Sojin saman Najeriya na binciken kuskuren kashe fararen hula 24 a Giwa

Sojojin saman Najeriya

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 3

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce ta soma bincike bayan da rahotanni daga jihar Kaduna suka ce wani hari da jirginta ya kai ya kashe farar hula aƙalla 24.

Lamarin dai ya faru a ranar Juma’a ta makon jiya a yankin ƙaramar hukumar Giwa da ke arewacin jihar ta Kaduna.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi ne, rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kai hare-hare kan maɓoyar ‘yanta’adda a dajin Yadi da ke ƙaramar hukumar ta Giwa.

Sanawar wadda muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar Kabiru Ali ya fitar, ta ce an kai harin ne ranar Juma’a bayan samun sahihan bayanan sirrin da ke nuna akwai dandazon ‘yanta’adda da makamansu a wajen.

Sai dai wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar da yammacin nan ya ce fararen hula 24 aka kashe bayan da jirgin yaƙin Najeriyar ya yi luguden wuta kan wani masallaci da kewayensa yayin kai farmakin.

Rahoton ya ambato wani mazauni yankin Muhammad Husaini na cewa jiragen sun kai hari ne kan wani Masallaci da ke garin Jika da Kolo a maimakon maɓoyar ‘yanta’addan.

Haka ma rahoton ya ambato kansila mai wakiltar yankin Isma’il Ahmed na tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce mutane 24 ne da ke zaune daura da Masallacin da aka kashe.

Sai dai duk da ya amsa cewa kusan rabin wannan garin na hannun ‘yan fashin daji ne, amma a cewarsa wadanda aka kashe fararen hula ne.

Samun waɗannan rahotannin dai ne ya sa rundunar sojin saman a ranar Litinin ta sake fitar da wata sanarwar kan wannan farmakin na ranar Juma’a inda ta sake jaddada cewa sai da ta tantace bayanan sirrin da ta samu kafin kai wannan harin.

Har ma ta kara da cewa yankin ya kasance matattarar ‘yanta’adda tsawon shekaru biyu kenan yanzu kuma ta yi imanin wannan farmaki ya samu nasara wajen rage ayyukan ‘yan fashin daji da sauran hare-hare kan al’ummar jihar ta Kaduna.

Sai dai rundunar ta ce ba za ta yi fatali zarge-zargen cewa hare-haren sun rutsa da fararen hula ba, don haka ta kaddamar da bincike domin gano gaskiyar wannan lamarin kuma za ta sanar da al’ummar kasar abin da ta gano.

Sanarwar da rundunar ta fitar ranar Lahadi ta ce ta kai farmakin ne bayan samun bayanan sirri kan maɓuyar kusurgumin ɗan fashin daji Kadage Gurgu, wani makusanci ga Dogo Gide.

Ta ce ta kai harin ne sakamakon bayanan da ta samu cewa sun ce riƙaƙƙen ɗan fashin Kadage Gurgu na samar da mafaka ga ɓarayin daji da suka gudo daga jihohin Zamfara da Sokoto saboda luguden wutar da ake masu.

Yanzu kuma rundunar sojin sama ta ce ta ƙaddamar da bincike domin tabbatar da rahotannin da ke cewa fararen hula aka kashe.

Lamarin na ranar Juma'a shi ne na baya bayan nan a hare-haren da sojojin Najeriya ke kai wa da ke rutsawa da fararen hula. Ko a watan Disamban 2023 an kai hari ta sama inda aka kashe fararen hula kusan 100 a Tudun Biri a jihar Kaduna.