Halin da ake ciki bayan kashe-kashen ƙabilanci a Taraba

Gwamnan Taraba Agbu Kefas

Asalin hoton, Taraba State Government

Bayanan hoto, Gwamnan Taraba Agbu Kefas ya nemi sarakuna da shugabannin mazaɓu su ba da haɗin kai wajen dawo da doka da oda

Shaidu daga Karim Lamiɗo cikin jihar Taraba a yankin arewa maso gabashin Najeriya sun ce ƙura ta fara lafawa da safiyar yau bayan hukumomin sun ƙaƙaba dokar hana fita, sanadin wani ƙazamin rikicin ƙabilanci.

Ana fargabar rikicin ya yi sanadin mutuwar gomman mutane.

Jihar Taraba ta yi ƙaurin suna a kan rikice-rikicen ƙabilanci da na addini, abin da kan rura wutar zaman gaba da rashin yarda tsakanin ƙabilun da ke zargin juna.

Kusan mako ɗaya kenan ƙabilun Karimjo da Wurkum suna kai wa juna hare-hare, inda wasu rahotanni da ba a tabbatar ba ke cewa an kashe kusan mutum 50.

Gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa'a 24, yayin da rundunar 'yan sandan Taraba ta ce ba ta da tabbaci game da adadin mutanen da lamarin ya ritsa da su.

Wani mazaunin unguwar Step 1 a cikin Karim Lamiɗo ya faɗa wa BBC cewa lamarin ya shafi ƙauyuka da yawa, kuma an yi ƙone-ƙone da kuma kashe-kashe.

"Yanzu kam muna gida, ba shiga ba fita. Kowa yana gida," in ji shi.

Karim Lamido na da nisan kilomita 232 daga Jalingo babban birnin jihar, wadda ke fuskantar yawan rikicin ƙabilanci dahare-haren 'yan bindiga.

"An saka dokar hana fita ne da zimmar dawo da doka da oda da kuma kare rayukan mazauna garin Karim da kewaye," kamar yadda kakakin gwamnatin jihar Yusuf Sanda ya bayyana a cikin wata sanarwa.

A watan Mayun da ya wuce, rikicin ƙabilanci tsakanin ƙabilun biyu ya yi sanadin kashe aƙalla mutum 20 a ƙaramar hukumar ta Karim Lamido.

Tashin hankalin na watan Mayu ya samo asali ne daga rikicin sarauta a yankin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta ce faɗa ya lafa, kuma ba a samu rahoton ci gaba da rikici a wayewar garin Litinin ba.

"Zuwa a yanzu kwamshinan 'yan sandan Taraba CP Yusuf Mamuda Sama'ila yana bibiyar abin da ke faruwa a garin, bayan kafa dokar hana fita, sannan ba a samu sake tashin rikici ba," in ji mai magana da yawun 'yan sandan Taraba.

SP Usman Abdullahi Jada ya ce 'yan sanda sun kama matasan da ake zargi suna da hannu a rikicin. A cewarsa, wasu a ciki sun je kwasar 'ganima' ne, sannan an kama wasu da ake zargin da hannu a kashe-kashe, yayin da aka kama wasu bisa zargin cinna wuta a gidaje.

Ya ce wasu ma bincike ya tabbatar da hannunsu a rikicin, har ma an gabatar da su gaban kotu, kuma tuni kotu tana bin kadin ƙararrakin.

A cewarsa, bayan rikicin farko da na biyu a makon da ya wuce, 'yan sanda sun kama aƙalla mutum goma sha biyar zuwa sha shida.

"Amma na Asabar ɗin nan, ba wanda aka kama tukunna," in ji Usman Jada. "Ana ƙoƙari a ga mutane sun koma hayyacinsu".

Musabbabin rikicin

Wannan dai ya danganta da wanda aka tambaya, yayin da ƙabilun biyu ke zargin juna da fara kai hari tun daga farkon makon jiya.

Shugaban wata ƙungiyar 'yan ƙabilar Karimjo ta ƙasa, Kennedy James ya ce abin ya fara ne bayan wasu da ya kira ɓarayi sun sace shanu a garin Sarkin Kudu.

"Muna gida muka ji labarin cewa wasu ɓarayi sun shiga Sarkin Kudu inda suka sace shanu. Mutanen gari sun bi su amma ba su iya kama su ba," a cewarsa.

Ya ƙara da cewa: "To a kan hanyarsu ta komawa sai suka dinga ƙona ƙauyukanmu da ke kan hanya."

A cewarsa, an samu asarar rayuka tare da dukiyoyin mutane masu yawa.

Sai dai Mallam Iliyasu Idris Ajiyan Wurkum ya musanta zargin, yana mai cewa wasu matasan Karimjo ne suka fara far wa wani ƙauye ɗauke da makamai.

"Da misalin ƙarfe 3:00 na daren 1 ga watan nan [Yuli] wasu matasan da muke zaton na Karimjo ne suka auka wa wani ƙauye suna harbe-harbe," in ji shi.

A gefe guda kuma, 'yan ƙabilar Karim sun musanta cewa su ne suka fara kai harin saboda akwai yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu.