Abu biyar da suka kamata ku sani kan jigilar maniyyatan Najeriya na 2025

Asalin hoton, NAHCON/X
A ranar Juma'ar nan ta 9 ga watan Mayu ne ake sa ran alhazan Najeriya ke fara tashi zuwa ƙasa mai tsarki kamar yadda hukumar alhazan ƙasar ta tabbatar.
Ga wasu abubuwa guda biyar da suka kamata ku sani kan aikin hajjin na bana.
1) Jirgin farko zai tashi daga Owerri

Asalin hoton, NAHCON/X
Hukumar alhazan Najeriya ta ce za a ƙaddamar da aikin hajjin bana ne da tashi alhazai daga filin jirgin sama na birnin Owerri da ke jihar Imo a kudu maso gabashin Najeriya.
Ƙaddamar da fara tashin alhazan zuwa ƙasa mai tsarki wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma za su jagoranta, zai bai wa maniyyata 315 jihohin Imo da Abia da Bayelsa tashi zuwa ƙasa mai tsarki.
Jirgin Airpeace ne zai yi jigilar alhazan daga Imo. Wannan ne karon farko da wata jiha mai ƙarancin yawan Musulmai a Najeriya ke karɓar baƙuncin tashin alhazai na farko.
2) Ƙarin jirage uku a ranar farko

Asalin hoton, NAHCON/X
Bugu da ƙari, ƙarin jirage guda huɗu za su yi jigilar ƙarin maniyyata a ranar 9 ga watan na Mayu.
Jirgin Max Air zai tashi da jihar Bauchi da kuma jiragen FlyNas guda biyu da za su kwashi alhazai daga jihar Kebbi da Osun da Legas da kuma wanda zai tashi daga jihar Neja duka a ranar farko.
Ana sa ran jiragen za su kwashi alhazai 2,528 a ranar Juma'ar nan.
3) An rufe karɓar kuɗin aikin hajji
Hukumar alhazan ta Najeriya, NAHCON ta ce ta rufe karɓar kuɗin aikin hajjin bana ranar 2 ga watan Mayun 2025 wato mako guda kafin fara aikin jigilar alhazan zuwa ƙasa mai tsarki.
Hukumar ta ce duk maniyyacin da ya biya kuɗin aikin hajji bayan ranar 2 ga watan na Mayu to za a mayar masa da kuɗin nasa.
Shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh ne dai ya ƙara kwanakin biyan kuɗin bayan ƙarewar lokacin a ranar 25 ga watan Maris.
4) Maniyyata fiye da 40,000 daga Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Wata sanarwa da hukumar alhazan ta NAHCON ta fitar mai sa hannun mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, ta ce ya zuwa ranar 2 ga watan na Mayu da aka rufe karɓar kuɗin maniyyata, maniyyata 40,671 suka biya.
5) Ranar kammala jigila
A sanarwar da ta fitar, hukumar alhazan ta Najeriya ta ce za ta kammala jigilar kwashe dukkannin alhazan ƙasar fiye da dubu 40 a ranar 24 ga watan Mayu. Kuma hakan na nufin za a kwashe makonni biyu ana jigilar.
Dangane da ranar da za a fara kwasar alhazai domin komawa gida, hukumar ta ce za ta fara kwaso mahajjata daga ranar 13 ga watan Yuni sannan za a ƙarƙare a ranar 2 ga watan Yulin 2025.










