Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko kun san abubuwan da ke janyo matsalar bugun jini?
Yayin aka ware kowacce ranar 29 ga watan Oktoban a matsayin ranar da za a duba irin kamarin da matsalar bugun jinni da kuma wayar da kai a kan irin illolin da ke tattare da wannan matsala, masana sun yi Karin haske a kan ita kanta cutar da ma abubuwan da ke janyo ta.
Farfesa Balarabe Sani Garko, kwararren likita ne a fannin cutukan da suka shafi zuciya d ahawan jinni da makamantansu a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello, Shika Zaria, ya yi wa BBC Karin haske a kan ita kanta cutar.
Kwararren likitan ya ce, idan aka ce mutum ya gamu da lalurar bugun jinni to ya samu matsala ne da hanyoyin da jini ke bi a jikin dan adam da kuma bangaren kwakwalwa.
Wata kila a samu hanyar jini ta toshe ko kuma hanyar jini ta fashe jini ya hadu da wani abin, wannan shi ake cewa bugun jinni wato a turance stoke, in ji likitan.
Kwararren likitan ya ce, akwai abubuwan da ke janyo ita wannan cuta kamar idan zuciya ta na buga jini ya tafi da karfi, wato kama hawan jini ke nan.
Ya ce,” Baya ga hawan jini da ke janyo wannan cuta, akwai kuma ciwon siga, da a turance ake cewa Diabetes, shi ma yana janyo wannan cuta ta bugun jini.”
Likitan ya ce, idan wasu abubuwa ma suka yi wa mutum yawa a jikinsa kamar kitse, su kan daskare su toshe hanyoyin jini wanda hakan zai jawo matsalar gamuwa da bugun jini.
Farfesa Balarabe Sani Garko, ya ce akwai matakan da ya kamata a dauka don kaucewa kamuwa da cutar bugun jinni kamar kaucewa duk wani abin da aka san zai iya janyo toshewar hanyoyin jini sai kula da su.
Ya ce, kamar misali idan mutum na da lalurar hawan jini, yakamata ya rinka zuwa asibiti ana duba shi da kuma auna shi, haka smai lalurar ciwon siga ma, dole a kula.
Kwararren likitan ya ce, yakamata mutane ma su rinka zuwa asibiti ana duba yawan maiko ko kitsen da ke jikinsu wato Cholestrol don kaucewa kamuwa da cutar bugun jini.
Likitan ya ce, baya ga duba irin wadannan cutuka, yana da kyau mutane su rinka zuwa ana duba kwakwalwarsu da koda dama sauran abubuwa da suka kamata a rinka ana duba lafiyarsu akai-akai a asibiti.
Farfesa Balarabe Garko, ya ce, ita cutar bugun jini ba wai kawai masu shekaru da yawa ta ke kamawa ba, yaro ko matashi ma na iya kamuwa da ita, a don haka dole mutane su kiyaye.