Taliban: Matan Afghanistan da ke ganin Taliban na takura musu saka su sa nikabi

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Lara Owen
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC 100 Women
Lokacin da Soraya ta fita zuwa kanti kamar yadda ta saba a birnin Kabul a makon nan, yanayin ya sauya.
Wakilan gwamnatin Taliban mai mulkin Afghanistan na ciki, inda suke sa ido kan abubuwan da mata masu shaguna ke sayarwa da kuma ko tsayin tufafin ya kai yadda hukumomi ke buƙata.
"Na firgita," a cewar Soraya.
A ranar 7 ga watan Mayu ne fuskokin mata a Afghanistan suka fuskanci sabuwar dokar Taliban bayan sun sanar cewa dole ne mata su saka niƙabi a bainar jama'a karon farko cikin shekaru da dama.
Jami'an Taliban sun bayyana dokar da cewa shawara ce amma sun saka wasu dokoki kan duk wanda ya ƙi bin dokar.
Soraya mai kasuwancin ƙaramin jari ba ta taɓa tunanin za a tilasta mata ba wata rana wajen saka niƙabi kamar yadda Taliban ta yi a shekarun 1990.
"Abin baƙin ciki ne cewa wasu mutane a kan titi su zo kaina su ce na rufe fuska ta," a in ji ta, tana bayyana abin da ya faru lokacin da ta fita sayayya.
"Hatta telan da na je wajensa sai da ya nemi na rufe fuska ta kafin na yi magana da su."

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan da Taliban ta ƙace mulki a Agusta 2021, sun saka dokoki iri-iri na tauye 'yancin mata - inda aka hana su yin aikin gwamnati, da zuwa makarantun sakandare da kuma hana su yin tafiya fiye da kilomita 45 ba tare da muharrami ba namiji.
"Abin ya zama kusan kamar laifi ne mutum ya zama mace a Afghanistan," a cewar Sana, wadda ta rasa aikinta bayan Taliban ta hau mulki.
"Ko ma me suka ce mu saka na tufafi - ba zan fita daga gidana ba, lamarin abin sace gwiwa ne."
Muharrami namiji ne shugaba
Da ma can akasarin matan Afghanistan na saka tufafi mai kama da hijabi, amma dokar yanzu ta buƙaci mata su saka doguwar riga ko kuma niƙabi da zai rufe fuska duka amma ban da ido.
Muharraminsu namiji ne zai dinga saka ido kan tufafin da za su dinga sakawa, ko kuma su za su fuskanci hukunci. Za a iya gayyatarsu don amsa tambayoyin hukuma da kuma ɗaure su idan ta kama.
Wata ƙungiya ta yi zanga-zanga a Kabul a makon nan game da dokar saka kayan gargajiya da aka saka.
"Cikin wata takwas da suka gabata Taliban ba ta yi mana komai ba sai saka mana dokokin tufafi. Akwai matsalolin siyasa da na tattalin arziki amma Taliban ba wannan ne a gabanta ba," in ji Maryam, wata mai zanga-zanga.

Asalin hoton, Rukhshana Media
Wasu 'yan zanga-zanga sun faɗa wa BBC cewa Taliban ta yi yunƙurin hana su gudanar da macin a ranar Talata.
"Sun saka ni tsayawa a wuri ɗaya tsawon awa biyu, suka ƙwace wayata sannan suka yi barazanar kai mu ofishin 'yan sanda," in ji Hajira.
Sashen Afghan na BBC ya tuntuɓi Taliban kan hakan amma ba su samu amsa ba.
Bijirewa a kan tituna
Anoushah, wata mai kare haƙƙin mata a Kabul, ta ce ita ma daga baya ta yanke shawarar ɗaukar mataki.
"Ranar farko da aka saka dokar na fita gari da ɗana mai shekara 12 sanye da kayana kamar yadda na saba, fuskata a buɗe. Na so na je kan wasu 'yan Taliban don na ƙalubalance su."
Sheikba wadda ta ce ba ta bin kowane addini, ta yi alwashin yaƙar duk wani yunƙurin hana ta yin shigar da take so - duk da arangamar da ta yi da hukumomi a kwanan nan.
A kan hanyarta ta zuwa jami'a, 'yan Taliban suka tare ta saboda ba ta saka kayan da suka dace ba.
"Na yi ƙoƙarin na yi masa bayani cewa zafi ya yi yawa, amma da ya matsa dole sai da na rufe fuskata," a cewarta.

Asalin hoton, Getty Images
Dokokin hana tafiye-tafiye
Ba wannan ne kaɗai abin da take fuskanta ba. A kwanan nan aka hana Sheikba shiga jirgi don zuwa karatun kyauta a Iran saboda ba ta tare da wani namiji.
Suka ce matan da ke son yin tafiya mai nisa a mota sai sun zo da namiji za a ƙyale su su shiga mota.
"Na yi yunƙurin na yi musu bayani amma sun ƙi saurare ni."
Kamar ita, Fereshtah ma na fargaba game da makomarta. Mahaifinta ya rasu tun tana shekara ɗaya kuma rashin wani ɗan uwa namiji a gidansu zai iya sakawa a hana ta zirga-zirga.

Asalin hoton, Getty Images
Saƙo daga jami'a
A wannan makon ne Fereshtah ta samu saƙo daga malamanta na jami'a cewa ita da sauran ɗalibai su bi dokar da Taliban ta saka.
"Zan ɗan ƙara rufe fuskar saboda ina da damuwar idan suka zo gidan nan kuma babu namiji a gidan, amma dai ba yadda Taliban ke so ba," a cewarsa.

Asalin hoton, Getty Images
Amma wasu 'yan ajinsu ba haka suka samu lamarin ba.
"Sun faɗa min cewa za su saka cikakken hijabi saboda iyayensu sun gargaɗe su game da abin da ka iya faruwa," in ji Sheikba.
Najma da ta yi digiri a Jami'ar Herat na ganin lokaci ya yi da al'ummar duniya za su matsa wa Taliban lamba game da haƙƙoƙin mata.
"Abin na baƙanta min, ina jin cewa na gaza saboda ba ni da wani zaɓi sama da na yi biyayya ga waɗannan dokokin na banza," a cewarta.
"Ba zan iya siffanta rashin kyawun yanayi nan ba, suna matsa mana mata da yara, suna ƙuntace mu a keji."












