‘Yadda iyayena suka ɓoye cikin awaki don guje wa masu satar mutane'

....

Asalin hoton, getty images

"Lokacin da maharan suka shigo garinmu, na ji ƙarar harbe-harbe, sai na yi sauri na hau kan babur ɗina na tsere a cikin duhun dare, na bar matata da ƴaƴana da tsofaffin iyayena," kamar yadda wani mazaunin garin Kuchi ya shaida wa BBC, (ba za mu ambaci sunansa ba saboda dalilai na tsaro)

Mazaunin garin ya ce ya zaɓi ya ceci ransa tukuna inda ya tsere zuwa Minna, babban birnin jihar Neja ta tsakiyar Najeriya. Amma kuma ya damu matuƙa da halin da iyalansa ke ciki.

“Mahara sun kama matata da kuma yayarta. Amma daga baya matata ta tsere musu a lokacin da masu garkuwan ke ƙoƙarin kai su wurin da za su tsallaka kogin Shiroro.” in ji mazaunin garin.

Sai dai har yanzu masu garkuwan suna tsare da ƴar'uwar matarsa yayin da masu garkuwan sun riga sun kira ƴan'uwan waɗanda aka sace domin neman kuɗin fansa.

Ya ci gaba da cewa, "ƴaƴana da iyayena sun shiga ɗakin awakinmu suka ɓoye a cikin dabbobin da ke wurin. Abin farin cikin shi ne ba a gano su ba. Bayan maharan sun tafi, iyayena da ƴaƴana suka gudu cikin daji inda suka tsere zuwa wata unguwa da ke makwaftaka da mu.”

Matarsa ​​ta kira shi kwana ɗaya bayan faruwar lamarin inda ta ce ta yi nasarar tserewa kuma tana ɓoye a wani ƙauye. "Yanzu ina magana da matata ta waya, amma ba a wuri ɗaya muke ba."

A daren Juma'a ne wasu mutane ɗauke da makamai suka kai samame a ƙauyen Kuchi inda suka yi garkuwa da mutane aƙalla 160.

Jami’an yankin sun ce ƴan bindigar suna da makamai sosai kuma yana zargin cewa sun fito ne daga ƙungiyar Boko Haram yayin da suke ɗauke da tutocin masu iƙirarin jihadi a harin na ranar Juma’a.

Sai dai kuma har yanzu babu tabbacin ko ƴan bindigar na da alaka da ƴan boko haram.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaban karamar hukumar Munya wanda ƙauyen Kuchi ke ƙarƙashinta ya ce ƴan bindigar sun shafe sama da sa’o’i biyu a yankin suna dafa abinci da shan shayi tare da kwashe kayan shaguna da gidaje.

“Jami’an tsaro ba su kai ɗauki ba. Kuchi da al’ummomin da ke makwaftaka da su har yanzu suna cikin ƙangi ne na ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai,” in ji Aminu Abdul Hamid Na-jume, shugaban karamar hukumar Munya.

Ya shaida wa BBC cewa maharan, "sun bi gida-gida, suna sace mutane bayan sun kashe mutanen kauyen guda 10, ciki har da mafarauta biyar, a lokacin musayar wuta." Wasu mazauna garin uku kuma sun jikkata.

Yawancin waɗanda abin ya shafa mata ne da yara da kuma tsofaffi.

Mista Najume ya ce yanzu haka ana zaman ɗarɗar da tashin hankali a tsakanin al’ummomin da ke makwabtaka da su yayin da mazauna Kuchi ke jimamin mutuwar mutane da aka kashe tare da jiran samun bayanai game da waɗanda aka sace.

Wani mazaunin garin ya ce ƴan bindigar sun koma kauyen ne a daren Asabar inda suka ci gaba da yin garkuwa da mutane, ciki har da sarkin ƙauyen da matansa biyu. Wannan ya sa sauran mutane ƴan ƙalilan suka rage a ƙauyen suka tsere.

Har yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta ce uffan ba a kan lamarin.

A ƴan kwanakin nan dai an kai hare-hare kan wasu al'umomi a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya yayin da wasu gungun ƴan fashi da makami kuma suka kori ƙauyuka da dama.

An yi garkuwa da mazauna yankuna da dama domin neman kudin fansa ko kuma a kashe su.

A watan da ya gabata ne aka kashe sojoji shida a wani harin kwanton ɓauna da aka yi musu a lokacin da suka kai ɗauki.