Shimfiɗa ƙyalle a daren farko da sauran al'adun auren Hausawa da suka ɓace

Mace na kaɗa shantu

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 7

Hausawa al'umma ce da ke da dogon tarihi na al'adu da suka gada daga kaka da kakanni.

Daga cikin al'adun da suka shahara a baya, akwai na neman aure, da shirye-shiryen daura aure da kuma kyawawan dabi'u da ake koya wa matasa kafin su shiga gidan aure.

Sai dai, a yau, da yawa daga cikin wadannan al'adun sun fara ɓacewa, wasu kuma sun sauya saboda canjin zamani da kuma tasirin addini.

To ko waɗanne al'adun auren Hausawa ne suka fara ɓacewa?

Domin sanin waɗannan al'adun ne BBC ta tuntuɓi farfesa Balarabe Abdullahi, na Sashen Harsuna da Al'adun Afirka na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Farfeasa Balarabe ya bayyana cewa yanzu matasa da yawa ba su da masaniya kan yadda ake gudanar da aure a baya.

Al'adun neman aure a da

Masu kidi

Asalin hoton, FB/Sani Maikatanga

A zamanin da, neman aure ya kasance wani tsari na musamman da ke tabbatar da aminci da girmama iyaye da al'umma. Wasu daga cikin muhimman al'adun in ji Farfesa Balarabe sun hada da:

Kame

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan ita ce al’adar zabar wa ‘yaya mata tum suna jarirai ko kuma a lokacin da suke da kananan shejaru. Uba kan yi wa ɗansa kamen yarinya tun tana jaririya ko kima a wani lokacin iyayen yarinya da na yaro kan zauna su amince da hadin.

A saboda haka wasu yaran sun san mazansu ko kuma matansu tun suna kanana.

A mafi yawan lokuta auren kan gudana bayan sun girma ba tare da wata tangarda ba, kasancewar a wancan lokaci akan yi wa yara aure ne da karancin shekaru.

Sai dai sanadiyyar wayeywar zamani abubuwa sun sauya, inda wasu yaran suka rika nuna turjiya, wannan ya zamo daya daga cikin abubuwan da suka sa irin wannan aure ya daina samun tagomashi, inda tanzu aka fingwammacewa a bar yara su zabi wanda suke so.

Tsarance

Wannan wata dadaddiyar al’ada ce da Hausawa suka rika yi kafin zuwan addinin Musulunci.

Yarinyar da za a aura, za ta je gidan iyalin angon ne ta kwana a dakinsa tana sanye da dirwan bante. Ana so a ga ko rashin aminci zai shiga tsakaninsu.

Idan aka lura cewa babu abin da ya faru a tsakaninsu, za a ba shi ita aure saboda amanar da suka rike. Idan kuwa ya gaza jurewa to ba za a ba shi ita ba.

Wannan na daga cikin al’adu da Hausawa suka yi watsi da su sanadiyyar wayewa ta Musulunci, kasancewar bai yi daidai da tanade-tanaden addinin ba, in ji farfesan.

Toshi

Wannan na nufin kyautatawa tsakanin saurayi da iyayen yarinya. Yakan kai musu kayayyaki ko taimakawa a gonar gida. Ana ganin hakan a matsayin shaida ta gaskiya da niyya.

Sai dai a zamanin yanzu irin wannan hidima da ango kan yi wa yarinya da iyalanta ta sauya, inda takan zo ta siga daban-daban.

A yanzu abin da ya rage ana yi shi ne hidimar da akan kira ‘na gani ina so’, inda ango ke sayen wasu kaya na masarufi ya kai wa iyalin amarya, ciki har da abubuwa kamar goro da alawa da biskit, wanda akan raba wa dangi domin sanar da su cewa yaro ya nuna cewa yana neman ‘yarsu da aure.

Auren sadaka ko kyauta

Aure na buƙatar sadaki kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, amma, a da, akan yi auren sadaka ne kamar inda wani uba ko ubangida kan bai wa saurayi kyautar budurwa saboda kyawawan ɗabi'unsa da biyayya ko kuma nasaba.

