ɗaya ne a wurin Mahalicci.

Asalin hoton, EPA
Musulmai maza kan yafa ihirami, wanda tufafi ne mai sauƙi, hakan na nuna cewa kowane ɗan'adam daidai yake da kowa komai dukiya ko kuma matsayinsa.
Su kuma mata suna sanya kaya mai sauƙi wanda zai rufe dukkanin sassan jikinsu baya ga fuska.
Hawa tuddai
Ɗaya daga cikin manyan ayyukan Hajji shi ne Ɗawafi, inda maniyyata ke zagaye ɗakin Ka'aba sau bakwai - a farko da kuma ƙarshen aikin Hajji.
Sai dai wani babban aikin da ake yi shi ne kai-komo tsakanin tuddai biyu.
Wannan shi ne tafiyar sassarfa tsakanin dutsen Safa da kuma Marwa sau bakwai, wadanda ke a harabar Masallacin Harami.
Wannan aiki na alamta wahalar da Hajara, matar annabi Ibrahim ta sha lokacin da ta riƙa kai-komo tsakanin tuddan biyu tana neman ruwa domin bai wa jaririn ɗanta.
Maƙurar aikin Hajji
Yayin da ake gudanar da ayyuka da dama a harabar Masallacin Ka'aba, maƙurar aikin Hajji na faruwa ne a dutsen Arfa, wani tantagaryar fili da ke wajen birnin Makkah.

Asalin hoton, EPA
A nan ne masu ibada kan taru tun daga ɓullowar rana zuwa faɗuwarta suna gudanar da tsantsanr addu'a, da nazari kan abubuwan da suka aikata da kuma karatun Ƙur'ani.
Wannan wuri mai tsarki yana da matuƙar muhimmanci ga Musulmai. Bayani ya tabbatar da cewa a kan wannan dutse ne annabi Muhammad ya gabatar da huɗubarsa ta ban-kwana.










