Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilai shida da za su sa ku bayar da gudumawar jini
A kowace rana a sassa daban-daban na duniya, mutane da dama ciki har da mata masu haihuwa da suka zubar da jini da yara masu fama da ƙarancin jini, da waɗanda suka gamu da haɗurra na buƙatar jini domin ceto rayuwarsu.
Sai dai, mafi yawan mutane ba sa bayar da jini sai lokacin da wani na kusa da su ke cikin hali na gaggawa. Wasu kuma suna guje wa bayar da jini saboda rashin fahimtar amfanin yin hakan ko kuma rashin tabbas kan me zai faru da su bayan sun bayar.
Amma masana sun tabbatar da cewa, bayar da jini ba wai kawai taimako ne ga wanda ke buƙatar jinin ba, yin hakan alheri ne ga mai bayarwa, kamar yadda wani likitan jini Dr. Yusuf Ibrahim ya bayyana wa BBC.
Likitan ya ce ya kamata mutane su fahimci muhimmancin bayar da jini su kuma riƙa kai kansu asibiti domin su bayar da jini a kai a kai kuma haka nan ba wai sai wani nasu na cikin matsalar buƙatar jinin ba
A cewarsa, jini abu ne da ake buƙatarsa koyaushe a asibitoci saboda mutane da dama na cikin halin da buƙatar shi.
Shin ko kun san amfanin da za ku samu idan kuka bayar da jininku?
Ga wasu daga cikin amfanin bayar da jini da Dr. Yusuf ya lissafo:
Ceton rai
Dr. Yusuf ya ce, "A gaskiya, mutum mai bayar da jini yana taimakawa wajen ceto rayuka da yawa."
Ya ce idan mutum yana zuwa asibiti ya bayar da jini haka nan, bai san iyakan rayukan da yake taimakawa ba.
"Idan aka bai wa mai buƙatar jini jininka, ka taimaka masa da iyalinsa, da ƴan'uwansa da duk wani mutum da yake son shi saboda ka ceci rayuwar shi." in ji Likitan.
"Saboda haka ina karfafa wa mutane gwiwa da su dage su riƙa zuwa asibiti bayar da jini, haka nan ba dole sai wani nasu na buƙata ba," likitan ya ƙara da cewa.
Rage haɗarin kamuwa da cutar zuciya da bugun jini
Likitan ya ce lokacin da mutum ya bayar da jini, yawan ƙarfin sinadarin Iron a jininsa na raguwa.
Idan ƙarfin sinadarin Iron ya yi yawa a cikin jini, yana iya toshe jijiyoyin jini wanda ke haifar da haɗarin bugun zuciya. Saboda haka, bayar da jini a kai a kai yana taimakawa wajen kiyaye lafiyar zuciya da jijiyoyin jini.
A cewar Dr. Yusuf: "Mutanen da ke bayar da jini a kai a kai na da ƙarancin yiwuwar kamuwa da cututtukan zuciya. Domin jininsu ba ya tara sinadarin Iron fiye da kima."
Bayar da jini na sabunta jini a jiki
Dr. Yusuf ta ce lokacin da mutum ya bayar da jini, jikinsa yana fara samar da sabbin ƙwayoyin jini domin maye gurbin waɗanda aka rasa.
Wannan yana sabunta jini da kuma jiki, yana kuma taimakawa wajen inganta zagayowar jini.
Sabon jini yana nufin sabon kuzari, da lafiyar fata, da kuma kyakkyawan yanayin jiki gaba ɗaya in ji likitan.
"Jikin ɗan'adam yana da ikon sabunta kansa. Bayan bayar da jini, cikin kwanaki kaɗan sabbin kwayoyin jini suna dawowa. Wannan yana nufin mai bayarwa yana samun sabon kuzari da lafiya," in ji Dr. Yusuf.
Damar gano matsalolin lafiya tun da wuri
Dr. Yusuf ya ce kafin mutum ya ba da jini, ana duba lafiyarsa gaba ɗaya ta hanyar gwaji da suka haɗa da gwajin yawan jini, hawa da saukar jini, yawan sukari da ke cikin jini, da kuma gwajin cututtuka kamar HIV da ciwon ƙoda da sifilis.
Wannan yana nufin cewa, mai bayar da jini na samun cikakken binciken lafiya kyauta. Idan aka gano wata matsala, zai iya sanin ta da wuri kafin ta tsananta in ji likitan.
Ƙara lafiya, jin dadi, tausayi da kwanciyar hankali
Bayar da jini in ji likitan na nufin taimako ga wani da ke cikin hali na gaggawa.
Wannan aikin alheri yana haifar da farin ciki da kwanciyar hankali.
Masana ilimin halayyar ɗan'adam sun tabbatar da cewa, mutum da ke taimakon wasu yana samun farin ciki a zuciya da kwanciyar hankali wanda hakan ke ƙara lafiya fiye da wanda ba ya taimako.
Dr. Yusuf ya ce: "Wasu daga cikin masu bayar da jini suna cewa, duk lokaci da suka ba da jini suna jin kamar sun ceto rai. Wannan jin daɗin na ƙara musu lafiya kuma yana kara musu ƙarfin gwiwa su ci gaba da bayar da jini lokaci-lokaci."
Rage yawan sinadarin ƙarfi maras amfani
Dr. Yusuf bayyana cewa, yayin da mutum ya bayar da jini, jikinsa yana ƙona sinadaran 'kalori' 600 zuwa 650. Wannan yana taimaka wa masu kiba wajen rage nauyi cikin hanya mai lafiya ba tare da amfani da magani ko daina cin abinci ba.
Duk da haka, dole ne a tabbatar da cewa mai bayarwa yana da lafiya sosai kafin a ba shi damar bayar da jini.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), jinin mutum ɗaya da aka bayar na iya ceton rayuka har uku. Wannan na nuna cewa bayar da jini ba ƙaramin abu ba ne.
A kowace rana a Najeriya, asibitoci na buƙatar jini fiye da abin da ake samu daga masu bayarwa. Idan mutane za su fahimci cewa bayar da jini ba wai kawai taimako ga mai buƙata ba ne kawai, amma kariya ga lafiyar su, da yawa za su fara bayarwa," in ji Dr. Yusuf.