'Ban san inda mijina da 'yan uwana suke ba bayan barayin daji sun kai mana hari a Gummi'

Daruruwan ‘yan gudun hijirar da suka tserewa hare-haren ‘yan fashin daji daga ƙauyukansu zuwa garin Gummi na jihar Zamfara da ke Najeriya na fuskantar ƙalubale iri daban-daban da matsin rayuwa.

‘Yan gudun hijirar, waɗanda aka tsugunar a makarantun gwamnati, sun ce suna cikin tsananin buƙatar tallafin makwanci da abinci da kuma magunguna.

Gwamnati Zamfara dai ta ce tana bakin iyakar ƙoƙari don tallafa wa dubban ‘yan gudun hijirar da ke sassan jihar.

Wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar da BBC Hausa ta tattauna da su ta waya sun shaida mana cewa suna cikin tashin hankali ga kuma lokaci na damuna.

‘Yan gudun hijirar sun kwarara zuwa cikin garin Gummi ne daga kauyuka fiye da ashirin, ciki har da Gwalli da Ranke da Gidan Illo da kuma Zugu a karamar hukumar Bukuyum.

Muna bidar taimako

Wannan mutumin ya ce ba su da wurin kwana ga kuma rashin abinci.

"Ba a gidaje muka kwana ba, don babu wani wanda haka dai zai amince ka kwana gidan shi. Wasu na kwana tasha, wasu cikin firamare, wasu ba mu ma san inda suke kwana ba. Har da ma inda ba ka zata ba, babu inda ba ka ganin mu."

Ya kuma ce al'amari ne wanda haka kawai mutum ba zai yarda ba har sai ya gani da idonsa.

Ita kuwa wata mata ta ce ba ta san inda maigidanta da sauran ‘yan uwanta suka shiga ba, tun bayan da ‘yan fashin daji suka tarwatsa kauyensu.

"Wallahi tashin hankali ne, barayi na koro mu daga Zugu mun ka zo Gummi. Gaskiya muna cikin matsiyacin hali domin ko abincin da za mu ci bamu da ballantana magani in 'yan uwanmu ba su da lafiya. Yanzu haka wani bai da lafiya, sai dai mu yi bara domin mu ba shi magani."

Ta ce ba ta san inda mai gidanta da 'yan uwanta suke ba, "Mu ma nan halin bidarsu muke ciki."

Ta kuma ce cikin makarantar sakandare suke kwana, kuma wurin kwanciyar maras kyau ne saboda yawan sauro da sanyi da karancin abinci.

Kananan hukumomin Gummi da Anka da Bukuyum na da daruruwan ‘yan gudun hijira maza da mata da kananan yara, wadanda ke matukar bukatar tallafin kayan abinci da wurin kwana da magunguna musamman a wannan lokaci na damina.

Gwamnatin jihar Zamfara dai ta ce ta aika tawagar jami’an gwamnati zuwa yankin, karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Sen. Hassan Muhammad Nasiha.

"Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya umarce mu da mu kai agaji, sannan mu ga abin da ke faruwa. Kuma na je dukkan masarautu na Anka da Bukuyum da Gummi inda aka gwada min 'yan gudun hijirar da ke can kuma na yi musu jawabai," in ji shi.

Ya ce ya mika wa 'yan gudun hijirar tireloli biyu-biyu na abinci da naira miliyan biyar-biyar a kowace karamar hukuma.

Ko me gwamatin Zamfara ta ke yi game da matsalar tsaron da ta raba su da muhallansu?

Sanata Hassan Muhammad Nasiha: "Sha'ani na tsaro sha'ani ne na sirri. Idan Allah ya yarda, yadda ka ji sauran bangarora sun yi shiru, haka ma shi wannan bangaren ana nan ana daukar mai mataki in Allah ya so."

A baya-bayan nan ne, mataimakin gwamnan ya ziyarci yankin na Gummi har ma yace an ba su tallafi, amma ga alama ‘yan gudun hijirar na bukatar kari saboda yawansu da kuma halin da suke ciki, kuma hakan na nuna cewa tilas sai gwamnati ta yi da gaske don fitar da dumbin mutanen da matsalar tsaron ta raba su da harkokinsu na yau da kullum.