Ta yaya za a inganta aikin ɗansanda a Najeriya?

Asalin hoton, FCT Police command
A ranar Litinin 7 ga watan Afrilu ne aka yi bikin ranar ƴan sanda ta Najeriya wadda aka ƙirƙira da manufar yin waiwaye kan ayyukansu da lalubo hanyoyin inganta aiki da rayuwarsu.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ne ya ayyana ranar bikin tuna wa da ayyukan ƴan sandan a kowace shekara.
Yayin bikin a dandalin Eagles Square da ke Abuja, shugaba Bola Tinubu wanda mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima ya wakilta ya sha alwashi yi wa rundunar ƴan sandan ƙasar garambawul domin dacewa da zamani.
Shin ta yaya ya kamata a inganta aiki da rayuwar ƴansandan na Najeriya? BBC ta tattauna masana dangane da hakan:
Kallon da jama'a ke yi wa ƴansandan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Kusan za a iya cewa idan aka ambaci aikin ɗan sanda a Najeriya abin da ke fara zuwa ran ƴan ƙasar shi ne rashawa da cin hanci da ƙage da sharri kamar yadda wani ɗan sanda da ba ya son a ambaci sunansa ya shaida wa BBC.
"Irin kallon da jama'a suke yi mana shi ne masu rashawa da cin hanci, mabarata kuma azzalumai sannan kuma masu sana'ar gadin manya.
Wallahi idan ban da yanzu da rashin aikin yi ya damu matasa, da wuya ka samu matashin da ke son shiga aikin ɗan sanda saboda matsalolin da ke addabar aikin waɗanda aka gaza shawo kansu har yanzu." In ji ɗan sandan.
To sai dai Malam Kabiru Adamu, shugaban kamfanin da ke bayar da bayanan tsaro na Beacon Security and Intelligence ya ce ba laifin ƴan sandan ba ne dangane da irin kallon da ake yi musu.
"Akwai wasu muhimman abubuwan da rashin yin su ke janyo irin kallon da jama'a ke yi wa ƴan sandan Najeriya. Kuma idan har za a yi su yadda ya kamata to na tabbata aikin ɗan sanda zai samu martaba." In ji Malam Kabiru Adamu.
Hanyoyin inganta aikin ɗansanda

Asalin hoton, FCT Police Command
Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin samar da bayanai kan tsaro Beacon and Security Intelligence ya ce hanya ɗaya tilo ta inganta aikin ɗan sanda a Najeriya ita ce walwala.
"Ba bu abu mafi muhimmanci ga aikin ɗan sanda kamar walwala. Kuma walwala na nufin abubuwa masu yawa kamar haka:
- Kayan aiki: Idan dai har ana son inganta aikin ɗan sanda to dole ne a sama sa kayan aiki na zamani waɗanda doka ta tanada. Wannan ya haɗa da makamai da ababan hawa kamar motoci da babura da ma man da za a yi amfani da shi a ababan
- Sutura: Yanayin suturar da jami'an tsaro ke sakawa na taka muhimmiyar rawa wajen sanya musu ƙaimin sha'awar yin aiki sannan kuma ta ƙara musu ƙima a idanun ƴan ƙasa.
- Albashi da Fansho: Batun albashi da alawus-alawus na ƴan sanda na cikin muhimman abubuwan da ake buƙata domin inganta rayuwarsu. Albashi na gaba-gaba wajen bai wa duk wani ma'aikaci walwalar da ta kamata ya samu ya gudanar da ayyukansa. Ya kamata idan ana son inganta aikin ɗan sanda a Najeriya to a ba su albashi daidai gwargwadon buƙatunsu na yau da kullum domin guje wa matsalar rashawa cin hanci. Kuma wannan na nufin a tabbatar da fansho bayan ritaya.
- Kula da Lafiya: Bai kamata a ce ɗan sanda ba shi da lafiya amma ya rasa inda zai je ya samu kulawa ta musamman walau yana cikin aikinsa ko kuma ya bar aiki.
- Muhalli: Shi ma wannan wani abu ne domin duk lokacin da aka ce ɗan sanda ba shi muhalli mai kyau sannan wadatacce da zai zauna da iyalansa to zuciyarsa ba za ta daidaita a kan aikinsa ba. Kuma wannan ya kamata ya zama lokacin aikinsu da ma bayan aikin nasu.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴansanda nawa ne za su wadaci Najeriya?
Malam Kabiru Adamu ya ce babu gaskiyar cewa Majalsiar Ɗinkin Duniya ba ta ƙayyade cewa a samar da ɗan sanda guda ɗaya ga farar hula 450.
Ya ƙara da cewa akwai abubuwan da ake dubawa kafin a ƙayyade yawan ƴan sandan da ya kamata a samar a ƙasa.
"Idan ka duba a Najeriya, akwai hukumomin da ya kamata a ce suna ƙarƙashin ƴan sanda ne misali kamar EFCC da ICPC masu yaƙi da rashawa da cin hanci da hukumar kiyaye haɗurra. Amma ban sani ba ko siyasa ce ko mene ne ya sa aka raba su.
Saboda gane haƙiƙanin yawan ƴan sandan da Najeriya ke buƙata ya dogara ne ga tantance irin ayyukan da ya kamata su yi. Amma dai zancen gaskiya Najeriya na buƙatar ƙarin ƴan sanda." In ji Kabiru Adamu.
A 2024, shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin ganin ya inganta aikin ƴan sanda ta hanyar ƙara yawansu da samar musu makamai na zamani domin tafiyar da aikinsu kamar yadda doka ta tanada.











