Me ke faruwa tsakanin Wike da gwamnan Bayelsa?

Gwamna Douye Diri na Bayelsa da Ministan Abuja Nyesom Wike

Asalin hoton, BBC Collage

Bayanan hoto, Gwamnana Bayelsa Douye Diri (hagu) da Ministan Abuja Nyesom Wike
Lokacin karatu: Minti 4

Rikicin siyasa a yankin kudu maso kudancin Najeriya na yaɗuwa zuwa jihar Bayelsa tun bayan saka dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar Rivers mai maƙwabtaka.

A wannan karon ma, ministan Abuja kuma tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike, shi ne kan gaba a rikicin, wanda wani magoyin bayansa George Turnah ya nemi shirya gangamin nuna goyon baya ga ministan da kuma Shugaba Tinubu na jam'iyyar APC a jihar ta Bayelsa.

Sai dai tuni wata babbar kotun Bayelsa ta haramta yin taron bayan antoni janar na gwamnatin jihar ya kai ƙarar Mista Turnah da Wike, yana mai cewa hakan "zai iya tayar da fitina".

Rahotonni na cewa magoya bayan Wike na ci gaba da shirin gudanar da taron, lamarin da ya sa shugabancin jam'iyyar PDP na jihar suka shirya nasu taron makamancin na su Nyeso Wike a farfajiya ɗaya.

Yankin na Neja-Delta ya daɗe yana fama da rikicin 'yanbindiga masu fasa bututun man fetur, kuma hakan na cikin dalilan da Tinubu ya bayyana kafin saka dokar ta-ɓaci a Rivers mai cike da cecekuce.

Wike ya fara takun saƙa da shugabancin PDP ne tun bayan kammala zaɓen fitar da gwani na takarar shugaban ƙasa a 2023 wanda bai yi nasara ba, inda daga baya ya ƙulla ƙawance da Bola Tinubu har ma ya zama minista a cikin gwamnatin ta jam'iyyar APC.

Mene ne asalin rikicin PDP a Bayelsa?

Tutar jam'iyyar PDP

Asalin hoton, PDP

Rikicin tsakanin Gwamnan Rivers Siminalayi Fubara da tsohon Gwamna Nyesom Wike ya shahara a siyasa da jaridun Najeriya.

Daga baya ministan na Abuja ya ci alwashin haddasa rikici a duk jihar yankin Neja-Delta da PDP ke mulki kuma ta goya wa Fubara baya, wanda shi ne mafarin rikici a Bayelsa mai maƙwabtaka.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamna Diri na Bayelsa na cikin gwamnonin PDP biyar na yankin Neja-Delta da ke adawa da Wike. Cross River ce kawai ba ta PDP ba a yankin.

Rigimar ta ƙara ƙamari ne bayan ɓangaren Wike ya shirya zaɓukan shugabancin PDP na mazaɓu a yankin kudu maso kudu ranar 22 ga watan Fabrairu, inda kuma wanda yake mara wa baya Dan Orbih ya samu nasara a matsayin shugaba da kuma George Turnah a matsayin sakatare.

Sai dai shugaban PDP na riƙo a ƙasa, Umaru Damagun, ya yi watsi da zaɓen a matsayin haramtacce, kuma a ranar 7 ga watan Maris kwamatin gudanarwar PDP na ƙasa ya rantsar da kwamatin shugabanci na riƙo ƙarƙashin jagorancin Emma Ogidi.

Cikin umarnin da kwamatin ya bai wa shugabannin riƙon akwai sake gudanar da zaɓen shugabanci a mazaɓu ranar 12 ga watan Afrilu.

"A wurin kwamatin gudanarwa na ƙasa, ba a yi wani zaɓen shugabannin kudu maso kudancin Najeriya ba. Saboda babu daɗewa wa'adinsu ya ƙare, a yau ne muke naɗa kwamatin riƙo," a cewar Damagun lokacin rantsar da kwamatin a watan Maris.

Mista Turnah da ƙungiyarsa ta New Associates sun zaɓi ranar ta 12 ga Afrilu don gudanar da gangamin goyon bayan Wike.

Gwamnan Bayelsa Douye Diri ya ce sun an kori Turnah daga PDP tun tuni.

"Wani maras kunya ne kawai yake ganin ya isa ya jagoranci wani ɓangare na PDP a Bayelsa ta hanyar haɗa kai da tsohon gwamnan Rivers Wike. Jam'iyyarmu a Bayelsa ta kori Turnah," in ji Diri.

Illar da rikicin zai haifar a yankin

Tuni masana harkokin siyasa a Najeriya suka fara karanta sabon rikicin na Bayelsa ta fuskoki daban-daban, musamman ganin maƙwabciyar Rivers ce.

"Babu abin wannan gangami zai haifar sai dai ƙara taɓarɓara lamarin siyasa," a cewar Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero ta Kano.

Masanin ya ce sun fara lura da yadda rikicin ke shirin haddasa rikicin ƙabilanci a yankin na kudu maso kudancin Najeriya.

"Idan aka je maƙabtan Rivers aka gudanar da wannan gangami, to zai ƙara assasa rikicin ne. Kuma kada a manta rikcin ya fara haddasa gaba tsakanin wasu ƙabilu, inda alamu suka nuna wata ƙabila ce ake nema a ƙwace wa dama," in ji shi.

"Yayin da ake yin irin tashintashina [a jihar Rivers], bai kamata ma a je a yi wannan gangami ba. Sannan kuma shi kansa zaɓen na 2027 saura shekara biyu. Domin haka, ganmi a yanzu bai dace ba."

Wani mai sharhi kan siyasar kudu maso kudancin Najeriya, Alhaji Yahaya Wunti, ya ce gwamnatin Bayelsa na ɗauki darasi.

"Taron na nuna isa ne kawai. Ita kuma gwamnatin Bayelsa ta fuskanci haka, abin da ya sa kenan ta hana gudanar da shi," a cewarsa.