'Ƴan bindiga sun mayar da mu tamkar bayi a garuruwanmu'

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hare-haren 'yan fashin daji na tilastawa daruruwan mutane da muhallansu
Lokacin karatu: Minti 2

Wata gamayyar kungiyoyin farar hula a yankin karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja da ke Najeriya, ta yi tsokaci kan yadda 'yan bindiga ke sanya mutanen da suka yi garkuwa da su aikin bauta a gonaki.

'Yan bindigar suna tilasta wa mutanen, ciki har da matan aure da suka yi garkuwa da su, yin shuka da noma da girbi.

Rahotanni dai sun ce galibin mutanen yankin sun tsere zuwa wasu garuruwa a jihar.

Yanzu haka dai jama'ar garin Allawa da sauran garuruwa da dama na yankin karamar hukumar Shiroron, sun yi kaurar dole zuwa wasu garuruwa, inda suke zaman gudun hijira, saboda kamarin hare-haren 'yan bindiga.

Malam Muhammad Musa, shi ne Na'ibin limamin masallacin Juma'a na garin Allawa, kuma sakataren kungiyar matasan Allawa mai sa ido kan al'amuran da ke aukuwa a yankin da kewayensa, ya shaida wa BBC kamarin matsalar tsaron ta samo asali daga watanni biyar da suka gabata, lokacin da aka janye sojojin da gwamnati ta girke msu a yankin Allawa.

Tun daga lokacin lamarin tsaro ya tabarbare, hakan ya sa mutane tserewa daga garin da a yanzu yake hannun 'yan bindiga.

Malam Musa ya kara da cewa: ''Sauran makoftan garuruwa da suke zaune lafiya sulhu suka yi da barayi ta hanyar biyan harajin wata-wata ko na makonni domin su zauna lafiya a garinsu.

Duk da mutanen garuruwa da dama sun bar yankin, amma 'yan bindigar nan ba su bar su ba.

A yanzu hakan akwai mata da suka sace watanni bakwai da suka gabata, an hade su wurare daban-daban, babu abin da suke yi musu sai bautarwa, aikin gona, da shuka har da gurbi.

Tashin hankalin ya shafi Fandogari da Kagara,'' in ji Malam Musa

Dangane da matakan tsaro da suka kamata hukumomi su samar kuwa, mutanen yankin na Allawa cewa suke, sun ce ba su ga wani tasiri da batun da hukumomi ke yi na cewa za su sauya salon yadda suke yakar 'yan bindigar ba.

Kkuma har yanzu babu matakin da aka dauka na kare rayuka da lafiya da dukiyoyin al'umma.

Mamaye garuruwa da 'yan bindiga ke yi a yankin arewa maso yammacin Najeriya dai, ana gani karin alamomi ne na yadda suke kara karfi da kuma samun iko, duk kuwa da tabbacin da hukumomi kan bayar, cewa suna dauka a kokarin shawo kan wannan matsala ta tsaro.