Abin da ya sauya shekara ɗaya bayan ƙwace ikon Afghanistan da Taliban ta yi

An gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar ta neman a sake bude makarantun sakandare ga yan mata

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar ta neman a sake bude makarantun sakandare ga yan mata

Shekara daya baya ne Kungiyar Taliban ta mamaye Kabul, babban birnin Afghanistan yayin da sojojin kasashen waje ke gaggawar janye dakarunsu.

Mai magana da yawun Taliban a lokacin, Zabihullah Mujahid ya yi alkawura da dama da gwamnatinsu ke son tabbatarwa.

Ko gwamnatin ta cika alkawuran?

Tsohuwar gwamnatin Taliban, a shekarun 1990, ta dakile 'yancin mata kuma tun bayan da Taliban ta kwace mulki shekarar da ta gabata, an kakaba wa mata jerin takunkumai a Afghanistan.

An bijiro da dokoki kan tufafi da wadanda suke haramta wa mata shiga wuraren jama'a ba tare da muharrami ba.

Cikin watan Maris, an sake bude makarantu domin sabon zangon karatu amma Taliban ta soke wani alkawari da ta yi a baya inda a yanzu, an haramtawa yara mata zuwa makarantun sakandare.

Taliban ta dora alhakin hakan kan rashin malamai mata da bukatar gyara tsarin rarrabe jinsi.

Lamarin ya shafi kimanin dalibai sama da miliyan guda, a cewar Majalisar Dinkin Duniya kuma hakan ya janyo cece-kuce a duniya.

Yara mata dai suna da izinin halartar makarantun Pramare.

Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a Kabul cikin shekarar da ta gabata
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cikin watan Fabrairu ne wasu jami'oin gwamnati suka sake bude makaratu ga dalibai mata da maza.

Amma yawan matan da ke aiki ya ragu tun lokacin da Taliban da karbe ragamar mulki, a cewar Bankin Duniya.

Adadin matan da ke aiki ya karu daga kashi 15 cikin 100 zuwa kashi 22 cikin 100 cikin sama da shekara 10, tsakanin 1998 da 2019.

Sai dai yadda Taliban ke kakaba karin takunkumai kan fitar mata daga gidajensu tun bayan da ta dawo kan mulki, kason matan da ke aiki a Afghanistan ya ragu zuwa kashi 15 cikin 100 a 2021.

Wani rahoton Kungiyar Amnesty International da aka fitar cikin watan Yuli ya ce Taliban ta take hakkokin mata da yara a Afghanistan.

Ta bayyana cin zarafi da azabtarwar da aka yi wa matan da suka shiga zanga-zangar da aka yi don nuna adawa da takunkuman da aka kakaba musu.

A watan Yuni, Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniya ya ba da rahoton tattalin arzikin Afghanistan ya ragu da kimanin kashi 30-40 tun lokacin da Taliban ta hau kan mulki a Agustan bara.

Wani nazari da hukumar da ke sa ido kan tallafin da Amurka ke bayarwa a Afghanistan ya bayyana cewa duk da cewa tallafin kasashe na ci gaba da kwarara kasar, har yanzu tattalin arzikin kasar na "tsaka mai wuya".

Yan Taliban tsaye kan iyakar da ta tsallaka Uzbekistan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yan Taliban tsaye kan iyakar da ta tsallaka Uzbekistan

Dakatar da galibin kungiyoyin agaji na kasashe waje da amfani da asusun ajiyar kudaden waje ya janyo mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar.

Taliban ta nemi kara yawan kudaden shiga da ake samu daga biyan haraji da kara fitar da kwal domin cin ribar tashin farashin kayayyaki a duniya.

Kasafin kudin wata uku da aka sanar cikin watan Janairun bana ya nuna Taliban ta karbi kusan dala miliyan 400 daga kudaden da ta samu daga a gida tsakanin Satumba da Disambar 2021.

Amma kwararru sun nuna damuwa kan rashin gaskiya a yadda aka tattara alkaluman.

