Shawara 10 ga mahajjata kan zaman Muna da Muzdalifa

Asalin hoton, Getty Images
Bisa tsari da ƙa’ida ta addini, a ranar Alhamis wacce ta yi daidai ta 8 ga watan Dhul Hijjah, wato 7 ga watan Yuli ke nan, ita ce ranar da mahajjatan da suka isa Saudiyya ke tafiya Muna don fara ibadun aikin Hajji.
Kamar yadda yake a tsari, da an yi sallar asuba hukumomi ke fara jigilar dukkan maniyyata daga Makkah zuwa Muna inda za su shafe kwana huɗu suna gudanar da ibadun da su ne Hajjin.
Ga wasu, ziyarar kan kasance zuwansu ne na farko, wasu kuma sun sha zuwa, wasu kuma a kan niyya suke ko baɗi ko baɗin-baɗaɗa.
Sai dai baya ga irin shirin da mahajjatan za su yi ta fuskar ibadah, akwai wasu shirye-shiryen da suka kamata mahajjatan su yi don kimtsa kansu da samun saukin al’amura yayin zaman wadannan ranaku.
Akwai tambayoyi da yawa a zuƙatan farkon zuwa kan: yaya tsarin tafiya Muna yake? Me ya kamata su tanada? Wane irin shiri za su yi? Yaya zaman yake kasancewa?
Waɗannan su ne tambayoyin da za mu duba amsoshinsu a wannan maƙala, tare da bai wa mahajjata shawarwari kan yadda za su yi wannan zama.
Mun tattaro bayanai daga tsofaffin alhazai da dama da suka sha zuwa Makkah aikin Hajji.
Shirya kayan sanyawa

Abu mafi kyau ga mahajjata idan za su tafi Muna ranar 8 ga wata to kar su kwashi kaya da yawa. Saboda zama ne na ɗan lokaci ba ka buƙatar tattara himilin kaya.
Mafi yawan tsoffin hannu da suka sha zuwa aikin Hajji sun ce idan maniyyata suka tashi hada jaka, mafi kyau shi ne su saka Ihrami kala biyu, da kuma kayan sawa marasa nauyi su ma kala biyu.
Wadannan haramin dama ɗaya za a tafi da shi a jiki ne, kuma ba za a cire ba har sai an sauka arfah, an yi jifan farko an kuma je an yi ɗawafin ranar sallah.
Sai dai ɗayan da za a ɗauka a matsayin ƙarin harami, ana iya musanyawa da shi idan na farkon ya yi datti, musamman ga wadanda ba za su sauke ɗawafin ranar sallah ba har sai washe garin idin.
Sannan sauran kaya nau’i biyu na gida kuma amfaninsu shi ne idan aka cire harami bayan sauke ɗawafi, to mutum na iya kwalliyar sallarsa da su a ran sallah.
Kazalika yana iya sauya ɗayan ma a washe gari.
Kaya ƴan ciki
A cikin ƴar ƙaramar jakar haɗa kayan, kar a manta a zuba kaya ƴan ciki irin su singileti, ko shimi ga mata, da kamfai da dai sauran ƙananan kaya masu muhimmanci.
Sannan tun da ba a sanya turare a lokacin zaman ihrami, to zai yi kyau mutum ya tanadi alumun don yin wanka da shi.
Hakan zai kawar da ɗan bashi-bashin da ka iya tashi a jiki.
Amma ana iya tafiya da su dan man shafawa da turare ta yadda idan ka sauke dawafin ranar sallah za a dan shafa. (Sai dai ka da a manta da hukuncin shari’a musamman ga mata kan hakan.)
Abinci da abin sha fa?
Ba kwa bukatar sai kun yi sayayyar kayan abinci don tafiya Muna don ana samun duk abin da kuke buƙata.
Ku tuna cewa idan kuka lodi kaya fa zuwa Muna za su iya zame muku ɗawainiya, don a lokacin da za ku tafi filin Arfa, inda daga can za ku wuce Musdalifa.
Abin da za a ba ku shawarar ɗauka na dangin abinci ba za su wuce ɗan yaji kaɗan da wataƙila irin ɗan biskit da ba zai zame muk dako ba.
Filin Arfa

