Abotar Bayahude da Bafalasɗine ta kawo zaman lafiya Gaza

Shekarunsu ɗaya sannan suna jin harshe guda, wanda ba Larabci ba, ba Hebrew ba, ba kuma Turanci ba. Wani abu da ya zarta kalmomi, mutuntawar da ta zarta yaren kowace ƙabila.

Ahmed, Bafalasɗine da Yuval, ɗan Isra'ila. Duka shekarunsa 29. Matansa biyu sun ƙware wajen iya magana, marubuta ne da suka yadda bayyana abubuwa kamar yadda suka gansu.

Ahmed na zaune a yankin Zirin Gaza da ya ƙunshi mutum miliyan biyu, yayin da abokin nasa Yuval ke zaune a ɗaya ɓangaren da ke yankin Birnin Kudus, mahaifansa Yahudawa ne masu matsakaicin samu.

Labarai ne sadaniyyar haɗuwar abokan biyu. Yuval ne ya fara karanta wani labari da Ahmed ya rubuta kan halin da Falasdinawa mazauna Gaza ke ciki a wani shafin intanet, daga nan ne ya yi ƙoƙarin samunsa kan hakan, Me zai faru idan da ya samu wani Bahayude ya fassara masa labaran zuwa harshen Heberw?.

"Mun tattauna na tsawon sa'a guda, kuma ta yi daɗi," in ji Yuval.

"Bayan ƙare tattaunawar tamu, sai ya ce min 'Bai taɓa yin magana da wani Bahayude ba a rayuwarsa'. Sai ya ce ina da wasu tambayoyi idan ba za ka damu ba?' Daga mai tambaya na koma wanda ake tambaya. Mun yi magana a waya na tsawon sa'o'i.".

Tare suka kafa wani shafi a Facebook da suka sanya wa suna 'Across the Wall'. Suna samo wanna sunan ne daga tazarar kilomita 59.5 da ke tsakanin Falasɗinawa da ke Gaza da ƙasar Isara'ila. Isra'ila ce ke lura da shige da ficen da ake yi a Gaza.

Ahmed ya yi ta ƙarfafa giwwar Falasdinawa marubuta, da su riƙa yaɗa ayyukansu. Kusan 'yan Isra'ila 200 ne suka sadaukar su riƙa fassara rubutun zuwa yaren Hebrew.

Abubuwan da suka riƙa wallafa wa ya janyo zazzafn martani daga 'yan Isra'ila. Yayin da mutanen biyu suka wallafa wani saƙo da ya ce "ku dora wa Hamas laifi kan kura-kuranku''.

"Muna da babban aiki, babban aiki ga iayalanmu da mutanenmu da ke Gaza, wadande ke buƙatar a bayyana halin da suke ciki, waɗanda ke buƙatar wanda za su yi musu adalci," in ji Ahmed.

Gomman shekarun da ake kwashe ana rikici tsakabin ɓangarorin biyu, ya haifar da gomman ƙungiyoyi da ke gwagwarmaryar samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa, kama daga ƙungiyoyi masu zamna kansu da ke adawa da gine-gine a matsugaunan Falasdinawa, da ƙungiyoyin mata da ke kira ga zaman lafiya, zuwa ƙungiyoyin da ke ƙoƙarin kaytata alaƙa tsakanin ƙananan yara Isra'ila da Falasdinawa.

"Ni wani mutum ne da baya son yaƙi, babau abin da nafi so fiye da zaman lafiya da kwanciyar hankali" in ji Ahmed.

A shekarar 2019 Ahmed ya samu damar yin karatu a Landan, daga can ne ya ci gaba da yin rubuta a intanet kan halin da Gaza ke ciki.

Har zuwa wannan lokaci da yaƙi ya tsananta. A ranar 7a ga watan Oktoba ne Hamas ta ƙaddamar da hare-hare kan Isra'ila inda ta kashe mutum 1,400, mafi yawancinsu fararen hula.

Sanna kuma ta yi garkuwa da fiye da mutum 200, wadanda har yanzu ke hannusu. Harin ya jefa mutanenIsra'ila cikin razani da firgici.

Yayin da ta sha alwashin wargaza Hamas, rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta ƙaddamar da hare-hare ta sama babu ƙaƙƙautawa. Daga baya kuma ta fara ta ƙasa.