A yanzu ko da za a yi aure mai kama da sadaka, mahaifin budurwa ne kan dauke wa saurayi hidimar biyan kudin sadaki, a wasu lokuta har da sauran hidimomi.

Al'adun lokacin aure

Hannu da lalle

Asalin hoton, Getty Images

Farfesa Balarabe ya ce ɗaura aure a da ya sha bamban da yadda ake yi a yanzu. Wasu daga cikin tsofaffin al'adun da aka yi su sun hada da:

Shimfiɗar faranji ko farin ƙyalle

Wannan ma wata al’ada ce da wayewar Musulunci da kuma zamani ya tafi da ita.

A zamunnan baya, akan shimfiɗa farin ƙyalle a gadon amarya a darenta na farko a gidan miji.

Makasudin yin hakan shi ne domin tabbatar da budurcinta.

A mafi yawan lokuta mutanen da shekarunsu suka jaya ne ke shimfida kyallen kuma su ne suke zuwa su kwashe a washegari.

Ana daukar kai budurci gudan aure a matsayin daraja da kuma alama ta kyakkawar dabi’a da tarbiyya daga bangaren amarya.

Gaza kai budurci gidan aure ya kasance wani abu da ke haddasa kananan maganganu tsakanin al’umma, tare da nuna yatsa ga iyalin amarya, wani abu da a wancan lokaci kan yi sanadiyyar mutuwar aure.

Kai amarya a kan doki ko jaki

A zamanin baya, amfani da doki ko jaki wajen kai amarya na daga cikin gata da za a nuna wa mace, maimakon a bar ta ta taka sayyada.

Dama wadannan hanyoyi sun kasance manyan hanyoyin sufuri a kasar Hausa, kasancewar babu abubuwa kamar mota wadda ake amfani da ita a yanzu.

Daga bisani kuma an rika amfani da babur, amma a wannan zamani an fi amfani ne da motoci, wani lokaci ma har da jirgin sama wajen kai amarya.

Gado

Asalin hoton, Getty Images

Kiɗan ƙwarya

Wannan yawanci tsofaffi ne ke taruwa a filin gida suna kiɗa da ƙwarya duk a cikin murnar bikin.

Wata hanya ce ta nuna murna, inda dangi da aminai da makwafta, musamman mata kan taru suna rawa domin taya amarya da iyayenta farin ciki.

A yanzu irin wadannan shagulgula su ne ake gudanarwa a matsayin kamu, ko dina da dai sauran su.

Ajo

Wannan al'adar ita ce taimakon da ake yi wa ango a lokacin da ya yi aure kasancewar Hausawa masu kara ne a tsakaninsu, akan yi ajo a ranar da ake wankin ango.

Har yanzu akan yi hakan wasu yankunan Sokoto da Zamfara, inda akan rika yi wa ango liki ko karin kudi a lokacin wankan ango.

Sai dai a zamanin yanzu irin wannan na zuwa ne a sigar karo-karo da abokai kan yi wa ango a lokacin biki ko kuma karin kudi da ake yi wa ango a lokacin dina ko wasu shagulgulan.

Wankan Ango da Amarya

Har yanzu ana gudanar da irin wannan al’ada a wasu yankunan kasar Hausa, kamar Sokoto da Zamfara.

A lokacin da aka ɗaura aure, akwai wasu manyan bukukuwa da ba a iya bari su wuce. Wankin ango misali, wata al'ada ce da Hausawa suka ɗora muhimmanci a kai. Ana yin wannan wanka da dare bayan an gama ɗaura aure, kuma shi ne karo na farko da saurayi zai yi irin wannan bikin a rayuwarsa.

Amarya ma kan yi wankan amarci kafin ta shiga gidan miji. Daga nan kuma a yi mata budar-kai, sayen baki da kanwar rana domin nuna amincewar al'umma ga sabuwar matar.

Wane tasiri wadannan al'adu suka yi a zamantakewar ma'aurata?

