Yadda ta kasance a taro tsakanin Tinubu da gwamnonin Najeriya

Tinubu da gwamnonin Najeriya

Asalin hoton, ASOROCL

Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya nemi hadin kai tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban kasa baki daya.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a ziyarar da gwamnonin jihohin Najeriya suka kai masa a gidansa da ke Legas ranar Talata, inda suka tattauna halin da kasar take ciki musamman kashe-kashe da matsin tattalin arziki.

Wannan na zuwa yayin da wasu yan bindiga suka kashe mutum sama da 100 a jihar Filato

Gwamnan Zamfara Dr Dauda Lawan Dare wanda na daga cikin gwamnonin da suka gana da shugaba Tinubun ya ce gwamnoni sama da 20 ne suka kai wannan ziyara.

Gwamnan ya ce ''Mun tattauna kan batutuwa da dama da suka hadar da batun hada kai da gwamnatin tarayya da kuma na jihohi, sannan ya yi jaje a kan abun da ya faru a jihar Plateau na kashe-kashen da aka yi.

Ya kara da cewa shugaba Tinubu ya yi alkawarin yin dukkan mai yiwuwa domin samawa yan kasar sauki, ta hanyar samar da wasu tsare tsare na ciyar da jama'a gaba.

''Mu kanmu gwamnoni ya ba mu shawarar bullo da irin wadannan shirye-shirye domin ganin an gudu tare an tsira tare a kan manufarmu ta ciyar da al'umma gaba'' in ji gwamnan.

A halin da ake ciki dai Najeriya na fama da tarin matsaloli iri iri, kama daga kan na tattalin arziki musamman hauhawar farashin kayan masarufi, da kuma matsalolin tsaro.

Masana sun jima suna bayyana cewa dole ne sai gwamnatocin jihohi sun yi aiki tare da gwamnatin tarayya kafin a iya magance matsalolin da kasar ke fama da su.