Filin Arfa waje ne da ake yini guda, tun asuba har bayan la’asar.
Kuma daga can ba Muna za a koma ba, Muzdalifa za a wuce sannan wajen jifa, kafin daga bisani a koma Musdalifa.
Hakan na nufin sai mutum ya shirya a nutse daga batun me za a tafi da shi har zuwa kan me za a bukata.
Abu mafi a’ala a nan shi ne a guji lodar kaya a tafi da su don kuwa idan kuka kwashi kaya to za ku sha wahalar dawainiya da su.
Kuna iya barin jakar kayan sawarku a Muna, sai ku nemi wata karamar jakar ta goyo.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cikin wannan jakar ta goyo zai yi kyau musamman ga mata, ki nemi fallen zani daya ki sa a ciki, a nemi tabarma irin wacce ake sayarwa a can mai saukin nadewa ko abin sallah a sa a jakar.
Sannan a dauki man goge baki da burushi. Da yake idan ana cikin harami ba a sanya turare, to ba kwa bukatar daukarsa.
Kazalika yana da kyau ki tanadi ruwa na kananan gorori duk da dai akan samu a filin Afra, amma ya kasance ba a rabo da daukarsa a jakar.
Sannan daukar lema ma abu ne da ka iya taimakawa saboda tsananin ranar da ka iya ƙwallewa, sannan kuna iya sa karin takalmi a cikin jakar saboda gudun tsinkewar na ƙafarku.
Amma dama a irin wannan yanayi dama sanya takalmi sau-ciki mai sauki shi zai fi ba da ma’ana.
A cikin jakar dai duk ana iya saka Kur’ani ko da karami ne saboda tilawa da sauran kananan littafan addu’o’i.
Amma shawara mafi dacewa tun da a yanzu wayoyin komai da ruwanka sun wadata, kana iya sauke manhajojin Kur’ani da na addu’o’i ka karanta daga kan waya.
Ana raba abinci sau biyu ko ma uku a filin Arfa, don haka ba kwa bukatar lodar kayan abinci daga Muna a lokacin tafiya.
Sai dai a shawarce zai yi kyau daga cikin abinci mutum ya ɗan adana kayan ƙwalam din wato (snacks) a cikin ƴar jakar goyen saboda za su iya yi maka rana a Muzdalifa.
Muzdalifa

Wannan waje ne da ake yada zango bayan tasowa daga filin Arfa, inda ake kwana sai asuba kuma a kama hanyar Jamrah, wato wajen jifan Shaidan.
Zaman Muzdalifa na daga cikin abin da dole sai an yi a cikin ibadar aikin Hajji, kuma a can ake tsinto duwatsun fa za a yi amfani da su wajen jifan.
Muzdalifa fili ne fetal kuma a nan za a kwana, duk da cewa an dauke wa tsofaffi da masu rauni da marasa lafiya da za ta cewa za su iya barin wajen da daddare kafin asuba.
Hakan na nufin akwai bukatar a yi wa zaman Muzdalifa shiri mai kyau yadda ba za a galabaita har a kasa aiwatar da sauran ayyukan ibadar ba.
Kun tuna shawarar sayen tabarma da aka ba ku?
To a Muzadlifah za ta fi amfani don kuwa ba wanda zai ba ku abin shimfida, taku za ku shimfida ku zauna a kai har ma da kishingida idan da hali.

