Dalilai biyar da suka sa dabbobi suka yi tsada a bana

Asalin hoton, Getty Images
A daidai lokacin da Babbar Sallah ta shekarar 2025 ke ƙaratowa - lokacin da musulmi suke shirye-shiyen gabatar da shagulgulan bukukuwan ranar - musamman ma layya ga masu iko, lamarin na bana kamar ya zo da wani salo na ba-zata ga waɗanda suke shirin yin layyar.
A Najeriya, farashin raguna a bana sun tashi a kasuwanni, lamarin da ya zo a daidai lokacin da ƴanƙasar ke kokawa kan tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
Tsadar ce ta wasu suka fara tunanin haƙura da layyar a bana domin yin wasu abubuwa daban da kuɗinsu.
Tsadar rayuwa ta ƙara ta'azzara ne a ƙasar tun bayan da Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur, sannan darajar naira ta karye, lamarin da ya jefa ƴanƙasar cikin matsin rayuwa, har aka gudanar da zana-zangar tsadar rayuwa a faɗin ƙasar domin nuna rashin jin daɗi.
Wannan ya sa BBC ta ziyarci kasuwannin dabbobi a wasu yankunan ƙasar, domin jin yadda take wakana da kuma masu saya domin jin abubuwan da suke jawo tsadar dabbobin.
Datse fatauci daga Nijar

Shugaban ƙungiyar masu sayar da dabbobi da sarrafa nama, kuma shugban ƙungiyar ƴankasuwar dabbobi na Goron Dutse, Alhaji Bashir Sule Ɗantsoho ya bayyana wa BBC cewa daga cikin abubuwan da suka jawo tsadar raguna da ma sauran dabbobi a Najeriya, akwai matakin da Nijar ta ɗauka na hana fitar da su wajen ƙasar.
A watannin baya ne gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da haramcin fitar da dabbobi daga ƙasar zau Najeriya.
Alƙaluman cinikayyar ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya, sun nuna cewa a shekarar 2023 kawai Nijar ta fitar da dabbobin da suka kai na dala miliyan 3.93 zuwa Najeriya.
Ministan kasuwancin ƙasar ya ce gwamnati ta umarci jami'an tsaro su ɗau matakan da suka dace a kai da kuma hukunta duk wanda ya saɓa wa sabuwar dokar.
Matsalar tsaro
Wani abu da Alhaji Ɗantsoho ya bayyana a cikin abubuwan da suka jawo tsadar dabbobin shi ne matsalar tsaro, wanda a cewarsa, ya shafi harkokinsu matuƙar gaske.
"Harkar tsaro ta rikirkita abubuwa a arewacin Najeriya. Wuraren da muke zuwa samo dabbobin suna fama da matsalar tsaro," wanda a cewarsa ya sa dabbobin suka yi tsada.
Yankin arewacin Najeriya ya ɗauki shekaru yana fama da matsalolin rashin tsaro na Boko Haram da ƴanbindiga, lamarin ya shafi harkokin yau da kullum, ciki har da kasuwancin yankin.
Daga cikin abubuwan da suke tsakiyar rikice-rikicen ƴanbindiga akwai dabbobi, inda a lokuta da dama, ɓarayin dajin sukan kashe mutane su kwashe musu dabbobi su shiga daji da su.
Darajar naira
Haka muna Ɗantsoho ya ce yadda darajar naira ta faɗi warwas idan aka kwatanta da sauran kuɗaɗen duniya ma matsala ce ga kasuwancinsu.
Ya ce, "idan muka fita saro dabbobin a wasu ƙasashe, sai mun canja naira zuw kuɗinsu na can," in ji shi, inda ya ƙara da cewa hakan ya sa suke saro dabbobin da tsada, kuma abincinsu da magungunansu sukaa yi tsada.
