Waɗanne rigakafi ake iya yi wa mai ciki da waɗanda ba a yi musu?

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Garkuwar jikin mace na raguwa a lokacin da take da juna biyu, kuma hakan na sa ta saurin kamuwa da ƙwayoyin cuta.

Sai dai rigakafi na taimakawa wajen kare mai juna biyu da ɗantayinta daga cututtukan da ake iya kaucewa.

Idan mai ciki ta samu rigakafin, tana bai wa jaririnta sojojin jiki da ke yaƙi da ƙwayoyin cuta.

Shafin intanet na ma'aikatar kiwon lafiya da ayyukan al'umma na gwamnatin Amurka ne ya wallafa haka, kan rigakafi ga mace mai juna biyu.

Bayanan sun ƙara da cewa sojojin jikin da uwa ta baiwa jaririnta a ciki, suna kuma samar da garkuwa ga jaririn, a tsawon wasu watanninsa na farko a duniya.

A cewar shafin rigakafin na kuma bayar da kariya ga ita kanta mace mai juna biyu a tsawon lokacin goyon ciki, don haka yana da muhimmanci mace ta san irin rigakafin da ya dace a yi mata a lokacin juna biyu.

Wata likitar mata wadda ke aiki da asibitin koyarwa na gwamnatin Najeriya da ke jihar Gombe, Dokta Aishatu Musa Hari ta ce, rigakafi na da muhimmanci wajen kare yaɗuwar cuta daga uwa zuwa jaririnta a lokacin goyon ciki ko haihuwa.

Wasu daga cikin rigakafin da tace suna da kyau ga masu ciki sun haɗa da:

  • Allurar Tt (Tetanus) sau biyar ake yinta: Rigakafi ne da ke bayar da kariya daga cutar da ake samu idan mutum ya ji ciwo kuma ƙasa ya shiga ciwon ko ya taɓa ƙarfe mai tsatsa da sauransu.
  • Rigakafin (Influenza): Cututtukan da ke shafar hanyar numfashi
  • Ciwon hanta (Hepatitis B)
  • Cutar sankarar bakin mahaifa (HPV)
  • Rashin daidaiton jini (Rhesus D): Ana baiwa mata masu cikin da rukunin jininsu (-) amma kuma na mazajensu (+) ne.
..

Asalin hoton, Getty Images

A cewar likitar "Shi yasa idan za kiyi aure yana da kyau ki san nau'in jininki, mijin ya san nau'in jininsa. Idan dukanku (+) ne to babu matsala. Amma idan jininki (-) mijinki (+) ne, kuma ɗan da ke cikinki ya ɗauko jinin babansa to jininki da na yaron ba ɗaya ba ne."

Dokta Aishatu ta ƙara da cewa idan a wannan yanayi jinin mace da na jariri ya gauraya, jikinta zai samar da sojoji waɗanda za su yaƙi duk jini (+) don suna ɗaukarsa baƙon abu.

Kuma a don haka duk cikin da zata samu nan gaba idan jinin jaririn (+) ne jikinta zai yaƙe shi, sai yaran su yi ta mutuwa. Amma idan an yi mata rigakafin yana hana jikinta samar da sojojin.

Wani ƙarin rigakafin da ake wa mai ciki shi ne idan mai juna biyu na fama da cutar sikila.

Rigakafin da ba a yi wa masu ciki

  • BCG
  • Ƙyanda
  • Mumps da rubella, waɗanda ke janyo ƙuraje a jiki.
  • Rigakafin cutar shawara (Yellow fiver)

Likitar ta yi ƙarin haske kan wasu daga cikin dalilan da suka sa ba a yi wa masu juna biyu waɗanan rigakafin.

Babban dalilin a cewarta shi ne suna ɗauke da ƙwayar cuta ko wani sashen ƙwayar cutar mai rai.

"Mata idan suna da ciki garkuwar jikinsu na yin ƙasa ne kuma idan ya yi ƙasa, idan ka sa irin wannan rigakafin da ke da rai, maimakon a samu abin da ake so sai ya cutar da su."

Ta bayyana cewa ƙwayoyin cutar da ake amfani da su wurin yin rigakafin da ake yi wa mata masu juna biyu, an riga an kashe su ko kuma an rage ƙarfinsu ta yadda ba zai iya cutar da mai ciki ba.