Hotunan 'yan Mozambique da suka bijire wa 'yan bindiga suna zuwa makaranta

Wasu daga cikin 'yan achaba da ke Pemba, wadanda ke harkokinsu a kan titunan birnin da ke da tashoshin jiragen ruwa a kasar Mozambique, sun tsere daga hare-haren masu ikirarin jihadi - inda suka tafi yankin arewa mai nisa domin guje wa rashin tsaron da ke addabar garinsu na Mocímboa da Praia.

Sai dai wadannan 'yan achaba, wadanda yawancinsu matasa ne, na kallonta a matsayin hanyar samun abincinsu, duk da nisan fiye da kilomita 325 da suka yi daba gida. Pelé Bambina, mai shekara 20, yakan dauki fasinjoji a babur dinsa a yayin da ya dan samu hutu tsakanin darussa daga makaranta.

An tilasta rufe makarantu a Mocímboa saboda rikicin 'yan bindiga, wanda aka soma a watan Oktoban 2017.

Masu ikirarin jihadi sun lalata manyan makarantun firamare da sakandare yayin hare-haren da suka ta'azzara a shekaru biyu da suka wuce, abin da ya tilasta wa Pelé ya bar garin.

"Na zo nan a cikin kwale-kwale a watan Yunin 2020. Daga lokacin da aka soma yakin, na daina samun kwanciyar hankali. Al'amura sun tabarbare, " in ji shi.

Shi da iyalansa duka Musulmai ne - kamar akasarin mutanen da ke lardin Cabo Delgado - amma hakan bai hana kai musu hari ba.

An sace daya daga cikin 'yan uwan Pelé kuma har yanzu ba a ganshi ba, yayin da aka yi wa biyu daga cikin 'yan uwansa mata fyade.

Pemba, babban birnin lardin Cabo Delgado, bai fuskanci hare-haren 'yan bindigar ba - amma ya kasance mafakar dubban mutanen da suka tserewa hare-harensu.

Yanzu Pelé yana aiki tare da wasu 'yan achaba da ke sana'arsu a yankin Emulação da ke Pemba, inda masu baburan hawa suka yi cincirindo.

'Yan achabar kan yi wasan karta a kan wayoyinsu, yayin da suke jiran fasinjoji. Dukkan wadannan matasa, masu shekaru ashirin da wani abu, 'yan asalin Mocímboa ne.

"Ni ne mutum na farko dan gidanmu da na bar garinmu. Na zo nan da kaina," a cewar Pelé.

Lokacin da ya iso nan, Pelé ya sha wahala wurin samun abin sanyawa a baki kuma ya sha alwashin kammala karatunsa.

"Na soma aiki a wurin aski, amma sai karshen wata ake biyana. Ina bukatar kudin da zan ci abinci, sannan na samu abin da zan je makaranta."

Kazalika ya yi kokarin sayar da abinci da kayan taba-ka-lashe sai dai ba su da riba sosai.

Matarsa ta bi shi garin wata biyu bayan zuwansa, sai dai sun yi matukar shan wahala.

Shekara daya bayan zuwansu abubuwa sun inganta: "Wata rana ina zaune a nan na zo wurin abokina sai wani mutum ya tambaye ni ko zan iya tuka babur, nan take na ce masa zan iya."