Yadda sauyi zuwa amfani da gas ɗin CNG ke wahalar da wasu ƙasashen Afirka

- Marubuci, Basillioh Rukanga & Alfred Lasteck
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Dar es Salaam
- Lokacin karatu: Minti 4
Sauyin man da mota ke amfani da shi na bunƙasa a Tanzaniya, amma ƙarancin gidajen mai babbar matsala ce.
Kamar Najeriya da sauran ƙasashe a nahiyar, Tanzaniya ma ta fara rungumar amfani da gas na CNG a madadin man fetur da dizel.
Ya fi lafiya ga muhalli fiye da man fetur, amma saboda rahusarsa ne ya sa fiye da masu amfani da mota 5,000 suka koma amfani da CNG a ƙasar da ke gabashin Afrika musamman motocin sufuri.
Gwamnatin ƙasar na son a koma amfani da CNG a ƙasar zuwa tsakiyar ƙarni.
Tanzaniya na da arzikin iskar gas a ƙarƙashin ruwa kuma masu amfani da CNG suna biyan rabin kuɗin da ya kamata su biya na fetur.
Wannan sauƙin ya ja hankalin masu sana'ar tasi kamar Samuel Amos Irube wanda bai ji wahalar kashe miliyan 1.5 na kuɗin ƙasar kwatankwacin dala 620 domin sauya motarsa zuwa amfani da CNG.
Amma a yanzu da dole sai ya buƙaci sake shan mai, yana shafe lokaci mai tsawo yana kan layi a gidan mai kafin ya samu a Dar es Salaam.
Ya ce akwai takaici, inda yakan yi awa aƙalla uku kafin ya sha mai, amma duk da haka ya fi shan fetur inda yake kashi 40 kawai idan ya kwatanta da lokacin da yake shan fetur.
Layin mai ba ya ja sosai a gidan man Ubungo na CNG inda har ya yi tsawo a zuwa hanya.
Medadi Kishungo Ngoma, ya shafe awa biyu yana kan layi da motarsa ga kuma kaya da ya ɗauka.

Ya shaida wa BBC cewa yana cikin mutanen farko da suka sauya motarsu zuwa amfani da CNG.
"Wani lokaci sai mun kira domin a yi mana aiki," in ji shi.
Ya ce babu wadatar kayan da za su wadaci masu buƙata da ke ƙaruwa.
Sadiki Chritian shi Mkumbuka ya shafe awa uku yana jira da babur dinsa mai ƙafa uku da ake kira Bajaji.
"Layin yana da tsayi, a cewarsa, yana mai cewa" ya kamata a ce akwai gidajen shan CNG kamar na fetur.
Amma farashin ne ke sa mutane dawowa.
"Ina biyan shillin 15,000 (dala shida) domin cika kilo 11 na tankin gas ɗina, wanda zan iya tafiyar kilomita 180," a cewar wani da ya bayyana sunansa a matsayin Juma, inda ya ƙara da cewa wannan rabin kuɗin da mutum zai biya ne idan zai sha fetur.

Ƙoƙarin jan hankalin mutane zuwa ga CNG a Tanzaniya bai karɓu ba sama da shekara 10 amma sai a 2018 ya fara karɓuwa.
Waɗanda ke jagorantar sauyin sun ce ba su ga ƙaruwar buƙatar ba.
Aristides Kato manajan kamfani da ke kula da aikin sauya motoci zuwa amfani da CNG a Tanzaniya ya shaida wa BBC cewa "an samu ƙaruwar mabuƙata da dama" a kwanankin nan masu amfani da CNG.
"Mun samu kanmu a yanayi na ƙarancin wuraren samunsa domin magance ƙaruwar masu amfani da gas ɗin," kamar yadda ya bayyana.
Mahukunta na son mutane su ci gaba da komawa zuwa amfani da CNG domin ya fi sauƙi da lafiya ga muhalli wanda ba ya fitar da gurɓatacciyar iska sosai, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Sai dai, manajan kamfanin Masar Taqa Arabia da ke da mallakin gidan mai na CNG kusa da filin jirgin sama, ya ce ƙaruwar buƙatar wata alama ce da ke nuna cewa CNG ya fara bunƙasa a Tanzaniya.
Amr Aboushady ya ce kamfaninsa na son gina wasu gidajen mai da dama kamar irin ci gaban da aka samu a Masar.
Masar ce ta fara amfani da CNG a nahiyar, inda kusan rabin miliyan na ababen hawa na ƙasar suka sauya zuwa ga amfani da tsari biyu na mai tun 1990.
Sauran ƙasashen Afrika da suka amince da amfani da CNG sun haɗa da Afrika ta Kudu da Kenya da Mozambique da Ethiopia.
Hukumomi a Tanzania a shirye suke su samar da gidajen mai tare da fatan jan hankalin kamfanoni masu zaman kansu domin shiga kasuwancin.
An gina babbar cibiyar CNG a Dar es Salaam ta kamfanin ƙasar na TPDC wadda za ta dinga ba sauran ƙananan a sassan ƙasar.