A watan Yunin 2023 ne babban bankin Najeriya, CBN ya aiwatar da tsarin da ya ce ya bijiro da shi domin daidaita darajar naira, inda banki ya fara amfani da tsarin sakewa naira mara kasuwa ta yi halinta wajen tsayar da farashin kuɗin da dalar Amurka.
Masana sun ce wannan matakin ne ya taimaka wajen karya darakar kuɗin ƙasar, saboda tattalin arzikin Najeriya na buƙatar dala wajen tafiyar da shi kasancewar galibi ana shigo da kayayyakin da ƙasar ke amfani da su ne daga wasu ƙasashen kuma ba ta iya samar da kayayyakin da al'ummarta ke buƙata.
Tsadar sufuri
Haka kuma ƴankasuwar sun bayyana cewa tsadar da suke fuskanta wajen safarar dabbobin daga wuraren da suke sarowa zuwa kasuwanninsu na ƙara ta'azzara farashin.
Yakubu Sani, shugaban ƴankasuwar dabbobi a Masaka da ke babbar hanyar Abuja zuwa Keffi ya ce raguwan da suke kashe naira 2,500 zuwa 3,000 a kuɗin sufuri, "yanzu muna kashe kimanin naira 8,000 zuwa 10,000," in ji shi.
Shi ma Ɗantsoho ya ce, "a baya kuɗin motar dabba ba ya wuce 800 zuwa 1,000, amma yanzu bayan kuɗin haraje-haraje na gwamnati da kuɗin leburori, kuɗin mota kawai ya 4,000 zuwa sama."
Yawanci ana saro dabbobin ne daga wasu wurare, sannan a yi sufurinsu zuwa birane domin sayar da su ga masu saya.
Abinci da magunguna
Haka kuma yanayin yadda tattalin arzikin ƙasar ya taɓarɓare ya jawo hauhawarar farashin kayan abinci da magungunan dabbobin kamar yadda na mutane ya tashi, wanda bai rasa nasa da karyewar darajar naira.
Tsadar abinci da magunguna sun sa masu dabbobin sun ƙara kuɗi, domin mayar da kuɗinsu, da samun riba.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Domin jin yadda farashin dabbobin suke a yanzu da ake ƙirga kwanaki kafin ranar ta Sallah, Alhaji Ɗantsoho ya bayyana mana yadda farashin dabbobin suke a yanzu.
- Raguna: Daga 150,000 zuwa miliyan 1.5
- Namijin Sa: Daga 600,000 zuwa sama
- Saniya: Daga 500,000 zuwa sama
- Raƙumi: Daga 650,000 zuwa sama
Sai dai ƴankasuwar sun ce duk da cewa kasuwar ba kamar ta bara ba, banar ma yanzu kasuwar ta fara buɗewa kaɗan-kaɗan.
Yakubu Sani ya ce a bara lokacin da sallah ta ƙarato haka, "raguna sun fi yawa, sannan kullum kasuwar a cike take ba kamar wannan karon ba da mutane suke zuwa jefi-jefi."
Shi kuma Ɗantsoho cewa ya yi, "muna godiya Allah domin duk halin da muke ciki, dole mu yi wa Allah godiya. Amma da yanzu da sallar take ƙara matsowa, kasuwar na ƙara buɗewa."
BBC ta yi kiciɓis da wani mai suna Muhammad Idris a kasuwar Masaka, wanda ya ce farashin ragon ba yadda ya yi tsammani ba ne.
"Na je kasuwar domin sayen ragu na kimanin naira 150,000 zuwa 180,000, amma sai na ga sun yi ƙanana, kamar ba su kai a yi layya ba."
Ya ce yanzu zai ɗan jira ne, "amma idan bai yiwu ba, zan haƙura kawai sai in saya nam a kasuwa kawai a yi amfani da shi."
A ƙarshe Ɗantsoho ya yi kira ga gwamnati ta duba halin da ake ciki, "mutane suna cikin matsai saboda yadda kuɗinmu y karye."