Ahmed ya riƙa karantawa tare da ganin labaran abubuwan da ke faruwa, lamarin da ya sa ya riƙa tunanin danginsa, da ke tsare a Gaza. 'Yan uwansa sun taru a wani gida guda daya domin tsira da rayukansu.

Ranar 22 ga watan Oktoba, kimanin mako biyu bayan fara yaƙin, wani hari ta sama ya fada gidan, tare da kashe mutum 21 a cikin dangin nasa.

Ya lissafa mutanen da suka mutun kamar haka "mahaifina, 'yan uwana maza biyu da 'yan uwana mata uku, sai 'ya'yan baffanninsa 14 wanɗanda duka ƙananan yara ne 'yan ƙasa da shekara 13".

Shekara uku da suka gabata mahaifiyarsa ta rasu sakamakon cutar kansa. A yanzu dai shi kaɗai ya rage a dangin nasu.

"Matuƙar ba ka cikin irin yanayin da nake ciki, ba za ka taɓa gane irin yanayin da nake ciki ba, bana fatan abin da ya faru da ni, ya faru da wani mutum, ko da kuwa maƙiyina ne," in ji shi.

Cikin wani hoto da ya ɗauka tare da danginsa, Ahmed ya kasance cikin farin ciki, musamman ganin yana tare da 'yan uwansa waɗanda yake wasa da su a kowane lokaci.

A 'yan kwanakin nan Ahmed na cikin tsananin damuwa, ta yadda sai ya sha magunguna zai iya samun baci. "wannan ita ce rayuwar da nake ciki," in ji shi.

A lokacin da Yuval ya ga labarin mutuwar dangin Ahmed, da ya yi matuƙar firgita, domin ya ma kasa sanin wane sako zai rubuta wa abokin nasa.

"A lokacin da na ga labrin na yi kuka, na kwashe tsawon yini guda ina tunani abin da zan rubuta masa, ban ma san me zan ce ba, don haƙuƙurtar da shi", in ji Yuval.

Kwanaki bayan faruwar lamarin, a yanzu Yuval ya fara fargabar cewa watakila ba zai ƙara samun labarin abokin nasa ba.

Kwatsam! sai ya samu saƙon murya daga Ahmed, cikin tattausar muryar da ke cike da tausayi, saƙon godiya ne ga abokin nasa Yuval kan jajen da ya yi masa mutuwar danginsa, sanna ya je yana mutunta shi fiye da yadda yake yi a baya.

Ahmed ya ce Yuvan ba zai taɓa zama matuƙin jirgin Isra'ila da ya jefa bom gidansu, wanda shi ne ya yi sanadiyyar mutuwar dangin nasa.

A lokacin da na haɗu da Yuval a birnin Kudus ya yi ƙoƙarin ƙin yin magana kan abokin nasa, na tambaye shi za su ci gaba da aiki tare a nan gaba?

"Ina tunanin sai dai ka tambaye shi, amma ni daga ɓangare ne za mu ci gaba da aiki tare, kamar yadda na shaida masa, za mu ci gaba, ba za mu daina ba''.

Matsayin da Yuval ya ɗauka ya haifar masa da wasu matsaloli. Ya rasa abokanai saboda kiran bai wa Falasdinawa 'yancin. A wannan lokaci da rikici ya tsananta, yana fuskantar barazana fiye da watannin da suka gabata.

A lokacin da na yi wa Ahmed tambayar zai ci gaba da yin rubuta ga mabiyansa 'yan Isra'ila?

"Ban sani ba ko zan ci gaba da aiki a shafin 'Across the Wall' ko kuma a a, saboda a yanzu bana cikin yanayi mai kyau, Na yi imanin cewa shafin 'Across the Wall' bai yi nasara ba,… manufarmu ita ce kare aukuwar irin wanna yaƙi, amma ba mu yi nasara ba.

"Don haka a yanzu, ban san yadda zan janyo hankalin sauran Falasɗinawa domin su yi rubutu kan Isra'ila, bayan kisan kiyashin da suka yi a Gaza''

Amma ya ce min shi a karan kansa zai ci gaba da rubutunsa.