Matsayar LP da NNPP kan tayin haɗaka daga Atiku

Manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya da suka fafata a zaɓen shugaban ƙasar na 2023, sun bayyana matsayarsu kan kiran da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi don neman su yi maja.
Ana yi wa kiran da Atiku Abubakar ya yi, kallon wani yunƙuri na farautar jam'iyyar LP wadda Peter Obi ya yi wa takara, da kuma ta NNPP da ɗan takararta, Rabi'u Musa kwankwanso.
Ko da yake, ita kanta jam'iyya mai mulki ta APC ba ta yi shiru ba a kan wannan kira na Atiku, domin tana masa kallon barazana da za ta iya kai wa ga tankwaɓe mulkin da ke hannunta, kamar dai yadda aka yi wa PDP a 2015.
Bari mu yi duba ra'ayin kowacce jam'iyya kan wannan batu:
Ba mu fahimci abin da Atiku ke nufi ba - LP

Asalin hoton, X
BBC ta nemi jin ta bakin jam'iyyar LP kuma ta yi ƙoƙarin tattaunawa da ɗaya daga cikin masu magana da yawun ɗan takararta Peter Obi, wato Dr Yunusa Tanko, wanda ya ce ba su fahimci inda Atiku Abubakar babban jagoran adawar ƙasar ya dosa ba.
Ya ce abin ba su fahimta ba shi ne "kiran mu yake mu koma gida ɗaya tilo, ko kuma yana nufin a haɗa ƙarfi da ƙarfe waje guda".
Ya dai yi marhabin da tayin Atiku, na a zo a yi tafiya tare, amma a ganinsa a haɗa ƙarfi da ƙarfe wuri guda zai fi, sannan kuma a "mayar da mulki" kudanci Najeriya matuƙar ana so a ceci ƙasar.
"Duk mai neman haɗa hannu da mu ƙofarmu a buɗe take, amma mu ɗunguma mu koma wata jam'iyya mu marawa wani baya wannan ba zai yiwu ba," a cewar Dr Yunusa.
Idan Kwankwaso za a marawa baya muna ciki - NNPP

Asalin hoton, KWANKWASO
Ita ma NNPP wadda ɗan takararta Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya zo na huɗu a zaɓen da aka yi a 2023, ta ce maja ba za ta taɓa zama laifi ba, musamman idan ɗan takararta za a marawa baya.
Yakubu Shandam wanda shi ne sakataren yaɗa labaran jam'iyyar na ƙasa ya ce, kiran da Atiku ya yi "ihu ne bayan hari".
"Tuni ya kamata a yi wannan kira, amma a yanzu gaskiya an makara. A yanzu ihu ne kawai bayan hari.
"Ya kamata Atiku ya dawo ya marawa Kwankwaso baya, su shiga su yi wannan faɗan tare, ba wai shi Kwankwaso da jam'iyyarmu, mu zo mu marawa Atiku baya ba," in ji Malam Yakubu.
Ya ƙara da cewa matuƙar za a haɗu ne a zaɓi Kwankwaso to ɗari bisa ɗari, za su shiga cikin wannan maja.
Ko a jikinmu an yakushi kakkausa - APC

Asalin hoton, X/@OFFICIALABAT
Ko shakka babu, rabuwar kan da aka samu tsakanin jam'iyyun adawa a zaɓen 2023, ya taka rawar gani wajen samun nasarar jam'iyyar APC mai mulki.
Masana na ganin da biyu daga cikin jam'iyyun adawar uku da suka yi takara sun haɗa ƙarfi wuri guda, da yanzu ba wannan batu ake yi ba.
Don haka ne ma, suke cewa wannan ja-in-jar ƙin amincewar jam'iyyun ga kiran na Atiku, abin farin ciki ne ga APC.
Malam Bala Ibrahim, daraktan yaɗa labaran jam'iyyar APC ya ce wannan kira na Atiku ba zai firgita su ba.
"Taron da suka yi na ƙananan jam'iyyu ne kuma aka yi rashin sa a suka ƙi amincewa da buƙatar. Don haka ko a jikinmu, wannan shiri da suke y", in ji Bala Ibrahim.
Ya ce jam'iyyarsu ta APC kullum ƙara haskakawa take yi, abin da yake sake ba ta farin jini tsakanin 'yan ƙasar.
An tambaye shi kan cewa maja ce ta kafa APC har ta kai zo inda take sai ya ce, "ko mai zai iya faruwa babu mai jayayya, amma "abin da wuya ga 'yan adawar na yanzu".
Me Atiku ke nema a taƙaice?

Asalin hoton, ATIKU ABUBAKAR/FACEBOOK
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Atiku Abukabar wanda shi ne jagoran adawa a Najeriya, ya yi kira ga jam'iyyun adawa a ƙasar su haɗa ƙarfi da ƙarfe, don tsamo dimokraɗiyyar ƙasar daga komawa zuwa mai bin tsarin jam'iyya ɗaya.
Ya kuma ja hankali a kan buƙatar yin hattara game da tsunduma Najeriya, cikin tsarin mulkin kama-karya na jam'iyya ɗaya.
Wata sanarwa da Paul Ibe, mashawarcin ɗan takarar shugaban ƙasar a zaɓen watan Fabrairun 2023 kan harkar yada labarai ya fitar ranar Talata, ta ce Atiku ya yi kiran ne lokacin da ya karɓi bakuncin shugabannin majalisar tuntuɓa tsakanin jam'iyyu ta Najeriya (IPAC).
A cewarsa, aikin kare mutuncin dimokraɗiyya, ba kawai na mutum ɗaya ba ne a ƙasar.
Atiku ya ƙara da cewa “Dukkanmu mun ga yadda jam'iyyar APC ke daɗa mayar da Najeriya zuwa ƙasar mulkin kama-karya mai jam'iyya ɗaya.
Idan ba mu zo mun haɗu don kalubalantar abin da jam'iyya mai mulki ke ƙoƙarin kafawa ba, dimokraɗiyyarmu za ta sha wahala, kuma sakamakon haka zai shafi hatta zuri'ar da ba a ma haifa ba”.
Ra'ayoyin masana
Masana harkokin siyasa a Najeriya tuni suka fara tofa albarkacin bakinsu kan kalaman na Atiku Abubakar.
Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero Kano na da ra'ayin cewa, samun haɗakar jam'iyyu masu ƙarfi, ka iya zama wani tagomashi ga siyasar Najeriya.
To amma game da kiran Atiku, Farfesa Fagge ya ce, "ya so ya ɗan makara saboda tun tuni kiran da ake sha'awa a ga 'yan siyasar sun fito sun yi a karan kansu, amma a lokacin da aka so hakan, ba ta samu ba.
"Son zuciya da buƙata irin ta raɗin kansu, ta hana manyan 'yan siyasa da jam'iyyun adawa, su zo su haɗa kansu waje ɗaya su yi hakan".











