Arfa: Mafificiyar ranaku ga Musulmi - Maqari

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Arfa: Mafificiyar ranaku ga Musulmi - Maqari

Asabar 15 ga watan Yunin 2024 ce ta zamo daidai da 9 ga watan Dhul-Hajj ta shekarar 1445 a kalandar Musulunci - ranar da maniyyata aikin Hajji za su gudanar da tsayuwa a dutsen Arfa.

Arfa ɗaya ne daga cikin rukunan aikin hajji a Musulunci, inda hajji ba ta cika sai da shi, kamar yadda malamai suka bayyana.

Baya ga haka, ranar na cike da falala a addinin na Musulunci, in ji Sheikh Ibrahim Maqari, ɗaya daga cikin limaman babban masallacin ƙasa da ke Abuja, Najeriya.

Kalli bidiyon da ke sama domin samun cikakken bayani.