'An tilasta mana barin wuraren kiwon dabbobinmu da muka gada kaka-da-kakanni'

Makiyayi

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Fulani makiyaya a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya, sun yi korafin cewa hukumomin jihar da goyon bayan jami'an sojoji sun tilasta musu barin wuraren kiwon dabbobinsu da suka gada kaka-da-kakanni.

Makiyayan sun kuma yi zargin cewa har yanzu jami'an sojoji na tsare da daruruwa shanunsu.

Wannan korafin na faruwa ne bayan wani rikicin da ya faru a karamar hukumar Karim Lamido tsakanin makiyaya da makwabtansu Bandawa, wadanda galibinsu manoma ne.

Rikicin dai ya tilastawa daruruwan mutane barin muhallansu domin tsira da ransu, inda har ya kai ga kone-konen gidaje har ma da gonaki kafin daga bisani a tura jami'an tsaron sojoji domin su kwantar da tarzomar.

To amma kuma bayan kwantawar rikicin Fulani makiyayan sun zargi jami'an sojoji da ci gaba da rike musu daruruwan shanu, inda kuma suka ce an yi musu barazanar su bar wasu wuraren da shekaru aru-aru nan aka san su.

Ahmed Isa Ardo Tashe, shi ne sakataren al'ummar Fulani makiyaya na karamar hukumar Karim-Lamido da ke jihar ta Taraba ya shaida wa BBC cewa,kamar yadda aka sani Saniya dabbace wadda tana shiga gonakin mutane ba tare da san ko gonar waye ba, to idan a shiga sai a kamata a tafi da ita, to kuma gonar da saniyarma ke shiga an riga an yi noma rani an kwashe, kuma su manoman da ke wajen mun riga su zama a wajen.

Ya ce,"Yanzu sojoji sun je wajen sun ce lallai sai mu tashi mu matsa gefe mu bar wajen wasu kabilu da ake kiransu Mugga,bayan a wajen mu na da gonaki muna da filaye da muka siya sannan ga rugoginmu a wajen,to ya ake muyi?".

"Yanzu sojoji na Mugga da Bandawa suna kuma barin kabilun wajen na daukar makamai suna samun yara makiyaya a daji suna harbesu da kuma kashe musu shanu." In ji shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ahmed Isa Ardo Tashe,ya ce,"Kullum muna fadakarwa a kan a samu zaman lafiya domini dan babu zaman lafiya ta ina Bafullatani zai je ya yi kiwo?.''

To said ai kuma bangaren manoma da makiyayan ke zargi da kashe musu shanu tare da kai musu hari ya mayar da martini, inda mai magana da kabilawar Bandawa Abdul'Aziz Bilyaminu, ya shaidawa BBC cewa babu kamshin gaskiya a wadannan zarge zargen.

Ya ce,"Akwai wajen da daji ne ya kai nisan mil takwas ba a komai a wajen sai aka ce idan damuna ta yi a bar bangaren da ake noma ayi noma kada aje ayi kiwo a wajen, sannan bangaren da ake kiwo kuma kada aje ayi noma kuma an dauki wannan matakin ne saboda kada manomi ya ce an shigar masa gona an masa barna hakan zai kawo zaman lafiya."

Abdul'Aziz Bilyaminu, ya ce," Maganar da suke an kama musu dabbobi, sun karya yarjejeniya ne shi yasa domin sun shiga inda aka ce kada su shiga shi ya sa jami'an tsaron dake wajen wadanda aka kai domin su kwantar da rikici a yankin ke kama duk wata dabba da suka gani ta shiga inda aka hana,sannan kuma tun da rikici ya kunno kai babu wani mutumin Banda da ke fita ya je inda aka haramta masa zuwa, don haka mu yaranmu ba sa harbe kowa ballantana su kashe musu dabbobi."

An dai jima ana fama da rikicin manoma da makiyaya a jihar ta Taraba musamman a kananan hukumomin Karim-Lamido da Lau da Wukari da Bali da kuma Gassol, wanda kan auku samakon wuraren kiwon dabbobi, abin da kuma ya sha sanadin salwantar rayuka da dama.