Dalilai huɗu da ke sa ƴan Najeriya tsoron mayar da motocinsu masu amfani da iskar gas

Asalin hoton, Getty Images
A farkon makon nan rahotanni suka ambato shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya gargaɗar ƴan Najeriya cewa "kodai ku rungumi iskar gas ko kuma ku ci gaba da shan mai a kan naira fiye da 1000 kowacce lita."
Tun dai bayan da gwamnatin ta Tinubu ta sanar da cire tallafin man fetur, a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ƴan Najeriya ke fama da ƙarin farashin man indaya ƙaru da fiye da naira 800 a kan farashin asali.
A yanzu haka ana sayar da litar man tsakanin naira 1,000 zuwa 1,300 a gidajen man ƙasar, wani abu da ya tilasta wa 'yan ƙasar da dama ajiye ababen hawan nasu.
Gwamnatin Najeriya da sauran masana na ta yin kira ga 'yan ƙasar su koma amfani da iskar gas ta CNG, wadda suka ce ta fi araha, da kuma rashin gurɓata muhalli.
To sai dai duk da cewa farashin iskar gas ta CNG na da sauƙi inda ake sayar da ma'aunin SCM guda ɗaya a kan naira 230, wasu batutuwa da alama na sa 'yan ƙasar yin ɗari-ɗari wajen rungumar amfani da iskar gas ɗin.
Shin ko waɗanne dalilai ne?
Aminu Tijjani Auwal, wani ƙwararren masanin harkar iskar gas a Najeriya ya shaida wa BBC cewa dalilan:
Dalilai huɗu da ke tsorata jama'a
- Tsadar juya motoci zuwa masu amfani da gas
Daya daga cikin manyan dalilain da ke hana mutane juya motocin nasu yadda sauyawar ke da matuƙar tsada.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu bayanai da BBC ta gano sun nuna cewa ana aikin mayar da mota mai amfani da iskar gas ta CNG tsakanin naira 750,000 zuwa 1,000,000.
Ko shakka babu wanann ba ƙaramin kuɗi ba ne, musamman a wannan yanayi da ke ciki na tsadar rayuwa da matsin tattali arziki.
- Rashin wadatar wurin shan iskar gas ɗin
Wani abu da ke ƙara sanya mutane fargaba da tsari shi ne rashin wadatuwar wuraren da za a sha iskar gas ɗin.
Bayanai sun nuna cewa duk girman Abuja, babban birnin ƙasar - da ke kan gaba a wuraren da suka fi zirga-zirgar ababen hawa - wurare ba su guda biyar na shan iskar CNG, ballantana kuma a sauran jihohin ƙasar.
Don haka idan har mutum yana son shan gas ɗin, to dole sai ya bi dogon layin da watakila zai shafe sa'o'i masu yawa a kan layi irin wanda ake yi wajen shan mai.
- Tsoratarwar da ake yi cewa tukunyar na fashewa
Wasu bayanai da bidiyoyin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta na iƙirarin fashewar motocin da ake sauya wa fasalin.
Wannan na daga cikin abubuwan da ke ƙara jefa fargaba a zukatan masu ababen hawa cewa ka da suna tafiya tukunyar ta fashe motar ta kama da wuta.
- Rashin wayar da kai
Wani abu da ya sa mutane ke ɗari-ɗarin amfani da batun shi ne rashin gangamin wayar da kai daga ɓangaren hukumomin da ke da alhakin yin hakan.
Mutane da dama ba su da masaniya game da sauƙin da ke tattare da harkar, kamar yadda masana suka yi bayani.
Shin CNG na da matsala?
Masanin ya ce iskar gas ta CNG ba ta da wata gagarumar matsalar da za a iya guje wa amfani da shi.
Dangane da bidiyoyin da ke yawo a shafukan sada zumunta na fashewar matar da aka sauya zuwa mai amfani da CNG, masanin ya ce ba a yi amfani da ingantattun kayan aikin da suka dace ba.
Masanin ya ce matsawar aka yi amfani da ingantattun kayan aiki, wajen mayar da mota mai amfani da CNG, to la shakka babu wata matsala da ke tattara da hakan, kamar yadda Aminu Tijjani Auwal ya bayyana.
Mene ne bambancin iskar gas ta LPG da ta CNG?

Asalin hoton, Getty Images
LPG shi ne iskar gas ɗin da ake amfani da ita wajen sanya wa tukunyar iskar gas domin girki, yayin da CNG kuma shi ne iskar gas da ake sanya wa ababen hawa wadda aka tace ta aka ragewa ƙarfin kama wa da wuta.
Aminu Tijjani Auwal, wani ƙwararren masanin harkar iskar gas a Najeriya ya shaida wa BBC cewa wani ƙarin bambancin da ke tsakanin waɗannan makamashin shi ne tukunyar CNG ba ta ɗaukar zafi saɓanin tukunyar iskar girki ta LPG.
''Yanzu idan za ka sanya wa motarka CNG ka fara tafiya, idan ka jima har raɓa za ka gani a jikinta'', in ji shi.
Masanin ya ƙara da cewa gas ɗin LPG yana da hayaƙi (flamable), ''ko yaya idan ya haɗu da wuta zai iya kamawa da wuta''.
Ta fuskar nauyi masanin ya ce CNG bai kai LPG nauyi ba.
Haka ma dangane da araha, iskar gas ta LPG ta fi CNG tsada, kamar yadda masanin ya yi bayani.
''Yanzu shi LPG ana sayar da kilo guda nasa a kan kudi naira 1,400 zuwa 1,500, yayin da ita kuma CNG ake sayar da ma'auninta (SCM) a kan naira 230 zuwa da 250'', in ji shi.
Hanyoyin da za a bi wajen gamsar da jama'a

Asalin hoton, Getty Images
Masanin ya ce abin da ya kamata a yi domin mutane su gamsu da amfani da CNG shi ne wayar da kai.
''Yana da kyau gwamnati ta ɓullo da dabarun wayar da kai, ta yadda mutane za su fahimci amfaninsa da kuma sauƙinsa'', in ji shi.
A gwamnati ta ɓullo da ƙarin wuraren mayar da motocin, masanin ya ce wani abu da ke sa mutane tsoron abin shi ne yadda wuraren sauya motar ba su da yawa.
Haka ma ya ce yana da kyau a ƙara yawan gidajen man da za su riƙa bayar da man ta yadda mutane za su riƙa ganin wadatuwar man gas ɗin na CNG.
''Matsalar yanzu ita ce idan kana son shan CNG a motarka, sai ka kwashe wasu sa'o'i masu yawa kana jira, to tabbas hakan yana rage wa mutane sha'awar mayar da motocinsu m,asu amfani da CNG.
Masanin ya ce a baya gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa kamfanin mai a ƙasar NNPCL zai riƙa sayar da gas ɗin, amma har yanzu ba a ga hakan ba tukunna.











