Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za mu tsuguna gaban Gwamna Wike mu ba shi hakuri - Dattawan PDP
Kwamitin amintattu na babbar jam`iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ya ce zai je gaban gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya roƙe shi domin ya ci gaba da zama a jam'iyyar.
Shugaban Kwamitin, Sanata Walid Jibrin, ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da BBC Hausa.
Ya ce Gwamna Wike babban dan jam'iyyar PDP ne da ba za a yi gangancin barinsa ya fita daga jam'iyyar ba.
"Idan ta kama na je wurinsa (Gwamna Wike) na rusuna masa na ba shi hakuri, babu wata damuwa idan za mu samu nasara," in ji Sanata Jibrin.
A cewarsa "A maganganun da ya yi a baya, ya ce shi dan PDP ne, ba zai bar wannan jam'iyyar ba ko ya ci zabe ko bai ci ba. Idan ko haka ne, ya kamata ya yarda da kaddara."
Tun lokacin da dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar ya zabi gwamnan Delta Ifeanyi Okowa maimakon gwamnan na Rivers a matsayin mataimakinsa ne aka fara samun takun-saƙa da Wike da wasu gwamnoni da ke goya masa baya.
Sai dai Sanata Jibrin ya ce suna fata tattaunawar da za su yi da Gwamna Wike za ta zama silar dinke barakar da ke neman raba kan 'yan jam'iyyar.
A halin da ake ciki dai an kafa wani kwamiti mai mutum tara, wanda aka ɗora wa alhakin sasanta ɓangarorin biyu.
A sanarwar da Walid Jibrin ya fitar ranar Lahadi da maraice, ya ce mambobin kwamitin sun haɗa da Atiku Abubakar da gwamnonin PDP na jihohi 13.
Sanata Jibril ya ce mambobin kwamitin za su kai wa Wike ziyara da zarar Atiku da shugaban jam'iyyar PDP Iyorchia Ayu sun koma Najeriya daga hutun da suke yi. Wasu rahotanni dai sun ce gwamnan ya ƙi yarda ya gana da wasu manyan 'yan jam'iyyar PDP da ke da kusanci da Atiku don sasanta su.
End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta
Su ma wasu muƙarraban Gwamna Wike da a halin yanzu ke nuna damuwa da halin da ake ciki a jam'iyyar, sun dage kan cewa dole ne Atiku ya ajiye Okowa ya dauki Wike idan yana son a sasanta.
Manyan jam'iyyar PDP kamar tsohon gwamnan Ekiti Ayodele Fayose, da kuma gwamnan Benue Samuel Ortom, da tsohon gwamnan Plateau Jona Jang na cikin wadanda suka yi Allah-wadai da zaɓar Okowa a matsayin mataimakin Atiku. Akwai 'yan jam'iyyar PDP da dama da ke ganin cewa Wike bai cancanci abun da suke gani a matsayin 'cin kashin' da ake yi masa a jam'iyyar PDP ba, saboda yadda ya tsaya kai da fata a jam'iyyar tun kafa ta ba tare da ya taba sauya sheka ba.
Sai dai a lokaci guda wasu na da ra'ayin cewa ya yi takara da Atiku, har ma ya kalubalance shi a bangarori da dama, don haka ba abun mamaki ba ne idan Atiku ya zabi wanda zai fi sakin jiki ya yi aiki tare da shi.
A can baya an taba samun dambarwa tsakanin shugaban Najeriya da mataimakinsa lokacin Obasanjo da Atiku, abin da ake ganin ya riƙa mayar da hannun agogo baya wajen kawo ci gaba.