Sabbin 'yansanda nawa Najeriya ke buƙatar ɗauka a kowace shekara?

Asalin hoton, NPF.GOV.NG
Yayin da rudunar ƴansandan Najeriya ta bayyana aniyarta na sake ɗaukar ƴan sanda dubu 30 a kowacce shekara, masu sharhi kan harkokin tsaro a ƙasar na ganin wannan adadi ba zai cike giɓin ƙarancin jami'an da ake da shi ba a ƙasar.
Masana tsaron na wannan tsokaci ne bayan da babban sufeton ya ce Najeriyar za ta ci gaba da ɗaukar ƴan sanda dubu 30 kowacce shekara.
Masanan na ganin cewa la'akari da irin ƙalubalen da ake fuskanta daga ɓangaren tsaro a Najeriya, adadin jami'an yan sandan da ake buƙata domin shawo kan matsalar, dole a ruɓanya yawan adadin.
SP Habibu Shehu Yakawada mai murabus ɗaya ne daga cikin masu wannan ra'ayi, ya ce kawo yanzu adadin 'yansandan Najeriya ba su kai 500,000 ba, kuma idan aka yi la'akari da jihohin da ake da su a Najeriya adadin ya gaza.
''Ta ina wannan adadin ƴansanda zai wadatar da Najeriya, da ke da jihohin 37 ciki har da babban birnin kasar Abuja'', in ji SP Yakawada mai murabus.
Haka kuma ya yi tsokaci kan tsarin tura ƴansandan da aka yaye zuwa jihohinsu don yin aiki, yana mai bayyana hakan da rashin dacewa.
''Ina jin dabara ce da gwamantin Najeriyar ta yi, na waɗanda aka tura garuruwansu, sun san masu aikata laifuka a yankunannsu, sai dai duk da haka ba dai-dai ba ne''.
''Mu a lokacin da muka yi aiki idan ka fito daga kwalejin 'yansanda, wasu jihohi aka tura mu, don mu je mu san mutanen yanki, su ma su sanmu''.
Har ila yau SP Yakawada mai murabus, ya ce 'duk da an samu ci gaba a ɓagaren samar da kayan aiki, ba kamar lokacin baya ba, akwai buƙatar gwamanti Najeriya ta yi wa ƴansadan ƙarin albashi don zaburar da su ƙara himma wajen kawar da ta ɓata gari a tsakanin al'umma.
"Ba kamar lokacin baya ba, da muka fara da naira 7,000 zuwa naira 8,000, amma albashin bai wadatar ba'..
A cikin 'yan shekarun nan batun ƙarancin yawan 'yansanda a Najeriya na daga cikin abubuwan da ake kallo ya na janyo matsala wajen yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar.











