An kaddamar da katafariyar Rugar makiyaya a jihar Borno

Asalin hoton, Abdulrahman Ahmed Bundi
Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta kaddamar da wata katafariyar Ruga da ta samar ga makiyayan jihar, a wani mataki na bunkasa harkar kiwo, da kuma kawo karshen rikici tsakanin makiyaya da manoma a yankin.
Tun zamanin gwamnatin tsohon shugabna Najeriya Muhammadu Buhari, ne dai aka bijiro da wannan shiri na samar da Ruga ga makiyaya a daukacin jihohin kasar baki daya, sai dai a jihohi da dama ta gamu da turjiya.
Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association wato MACBAN, Alhaji Baba Usman Ngalzelma, wanda ya halarci bikin kaddamar Rugar da aka yi a ranar Asabar 11 ga watan Janairun 2025, ya shaida wa BBC Hausa cewa, an kaddamar da Rugar ne a kauyen Garam-Nam da ke karamar hukumar Mafa a jihar ta Borno.
Ya ce, Rugar na da nisan kilomita 10 inda kuma a cikinta aka yi gine-gine na wajen zaman makiyaya, da samar da wajen kiwo da na noman ciyawa ga dabbobi da kuma shanun makiyayan, da wajen bayin dabbobi da wajen shan ruwa da asibitin kula da dabbobi da wajen koyar da makiyayan yadda zasu koyi kiwo na zamani da wajen sarrafa madara da dai dukkan wuraren da suka kamata wanda makiyayan zasu bukata.

Asalin hoton, Abdulrahman Ahmed Bundi
Alhaji Baba Usman Ngalzelma, ya ce,"Baya ga wadannan wurare da aka samar ga makiyayan, an kuma basu shanu bibbiyu da buhun shinkafa dama tallafin kudi."
Shugaban na Miyetti Allah Cattle Breeders Association, ya ce makiyayan da matsalar tsaro ta shafa a jihar ne suka fara amfana da wannan Rugar, dominan basu muhalli ga shanu har ma da tallafin abinci ga kuma wajen noma.
Ya ce," Da wannan Ruga da gwamnatin jihar ta Borno ta samar, an fara daukar matakan shawo kan matsalolin da makiyaya ke fuskanta musamman abin da ya shafi rikicin makiyaya da manoma a jihar."
Ya ce, a yanzu ita gwamnatin tarayya ta bawa harkar kiwo muhimmanci da kuma kulawar data dace sabanin abubuwan da ke faruwa ada inda aka mayar da hankali akan harkar noma aka yi birin da bangaren kiwo.
Alhaji Baba Usman Ngalzelma, ya ce a yanzu jihar Borno ita kadai ce ta samar da Ruga.
Rikici tsakanin makiyaya da manoma a Najeriya ba sabon abune inda a wasu lokuta ma har rasa rai akeyi, wannan ne ya sa shugaba Bola Tinubu ya yanke shawarar kafa ma'aikatar kula da habaka kiwon dabbobi ta kasa.
Shugaban ya ce yana fatan ɓullo da sabuwar ma'aikatar zai kawo ƙarshen rikice-rikicen da aka kwashe shekaru ana samu tsakanin manoma da makiyaya.











