Ƴan sa-kai 20 jirgin sojoji ya kashe a Zamfara - Amnesty

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar kare haƙƙin bil''adama ta Amnesty International ta ce jirgin sojin saman Najeriya ya kashe mutum 20 da jikkata gommai a ƙauyukan Maraya da Wabi da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, Amnesty ta ce mutanen da al'amarin ya shafa ƴan sintiri da suka taru domin tunkarar ƴnbindiga da suka shiga suka saci jama'a bayan hare-hare a ƙauyukan nasu.
Amnesty ta ce dole ne hukumomi su bincika al'amarin kasancewar ba wannan ne karo na farko ba ko da a wannan shekarar.
Abin da ya faru
Mazauna yankin sun ce 'yan bindigar sun sace mutune sama da 50 da ke aikin noma, amma jirgin saman da ya kawo dauki ya kashe wasu daga cikin 'yan sakai da ke ƙoƙarin korar 'yan bindigar.
Mazauna unguwar Mani da ke yankin ƙaramar hukumar ta Maru sun ce 'yan bindigar waɗanda suke kan babura sun kai musu harin da rana a lokacin da ake tsaka da aikin gona.
Mutanen sun ce koda isarsu sai suka fara harbin kan mai uwa da wabi da kuma kama wasu mutanen.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa, suna kan hanyarsu ta zuwa kai wa wadanda aka kai harin dauki sai ga wani jirgi saman soji shi ma ya je kai ɗauki to amma kuma sai ya fara harbinsu tare da hallaka wasu.
Mutumin ya ce,"ƴan bindigar sun tafi da mutum 50, shi kuwa jirgin saman sojin muna cikin tafi domin muje mu kai dauki inda aka kai harin sai muka hango yana yin ƙasa bayan da hango mu a nan ne sai ya fara mutane kowa kuma ya yi ta kansa, mu da Allah ya taimake mu sai muka kwanta kasa."
" Mun kwanta ne muka yi kamar muma jirgin ya bugemu to da muka gay a wuce sai muka mike muka kama gudu don tsira da ranmu.''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi ma wani mazaunin yankin da BBC ta zanta da shi buƙatar mahukunta ya yi da su ƙara kai musu ɗauki domin 'yan bindigar sun ce musu za su sake komawa garuruwan nasu.
Ya ce," Muna rokon gwamnati da ta ƙara mana jami'an tsaro domin su kare mu, amma kuma ya kamata su jami'an tsaron su sani cewa a wani lokaci suna kashe mana mutane a rashin sani, ya kamata su rinka tantancewa."
"Mun sanar da jami'na tsaro bayan kai mana hari to amma kawai sai muka ga jirgi ya zo ya kashe mana 'yan sakai."
Har kawo yanzu rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai ba akan wannan lamari.
Ko a watan Janairun shekarar 2025, wani jirgin saman Najeriya ya hallaka mutum 16 cikinsu har da 'yan sakai da manoma a kauyen Tungar Kara da ke jihar Zamfara bayan da sojojin suka yi zaton 'yan fashin daji ne.
Haka a watan Disambar 2024, ma wani harin jirgin sama ya kashe fararen hula 10 a jihar Sokoto, wanda gwamnan jihar ya bayyana a matsayin harin kuskure kan fararen hula.











