Murƙushe masu zanga-zanga a Najeriya tauye haƙƙi ne - Amnesty

Nigeria

Asalin hoton, Take It Back/X

Lokacin karatu: Minti 2

Kungiyar kare haƙƙin ɗan'adama ta Amnesty International ta bayyana damuwa da kuma allawadai kan yadda aka tarwatsa masu zanga-zanga a Najeriya.

A ranar Litinin ne wasu ƴan ƙasar suka fito zanga-zanga ta neman shugabanci nagari a Najeriya, yayin da kuma suka yi arangama da jami'an tsaro.

Zanga-zangar da wata kungiya ta "Take It Back" ta jagorata, ta bazu zuwa wasu manyan biranen Najeriya da suka hada da Abuja da Legas da Fatakwal duk da gargaɗin 'yan sanda suka yi na kaucewa gudanar da zanga-zangar.

'Yansandan Najeriya sun tarwatsa masu zanga-zangar a Fatakwal da Abuja babban birnin ƙasar ta hanyar harba musu hayaƙi mai sa hawaye.

Daraktan kungiyar Amnesty a Najeriya, Malam Isah Sanusi, ya ce sun yi allawadai da abin da ya faru kan masu zanga-zangar.

"Muna da labarin an kama wasu an tsare su, amma muna koƙarin mu tantance."

"Wannan abin kunya ne kuma abin takaici ne, domin mutane sun fito cikin lumana amma an nuna masu ƙarfi don haka mun yi allawadai da matakin da aka ɗauka," in ji Isa Sanusi.

Ya ƙara da cewa ba za ta taɓa samun zaman lafiya ba har sai mutane suna da ƴanci da dama da za su bayyana ra'ayinsu a kan yadda ake mulkinsu kan abin da ya masu daɗi da wanda bai masu daɗi ba.

"Ƴan Najeriya suna da ƴancin su fito su yi zanga-zanga cikin lumana, domin tsarin dimokuraɗiyya ya bayar da dama ga ƴan ƙasa su faɗi albarkacin bakinsu," in ji shi.

Kungiyar kare hakkin ɗan'adama ta yi kira ga gwamnatin Najeriyar ta kaucewa shiga hakkin jama'a na gudanar da zanga-zanga kan abubuwan da suke ganin ya kamata a yi gyara a kansu.

Ƙungiyar da ke jagorantar zanga-zangar ta ce ta sanar da rundunar ƴansanda game shirin gudanar da zanga-zangar domin samun kariya saboda ƴanci ne na dimokuraɗiyya.

Tun da farko rundunar ƴansandan Najeriya ta bayyana damuwa game da shirin zanga-zangar.

A sanarwar da ta fitar, rundunar ƴansandan ta ce an ware ranar bakwai ga Afrilu a matsayin ranar ƴansanda a Najeriya amma sai masu shirya zanga-zangar suka zaɓi gudanar da zanga-zangar a ranar.

Ƴansanda sun sha yin arangama da masu zanga-zanga a Najeriya musamman idan zanga-zanga ce ta nuna adawa ko kuma ƙyamar gwamnati.