Akwai yiwuwar a bukaci cin abinci a Muzadlifa, sai dai da wahala a samu abincin mai kyau da inganci.
Ana samun na sayarwa a wurare daban-daban, amma gara ka tsaya a iyakar duniyar da aka ajiye ka gudun tafiya neman wani abu ka ɓata. Hausawa kan sayar da abinci a wajen.
Sai dai gaskiya yawanci za ku gan shi a bude duk ƙura tana buɗe shi.
A wannan lokaci ne tsarabar abincin da kuka ƙullo a jakar goyonku daga filin Arfa za ta yi muku amfani.
Muzdalifa na da girma da rikitarwa, don haka a shawarce gara ku nutsu waje guda, ku je banɗakin da ke kusa da ku don yin alwala ku dawo matsuguninku ku yi sallah don gudun ɓata.
Idan aka sallace asuba, sai ku ɗan nemi wani abu ku ci don samun ƙarfin daɓar sayyadar tafiya filin jifa.
Jamrah, Jifan Shaiɗan
Aiki ga mai ƙare ka. A nan ne fa za ku nemi motocin da ke tafiya wajen jifa, amma wasu sun gwammace su daɓa da ƙafa saboda cunkoso da kuma rufe hanyoyi da ake yi.
Za ku yi tafiya iya tafiya. Don haka ne muka ce kuna buƙatar sanya wa cikinku wani ɗan abu da kuma guzurin ruwa a wannan jakar goyon don taimakon kai.
A mafi yawan lokuta rana kan take, don haka shan ruwan ke da fa’ida.
Hukumomin Saudiyya kan samar da wasu bututai masu kama da shawa mai feshin ruwa.
Duk inda kuka ga wannan kuma dama ƙarfi ya fara ƙarewa, to zai yi kyau ku matsa kusa ruwan ya feso muku don samun sa’ida.
Dama ya kamata a ce tun daga Makkah kafin ku tafi Muna kun loda data a wayarku.
Hakan zai taimaka muku wajen amfani da manhajar taswirar nuna hanya wato Goggole Map, saboda gudun ɓata za ta kai ku har wajen jifan.
Sannan akwai wani ɗan agogon fata da ake rabawa wanda idan ka ɓata za ku iya nuna awa askarawa su gano wane yanki ya kamata ku bi.
Bayan kammala jifa abu na gaba shi ne tafiya Makkah don yin ɗawafin ranar sallah.
Amma wasu sun gwammace su koma masaukinsu a Muna su huta tukunna kafin su je Makkan.
Tafiya Makkah na nufin ƙarin tafiya ba tare da hutu ba amma kuma sauke nauyi ne.
Komawa Muna kuma ko da kun koma kun yi wanka to ba fa za ku cire harami ba sai dai ku canza idan kuna da wani. Wannan ita ce fa'idar cewa ku tafi da harami kala biyu.
Muna a ragowar kwanaki

Wani abin ɗaure kai da mamaki shi ne yadda mutane ke zagewa su lodi kaya su tafi da su Muna daga Makkah, har ka ga sun zage suna wanki.
Maganar gaskiya yadda Muna take zama ne na ɗan lokaci takurawa kai ne ka je kana wanke-wanke a can.
Wani lokacin hatta da robobin zuba ruwan sha na alhazai mutane ke dauka suna wanki da su.
A can sama idan ba ku manta ba mun yi maganar cewa a tanadi kayan ƴan ciki wato undies. A shawarce ko su bai kamata a wanke a Muna ba.
A bari idan an koma Makkah sai a wanke dukkan kayan da suka yi dauɗa.
Sannan yana da kyau a nutsu a zauna waje guda a Muna a guji zirga-zirga marar amfani.
Kamun kai na daga cikin abin da ya kamata mahajjata su kula a yayin wannan zama na ibadah.
Amfani da banɗaki
Ni dai daga cikin abin da na koya a zaman Muna akwai ɗaukar matakan kariya musamman na amfani da banɗakuna.
Yanayin da banɗakuna ke ciki a Muna ba mai kyau ba ne sosai. Ga kuma layi na wanka da amfani da wajen.
Abu mafi kyau shi ne idan kuna son yin wanka to da zarar kun yi sallar asuba sai ku tafi kafin a fara layi.
Yana da kyau ku tanadi magungunan kashe ƙwayoyin da ke yaɗa cututtuka irin su detol da izal.
Ku watsa su a banɗakin sosai don taimakawa wajen kashe ƙwayoyin cuta.
Ku tabbatar kuna da jakar da ke dauke da kayan wankanku don sosonku ko sabulu su fadi kasa.
Sannan burushinku ya kasance mai murfi ne don gudun taba wani abu marar kyau.











