Nigeria za ta dauki 'yan sanda 10,000 aiki

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce za a dauki sabbin ma'aikatan 'yan sanda dubu goma a kasar.
Shugaban ya sanar da hakan ne a cikin jawabinsa a wani taro da rundunar 'yan sandan kasar ta gudanar kan sha'anin tsaron kasar.
Makasudin taron shi ne tabbatar da cewa, jama'ar kasa da jami'an tsaro sun fahimci muhimmanci tsaro a tsakanin al'umma.
Cikin wadanda suka gabatar da jawabi a taron sun hada da shugaban 'yan sandan Najeriya Mista Sunday Arase da mai Alfarama Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar.
A cikin 'yan shekarun nan batun karancin yawan 'yan sanda a Nigeria na daga cikin abubuwan da ake kallo ya na janyo matsala wajen yaki da matsalar tsaro a kasar.






