Mambilla: Yadda ake rayuwa a yankin da ya fi ko ina sanyi a Najeriya

- Marubuci, Salihu Adamu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
An yi imanin cewa tsaunin Mambila shi ne wuri mafi sanyi a duk fadin Najeriya.
A tsaunin da wuya ake amfani da na'urorin bayar da sanyi kamar su firji da fanka da na'urar sanyaya ɗaki saboda ba a buƙatarsu.
Akasarin yara da ke tasowa a yankin ba su taɓa ganin na'urorin da ke bayar da sanyi a zahiri ba sai dai a talabijin ko kuma litattafai.
Ko da yake babu wani bayani a hukumance da BBC ta samo da ke tabbatar da cewa tsaunin ne mafi sanyi a kasar, amma wadanda suka yi rayuwa shekaru aru-aru sun shaida wa BBC cewa a lokutan damuna ana zabga sanyin da makinsa ke kaiwa -1 a ma'aunin selshiyos.
Sannan yayin ziyarar wakilin BBC garin Salihu Adamu Usman garin Gembu a ranar hudu ga watan Satumban shekarar 2021, yanayin sanyi ya kai maki 17 digiri selshiyos.

Shi ma shafin da ke wallafa bayanai na intanet Wikipedia ya tabbatar cewa ƙauyen Dorofi da ke kan tsaunin na Mambila shi ne yanki mafi sanyi a Najeriya.
Da zarar ka fara haurawa kan tsaunin daga wani ƙauye da ake kira Mayo Selbe da ke karamar hukumar Gashaka za ka hangi tsauni mai tudun gaske lulluɓe da koren ciyayi da bishiyoyi da hazon ƙanƙara iya hangenka.
Daga wannan ƙauyen ne yanayi ke sauyawa daga zafi zuwa sanyi ko kuma sanyi zuwa ɗan karen sanyi.
Kana isa kan tsaunin daga garin Maisamari har zuwa sauran ƙauyuka da suka yi iyaka da jamhuriyar Kamaru za ka iske kusan kowa ya yi shigar maganin sanyi.
Za ka ga mutane da manyan rigunan sanyi da ake kira "Kuntu" da hulunan sanyi da takalma sau ciki domin maganin sanyi.
A wasu lokutan cikin damuna idan motoci na tafiya hazon ƙanƙara na tilasta musu tsayawa har sai ya ragu kafin su wuce.
Wasu lokuta ko da rana ne sai an yi amfani da fitila domin samun haske.

Da zarar baƙo ya zo da shayi ake marabtarsa maimakon ruwan sanyi kamar yadda aka saba a wasu sassan Najeriya.
Wani dan asalin tsaunin Mambila Hammadu Dan'ndes ya ce tun da ya fara karatun firamare har ya gama bai taba ganin fanka ko firji ko na'urar sanyaya daki ta AC ba a rayuwarsa.
"Maganar gaskiya babu na'urorin bayar da sanyi a tsaunin Mambila musamman a shekarun baya, gwamma yanzu da aka yi banki a can wasu yara ke samun damar ganin na'urar AC.
Karon farko da naga fanka shi ne lokacin da wani ɗan uwanmu ya yi rashin lafiya ina makarantar sakandare sai aka kwantar da shi a asibiti, da muka je duba lafiyarsa, a cikin dakin akwai fanka, wuta na dawowa sai na ji wani abu ya fara kara yanata bada iska sai da na razana".
Ya ce a karon farko da ya fara barin tsaunin Mambila zuwa Yola sai da ya yanke shawarar ya koma gida saboda irin zafi da yaji.
"Cewa na yi babu a bunda zai tilasta min zama a gangare domin kuwa har rashin lafiya sai da na yi hatta hannuna sai da na gagara dagawa" in ji Dan'ndes.
Ya kara da cewa "zafi da na ji na dauka tashin duniya ce, domin kuwa ko yanzu idan na je wani waje na yi ta rashin lafiya da zarar na koma Gembu sai in ji na warke.
"A karon farko a Yola na fara zama da na ga mutane suna shan ruwan sanyi har mamaki abin ya ba ni, sannan kuma lokacin zafi sai na yi wanka kamar sau goma a rana".

Shi ma wani mazaunin Gembu Hussaini Abdullahi ya ce idan har aka haifi mutum kuma ya tashi a tsaunin Mambila ba ya damuwa da sanyin wajen.
"Idan ka tashi a nan tun kana yaro za ka saba, don haka sanyin ba zai dameka ba, amma idan baƙo yazo to sai ya ba da labari".
Abdullahi ya ce ba zai iya zama a wurare masu sanyi ba.
"Kai! Bazan iya zama a Sokoto ko Yola ko Maiduguri ba, saboda akwai zafi sosai, sai dai in je in dawo, kasan kowa da inda ya saba, idan na je garuruwa da ake zafi dole sai na yi ta rashin lafiya har sai na je asibiti".
Sharhi

Tsaunin Mambila wuri ne da ke cike da ni'imomi kama daga yadda zaka hangi tsaunuka lullube da koren ciyayi shar da bishiyoyi gwanin sha'awa, sannan ga kayan marmari ga zuma da shanu ga madara da kuma ganyen shayi da ake nomawa a yankin da dai sauran ababen nishadi.
Idan da gwamnatoci zasu maida hankali wajen zuba jari da kuma gyara tsaunin Mambila, to babu shakka zai zamto wurin yawon bude ido da shakatawa inda za a rika zuwa daga sassan Najeriya daban-daban da kuma kasashen ketare domin kasha ƙwarƙwatar ido.
Hakan kuma zai ƙarawa gwamnati samun kudin shiga musamman a irin wannan lokaci da ake lalubo wasu hanyoyin samun kudi mai makon dogaro ga man fetur kacokan.











