Matar da ta fi kowa gajarta a Kenya: Ƙalubalen da nake fuskanta

Asalin hoton, Alice Mbere
- Marubuci, Hamida Aboubakar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Swahili
- Aiko rahoto daga, Nairobi
- Lokacin karatu: Minti 4
Alice Mbere, ƴar ƙasar Kenya mai shekara 27 a duniya ita ce ta biyar a cikin yara tara da iyayenta suka haifa.
An haife ta lafiya ƙalau, sai dai a lokacin da ta kai shekara biyar ne iyayenta suka gane cewa tsawonta ya yi kaɗan da yawa, inda a lokacin ne suka fara tuntuɓar likitoci.
"Na tuna cewa akwai wani likita da ya taɓa ba ni magani, ya ce na riƙa sha safe da yamma, ya ce zan ƙara tsawo, amma har maganin ya ƙare babu abin da ya sauya a tsawona," in ji Alice.
Alice ta shaida wa BBC cewa kowane likita akwai nashi bayanin na daban da yake yi game da batun tsawonta.
Wasu suka ce tana da matsalar ƙashi. Wani ya ce idan aka yi mata tiyata za ta ƙara tsawo. Sai dai duk waɗannan babu abin da ya yi aiki.

Asalin hoton, Alice Mbere
"Har iyayena suka gaji, an kai lokacin da mahaifina ya ce matuƙar dai rashin tsawon ba zai cutar da lafiyata ba, to a ƙyale ni kawai yadda nake."
Alice na da tsawon santimita 85 ne kacal. Kuma tana amsa cewa ita mutum ce mai buƙata ta musamman.
Alice na fama ne da wata lalura ta rashin tsawo, kuma ta fara cin karo da ƙalubale ne a lokacin da ta shiga makaranta, inda ta ga ta sha bamban da sauran ɗalibai.
Kasancewar mutane a kodayaushe sai su riƙa kallon ta suna mamaki.
"Zan iya tuna lokacin da na shiga makarantar sakandare, a lokacin da na fara zuwa shugaban makarantar ya yi yunƙurin ƙin ɗauka na, inda ya ce a kai ni makarantar masu buƙata ta musamman," in ji Alice.

Asalin hoton, Alice Mbere
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaban makarantar ya ce Alice na buƙatar gado na musamman da kuma wasu abubuwa da ke buƙatar kashe kuɗi, kuma makarantar ba ta da waɗannan kuɗaɗen da za ta kashe.
Ta ce ba ta ji daɗin maganarsa ba, kuma ta ji tamkar an tsangwame ta.
Sai dai duk da ƙalubalen da ta fuskanta wajen neman ilimi, ta jure, har ta kammala karatunta na digiri a Jami'ar Co-operative University of Kenya, inda ta karanta fannin kula da ma'aikata.
"Akwai ƙalubale sosai ga mutum mai gajarta iri na, ɗaya daga cikin irin waɗannan ƙalubale shi ne samun kayan sawa da suka min daidai," in ji Alice.
Ta ce ba kowane kanti ne za ta iya shiga ta samu kayan da za su yi mata daidai ba, saboda haka a mafi yawan lokuta takan shiga kantin sayar da kayan yara ne domin samun kayan da za su mata daidai.
A wasu lokutan kuma ta gwammace ta ɗunka, saboda akwai wani telanta na musamman wanda yake da awonta kuma yakan ɗunka mata kayan da za su mata daidai a duk lokacin da take buƙata.

Asalin hoton, Alice Mbere
Sai dai, ƙalubale mafi girma da takan ci karo da shi sanadiyyar tsawonta, kamar yadda ta ce, shi ne yin wasu abubuwan na kasancewa mai matuƙar wahala, musamman a rayuwa irin ta yau da kullum.
"Shiga motar haya na yi min wahala. Domin sai an cincinɗa ni kafin na iya shiga motar, kusan sai an taimaka min wajen yin komai.
A gida, tana da wani ƙaramin tsani da kuma sandar dogarawa na musamman waɗanda take amfani da su wajen ɗauko abubuwa da ke saman kanta da shiga ban-ɗaki da kuma hawa gado.
Game da yadda take kallon rayuwarta a gaba, ta ce tana so ta haihu, kuma ta ce yanzu haka tana da saurayi wanda take matuƙar ƙauna, kuma yana da madaidaicin tsawo sannan yana da fara'a sosai kamar ta.
Ta ce tana sa ran samun iyali mai girma, kuma likitoci sun tabbatar mata cewa hakan abu ne da zai yiwu.
Ta shawarci masu bukata ta musamman cewa su sani kowane ɗan'adam daban yake, kuma kowa da irin rayuwarsa. Saboda haka abu ne mai kyau mutum ya karɓi ƙaddarasa ya yi rayuwa kamar kowa duk kuwa da irin ƙalubalen da zai iya fuskanta.