Farfesa Balarabe ya ce wadannan al'adun Hausawa sun yi tasiri matuka a zamantakewar ma'aurata da rayuwar iyalai ta hanyoyi da dama da suka haɗa da;

  • Kula da zaman ma'aurata

Iyaye suna tabbatar da cewa an tsara zaman ma'aurata yadda ya dace. Wannan yana taimakawa wajen kafa tushe mai karfi na zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin miji da mata.

  • Koyar da kyawawan ɗabi'u

Ana lura da kunya da ladabi, wanda ke tabbatar da cewa ma'aurata suna bin dabi'u na mutunci da girmama juna.

  • Koyar da fasahar rayuwa

Idan amarya ba ta iya girki ba, za a koya mata. Wannan yana taimakawa wajen tabbatar da cewa kowanne bangare na aure yana da kwarewar da ake bukata don rayuwa cikin lumana.

Me ya sa aka yi watsi da wasu al'adun?

…

Asalin hoton, Getty Images

Farfesa Balarabe ya bayyana dalilai da dama da suka sa yawancin waɗannan al'adun suka dusashe. Ya ce:

  • Tasirin addinin Musulunci, wanda ya tsara aure bisa tsari ta daban.
  • Sauyin zamani da zuwar fasaha; Wadannan ma sun sauya yadda matasa ke kallon aure.
  • Cakuduwar al'umma, wadda ta kawo sababbin al'adu daga waje.
  • Yanayin tattalin arziki, wanda ya rage ikon mutane wajen gudanar da manyan bukukuwa.

"Abubuwan nan da ake yi a da, idan aka dubi yadda rayuwa ta sauya, akwai yiwuwar su ɓace gaba ɗaya idan ba a ɗauki matakin adanawa ba," in ji Farfesa Balarabe.

Ko daina amfani da su zai zama illa ga al’adun Bahaushe?

Farfesan ya ce daina amfani da wasu daga cikin wadannan al'adun zai iya zama illa wajen adana dadaddun al'adun Hausawa.

Ya bayyana cewa al'adun kamar Toshi da Kame da Sadaka da sauran al'adun aure suna ɗauke da darussa masu yawa kamar kunya da girmama na gaba da rikon amana, da neman na kai.

Idan aka bar wadannan al'adu gaba daya, al'umma za ta rasa wasu muhimman darussa kuma waɗanda ke tasowa ba za su samu wata masaniya ba kan waɗannan al'adu.

Tun ina jaririya aka yi min kamen miji

BBC ta kuma tattauna da wata tsohuwa 'yar shekara 85 da ake kira da Gwaggo daga Kano, wadda ta bayar da tarihin yadda aka yi mata aure a lokacin da.

Ta ce lokacin da aka yi mata aure, ba ta kai shekara 15 ba.

"Tun ina jaririyata aka ce an yi min kame. Lokacin da aka kawo maganar aurena, an fara ne da toshi inda mijin da zan aura ya dinga kai wa iyayena hatsi da dabbobi." in ji ta.

"A ranar da aka ɗaura aure na, a zauren mahaifina aka ɗaura ba a masallaci ba. Bayan haka aka yi min wankan amarci, daga nan aka kai ni gidan mijina a kan jaki."Gwaggo Hauwa ta ƙara da cewa.

Ta kuma ce, a lokacin da za a yi mata aure, ba ta iya wasu abubuwa ba kamar girki, sai da aka koya mata harda yadda za ta wa mijinta ladabi da dai sauransu.

Al'adun auren Hausawa in ji farfesa Balarabe sun kasance ginshiƙi wajen tabbatar da aminci da ladabi da kunya da girmama juna tsakanin angon da amarya,da iyaye da kuma al'umma gaba ɗaya.

Farfesa Balarabe ya ƙara da cewa duk da cewa zamani ya kawo sauye-sauye, akwai buƙatar al'umma ta ƙarfafa tunawa da waɗannan al'adun, domin su zama haske da jagora ga matasa a yau wajen gudanar da aurensu cikin nagarta da aminci.