Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Muna kokarin saye zuciyar Wike da sauran gwamnonin PDP'
Wasu makusanta ɗan takarar shugaban kasa na jam`iyyar APC a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, sun tabbatar wa BBC cewa ya gana da Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike da wasu gwamnonin PDP a shirin da yake yi na samun nasara a babban zaɓen 2023.
Tawagar Gwamna Wike ta kunshi Gwamnan Oyo Seyi Makinde da na Binuwai, Samuel Ortom da na Abiya, Ikpeazu Okezie.
A karshen mako ne rahotanni suka ce gwamnonin sun bar Najeriya daidai lokacin da wutar rikici da rashin haɗin kai ke sake bayyana a babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Alhaji Ibrahim Masari na hannun daman Bola Tinubu ne, wanda a yanzu haka ke birnin Landan, ya faɗa wa BBC cewa ganawar ta mayar da hankali ne kan zaɓen 2023.
A cewarsa, suna da kwarin gwiwar saye zuciyar wadannan gwamnoni da jawo hankalinsu domin yi wa APC aiki.
Masari ya jaddada cewa akwai kyakkyawan zaton za su yi aiki tare da gwamnoni, musamman Wike, wajen lashe zaben APC.
End of Wasu labaran masu alaƙa da za a iya karantawa
Shin Wike zai sauya sheka ne?
BBC ta tambayi Ibrahim Masari idan akwai yiwuwar Wike ya koma APC, inda ya amsa da cewa ba lallai sai mutum ya sauya jam’iyya zai iya taimaka wa wani domin nasarar zabe ba.
“Wannan ba matsala ba ce, domin ba lallai sai ya koma APC ba, abin bukata shi ne Wike cikakken ɗan siyasa ne da ke da iko da gwamnoni da shiyyarsa da jihohi da dama”.
Masari ya kuma ce Wike zai yi mu su amfani sosai a APC.
A cewarsa: "Ba ma fargaba domin abubuwan da muke gani ko yake bayyana a yanzu na tabbatar mana da cewa akwai gwanonin PDP da za su yi mana amfani a zaben 2023."
Alhaji Masari ya kara da cewa "a siyasar zamani ba ka bukatar mutum ya dawo jam’iyyar ka kafin ya taimake ka".
“Muna kan tuntubar sauran gwamnoni”
APC dai ta nuna tana da kwarin gwiwar nasara da samun goyon-bayan wasu daga cikin jiga-jigai a PDP, sai dai da ya ke idan kana da kyau ka kara da wanka yanzu haka suna ci gaba da tuntubar sauron gwamnonin PDP domin nasara a zaɓen 2023, a cewar Masari.
Kafin ganawar Tinubu da wasu gwamnonin na PDP, a ranar 8 ga watan Yuli, wasu gwamnonin APC uku, da suka hada da Kayode Fayemi na Ekiti da Babajide Sanwo-Olu na Legas da Rotimi Akeredolu na Ondo sun ziyarci Wike a kokarin shawo kan sa da neman sulhu.
Kuma PDP ta kafa kwamitin sasanci domin daidaita Wike da ɗan takararsu na shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Tun lokacin da ɗan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar ya zaɓi gwamnan Delta Ifeanyi Okowa maimakon gwamnan na Rivers a matsayin mataimakinsa ne aka fara samun takun-saƙa da Wike da wasu gwamnoni da ke goya masa baya.
Wasu rahotanni dai sun ce gwamnan ya ƙi yarda ya gana da wasu manyan 'yan jam'iyyar PDP da ke da kusanci da Atiku don sasanta su.
Su ma wasu muƙarraban Gwamna Wike da a halin yanzu ke nuna damuwa da halin da ake ciki a jam'iyyar, sun dage kan cewa dole ne Atiku ya ajiye Okowa ya dauki Wike idan yana son a sasanta.