Rashin samun tallafin kasashen waje da kalubalen tsaro da matsalolin da suka shafi sauyin yanayi da hauhawar farashin kayayyakin abinci na kara haifar da tabarbarewar yanayin tattalin arzikin kasar.

Skip Karin wasu labaran da za ku so ku karanta and continue readingKarin wasu labaran da za ku so ku karanta

End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta

Alkawarin Taliban na hana noman ganyen opium na nuna tsarin da suka bijiro da shi ya dan samu nasara lokacin mulkinsu na baya sama da shekara 20 da ta gabata.

Ana amfani da ganyen Opium wajen samar da hodar heroin - sannan Afghanistan ta kasance kasar da ke samar da ganyen opium tsawon shekaru.

A Afrilun bana, Taliban ta sanar da haramci kan noman opium.

Babu wata kididdiga kan yadda tsarin tabbatar da dokar ke tafiya duk da rahotanni daga wasu yankunan da ake noman ganyen a Lardin Helmand da ke Kudancin kasar na nuna Taliban na tilastawa manoma su lalata gonakinsu.

Noman ganyen opium ya karu a 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Noman ganyen opium ya karu a 2021

Wani rahoto da aka fitar a hukumance cikin watan Yuli a Amurka ya nuna cewa duk da Taliban ta yi kasassabar rasa goyon baya daga manoma da wasu da ke da hannu a cinikin ganyen opium din, da alama sun tsaya kai da fata kan tabbatar da dokar haramta miyagun kwayoyi.

Sai dai Dakta David Mansfield, wani kwararre kan tattalin magunguna a Afghanistan ya bayyana cewa akwai yiwuwar a iya kammala noman ganyen zuwa lokacin da aka kakaba haramcin.

"Amfanin gona na biyu da ake nomawa a shekara a Kudu maso Yammacin Afghanistan karami ne ...don haka illarsa ... da ba zai yi wani tasiri ba," in ji Dakta Masnfield.

Yana da muhimmanci a san cewa sarrafawa da samar da sauran magunguna kamar crystal meth, na ci gaba da karuwa duk da Taliban ta haramta ganyen ephedra da ake amfani da shi wajen hada su.

Duk da cewa an daina rikicin da ya bai wa Taliban ikon kwace mulki, akwai farar hula sama da 2,000 da lamarin ya shafa (mutum 700 sun mutu, 1,400 sun ji rauni) da aka ba da rahotonsu tsakanin Agustan bara zuwa tsakiyar watan Yunin bana, a cewar kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.

Sai dai wadan nan alkaluma sun ragu sosai a shekarun da suka wuce lokacin da yakin ke kololuwa.

An alakanta halin da kusan kashi 50 cikin dari na wadanda lamarin suka shiga ga yyukan Kngiyar IS-Khorasan (IS-K) wani reshen IS da ke ci gaba da gudanar da harkokinta a Afghanistan.

A watannin baya-bayan nan, kungiyar IS-K ta kai hare-hare da dama kan farar hula musamman a yankunan da yan Shi'a da sauran tsirarun al'umma ke zama.

,

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mutum na jimami bayan harin da aka kai kan masallacin yan Shi'a a Kandahar a Octoban bara

Kasancewar wasu kungiyoyi masu adawa da Taliban kamar National Resistance Front (NRF) da Afghanistan Freedom Front (AFF), suma sun kara habaka.

Halin tsaro na ci gaba da zama cikin yanayi na rashin tabbas, a cewar MDD a watan Yuni, inda ta ba da misali da kasancewar kimanin wasu kungiyoyin mayaka da ke adawa da Taliban wadanda kuma suke ayyukansu a kasar.

An kuma samu karuwar take hakkokin bil adama har da kashe-kashe da tsare mutane da azabtarwa da Taliban ke yi, kamar yadda MDD ta bayyana.

Tsakanin Agustan 2021 da Yunin 2022, MDD ta ce an kashe kimanin tsaffin jami'an gwamnati da jami'an tsaro 160.