Ranar Hawan Jini ta Duniya: Hanyoyin kauce wa kamuwa da cutar hawan jini

Danna hoton da ke sama domin kallo bidiyon:

Likitoci da masana lafiya sun bayyana hanyoyin kauce wa cutar hawan jini a yayin da ake tunawa da Ranar Hawan Jini ta Duniya.

Kungiyar The World Hypertension League ce ta ware ranar 17 ga watan Mayu kowacce shekara domin tunatarwa kan hatsarin hawan jini da yadda za a kauce wa kamuwa da shi.

Wata kwararriyar likita, Dr Fatimah Maikanti Baru, ta shaida wa BBC cewa "za mu iya kasafta hanyoyi da ake samun hawan jini zuwa gida biyu: da wadanda za a iya canza su da wadanda ba za a yi ba."

Ta kara da cewa: "abubuwan da ba za a iya canza su ba su ne, shekaru - idan mutum ya zarta shekara 65, sai kuma kasancewa namiji da kuma gado."

A cewarta bincike ya nuna cewa bakaken-mutane da masu shan taba suna cikin wadanda suka fi kasadar kamuwa da cutar hawan jini.

Ta bayyana cewa akwai bukatar yawaita motsa jiki domin kauce wa kamuwa da hawan jini.