Matsalar da ke janyo yawan ɓarin ciki da mata ba su sani ba

Asalin hoton, Getty Images
Akwai wasu matsalolin lafiya da mata ke fuskanta a cikin ɗaukar ciki da haihuwa da ake gani kamar ƙananan abubuwa ne, amma sukan zama babbar barazana ga iyali.
Ɗaya daga cikin irin waɗannan matsalolin ita ce ‘RH incompatibility’ – wani yanayi da ke faruwa idan jinin uwa da na jariri ba su jitu ba kamar yadda Dr Bahijja Faruk, ƙwararriryar likitar mata ta shaida wa BBC.
Wannan matsala in ji ta na janyo zubewar ciki akai-akai da haihuwar jarirai marasa ƙarfi ko marasa lafiya ko ma mutuwar jarirai kafin ko bayan haihuwa.
Ta ƙara da cewa, "A cikin al'ummominmu inda mutane ke da ƙarancin ilimin kiwon lafiya, musamman batun RH, mata da dama na fuskantar ɓari ba tare da sanin musabbabin matsalar ba."
Mene ne rashin jituwar jini (RH incompatibility)?
Dr Bahijja ta bayyana cewa, RH wani sinadari ne da ke cikin jinin mutum.
Yana zuwa a nau'i biyu ne in ji ta da suka haɗa da:
- RH Positive (RH+)
- RH Negative (RH−)
Saboda haka rashin jituwar jinin uwa mai ɗauke da juna biyu da na jariri, shi ake kira da ‘RH-incompatibility’.
"Idan mace tana da jinin RH-negative, mijinta kuma yana da RH-positive, jaririn da za ta haifa zai iya gado jinin mahaifi. Wannan na iya janyo matsala domin jinin uwa ba zai jitu da jinin jaririn ba," in ji likitar.
"Abin da ake nufi a nan shi ne jinin RH-negative ba ya jituwa da na RH-positive."
"Dalilin haka ne jikin uwa za iya ɗaukar jinin jariri a matsayin abokin gaba, ya ƙirƙiri ƙwayoyin kariya da ke kai farmaki ga jinin jaririn, wanda hakan ke haifar da abubuwa kamar haka:
- Zubewar ciki
- Rashin girman jariri cikin lafiya,
- Lalurar Jaundice mai tsanani,
- Ko mutuwar jariri cikin mahaifa.
Mene ne ke haifar da rashin jituwar jini?
Likitar ta ce wannan matsalar na faruwa ne idan jinin uwa da ke Rh-negative ya haɗu da na jariri da ke Rh-positive wanda ke faruwa yayin ɓari ko haihuwa ko ɗaurin ciki mara kyau (ectopic pregnancy), ko gwaje-gwajen ciki da ake yi da allura da dai sauransu.
Yadda RH Incompatibility ke shafar ciki

Asalin hoton, Getty Images
Dr Bahijja ta ce wannan lamari na iya shafar ciki ta fanni daban-daban.
Ga jariri, zai iya
- Lalata jinin jariri har ya kai ga mutuwa
- Shawara mai tsanani (Jaundice)
- Rashin isasshen jini (anemia)
- Hydrops fetalis (Wannan wata matsala ce mai tsanani a cikin ciki, inda ruwa ke taruwa a kalla a sassan jiki biyu na jariri, kamar cikin ƙirji (pleural effusion) da zuciya (pericardial effusion), ko ƙarƙashin fata (edema).
- Rashin girman jariri
- Mutuwar jariri a ciki ko bayan haihuwa
Ga Uwa kuma, ta ce
- Ɓari akai-akai
- Ciki ba ya tsayawa
- Cikin da ke ɗaukar tsawon lokaci ba tare da haihuwa ba
- Damuwa da fargaba
"Shekarata 10 da aure, sau shida ina ɓari'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A lokacin da Maryam ta auri mijinta shekaru goma da suka gabata, burinta bai wuce ta haihu ta riƙe ɗanta ko 'yarta ba amma har yanzu burin na ta bai cika ba.
Cikin shekaru goma da aurensu, Maryam ta yi ɓari sau shida, ba tare da ta taɓa gane dalilin ba.
"Na fara daukar ciki ne a shekarar farko bayan aurenmu," in ji Maryam. "Amma cikin bai kai watanni biyu ba ya zube. Na yi tunanin wata matsala ce ta wucin gadi. Bayan haka kuma na sake ɗauka, har sau biyar duk suna zubewa."
Shekaru suna tafiya, damuwa na ƙaruwa, magunguna da addu'o'i sun yi yawa, amma ba wani sauyi. Sai dai ɓarin cikin da take samu akai-akai.
Sai daga baya da ta sake ɓari, sai wata ƙawarta take faɗa mata batun Rh -incompatibiliy, shine ya sa ta faɗawa mijinta sai suka je babban asibiti akwai gwada su.
"Asibitin gaskiya na da tsada, amma kuma sun wayar da kanmu kan wannan batu kuma sun mana maganar alluran rigakafin da ya kamata mace mai Rh- ya kamata ta karɓa bayan ɓari ko haihuwa, abin da bata taɓa ji ko karɓa ba." in ji ta.
Yanzu dai ta ce sun je asibiti kuma sina fatan komai zai yi dai-dai daga yanzu.
Mene ne rigakafin Anti-D (RhoGAM)
Likitar ta ce alluran rigakaifin da ya kamata a yi wa mace mai RH- da ta ɗauki ciki ta haihu ko ta samu ɓari da zai kareta daga wani ɓarin idan ta samu wani cikin shi aka kira da Anti-D (RhoGAM)
"Idan har ba ta karɓi wannan rigakafin ba, jikinta na iya samar da ƙwayoyin halitta na kariya wato antibodies kenan.
Wadannan antibodies din suna kasancewa a cikin jini suna aiki ta hanyar;
- Kai farmaki ga jinin jaririn idan wani sabon ciki ya shiga.
- Lalata jinin jaririn tun kafin ya girma.
- Ɓari sau da yawa koda kuma jaririn ya fara girma.
Ana bayar da rigakafin ne duk
- Bayan ɓari
- Cikin awanni 72 bayan haihuwa idan jariri Rh-positive ne
- Lokacin da aka yi tiyata ko wani abu da zai zubar da jini
- A makonni 28 na ciki (domin kariya)











